Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 9/1 pp. 3-5
  • Menene Amfanin Addini?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Menene Amfanin Addini?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Ya Sa Mutane da Yawa Suka Ƙi Addini
  • Ana Amfani da Addini Don Ayyukan Mugunta
  • “Da Wane Nufi?”
  • Ta Yaya Zan Gane Addini na Gaskiya?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Addinan Karya Suke Bata Sunan Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Allah Ya Yarda da Dukan Addinai Ne?
    Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 9/1 pp. 3-5

Menene Amfanin Addini?

“ZAN iya zama mutumin kirki ba tare da na zama mai addini ba!” Mutane da yawa suna jin hakan. Mutane da yawa masu yin gaskiya, da juyayi ba sa son addini. Alal misali, mutane kalilan ne a Yammacin Turai suke zuwa coci a kai a kai, ko da yawanci suna cewa sun gaskata da Allah.a Ko a Latin Amirka ma, kashi 15 zuwa 20 ne kawai na ’yan Katolika suke zuwa coci a kai a kai.

Kamar mutane da yawa, wataƙila kana jin cewa addini ba ya taimakon mutum ya yi rayuwa mai kyau. Mai yiwuwa, ka san cewa shekaru da yawa da suka shige a zamanin kakanninka, yawancin mutane suna bin addini fiye da yadda suke yi a yau. Me ya sa mutane a ko’ina ba sa yawan bin addini kuma? Mutum zai iya zama na kirki ba tare da bin addini ba? Da akwai addini da zai amfane ka ne?

Abin da Ya Sa Mutane da Yawa Suka Ƙi Addini

Cikin ƙarnuka da yawa, yawancin mutane a Kiristendom sun gaskata cewa Allah na bukatar a yi masa biyayya. Suna zuwa coci su sami tagomashin Allah ko ta wurin bukukuwa na firist ko kuma ta ja-gorar shugaban addini. Hakika, mutane da yawa suna sane da riya da ake yi a cikin addini. A ko’ina, an san cewa addinai suna saka hannu a yaƙi da kuma mugun hali na wasu limamai. Amma, yawancin mutane suna jin cewa addini yana da kyau. Wasu suna son gaibi, al’ada, da kuma waƙoƙin addinai; wasu suna ganin amfanin koyarwar nan da ba ta cikin Nassosi wadda ta ce za a ƙona mutane a wutar jahannama. Daga baya, abubuwan da suke faruwa sun canja ra’ayin mutane game da addini.

Koyarwar rai na bayyanau ta zama ruwan dare. An rinjayi wasu mutane cewa ba Allah ba ne ya halicci abubuwa. Yawancin addinai sun kasa ba da tabbaci cewa Allah ne Tushen rai. (Zabura 36:9) Ban da haka, da aka sami ci gaba a fasaha, hanyoyin magani, sufuri, da sadarwa, wannan ya sa mutane sun ji cewa kimiyya za ta magance kowace irin matsala. Ƙari ga haka, aka ji cewa masanan kimiyyar jama’a da halin mutane suna ba da ja-gorar da ta fi na addini kyau. Addinai kuma sun kasa nuna cewa rayuwa bisa dokar Allah ita ce ta fi kyau.—Yaƙub 1:25.

Saboda haka, addinai da yawa sun canja koyarwarsu. Firistoci da malamai suka daina koyar da cewa Allah yana bukatar biyayya. Maimakon haka, suna koyar da cewa kowane mutum ne zai yanke wa kansa abin da ke nagari da mugunta. Don su sami farin jini, wasu shugabannan addinai suna da’awar cewa Allah zai amince da kai ko yaya kake rayuwarka. Irin wannan koyarwa ya tuna mana abin da Littafi Mai Tsarki ya annabta: “Kwanaki za su zo inda ba za su daure da koyarwa mai-lafiya ba; amma bisa ga ƙaiƙayin kunnuwa za su tattara wa kansu masu-koyarwa bisa ga sha’awoyinsu.”—2 Timothawus 4:3.

Maimakon ta jawo mutane, irin wannan koyarwa tana korarsu. Suna mamaki: ‘Idan addinai suna shakkar ikon Allah na halittar abubuwa da kuma hikimarsa na kafa dokoki, ta yaya zuwa coci zai amfane mu? Me ya sa zan yi ƙoƙari na koya wa yarana addini?’ Mutane da suke ƙoƙari su yi rayuwa mai kyau suka soma ganin cewa addini ba shi da amfani. Sun daina zuwa coci, kuma addini ba shi da muhimmanci a garesu. Me ya sa abin da ya kamata ya kasance da amfani ya zama marar amfani? Littafi Mai Tsarki ya ba da bayani mai tabbatarwa.

Ana Amfani da Addini Don Ayyukan Mugunta

Manzo Bulus ya gargaɗi Kiristoci na farko cewa wasu za su yi amfani da Kiristanci don mugunta. Ya ce: “Kerketai masu-zafin hali za su shiga wurinku, ba za su kewaye ma garke ba; daga cikin tsakiyarku kuma mutane za su tashi, suna faɗin karkatattun zantattuka, domin su janye masu-bi bayansu.” (Ayukan Manzanni 20:29, 30) Wani da ya faɗi “karkatattun zantattuka,” shi ne Augustine, ɗan tauhidi na Cocin Katolika. Yesu ya koya wa mabiyansa su huɗubantar da mutane ta wajen mahawwara bisa Nassosi. Amma, Augustine ya canja ma’anar kalmomin Yesu da ke rubuce a Luka 14:23, wadda ta ce, “Ka i masu su shigo,” ya ce kalmomin suna nufin a riƙa tilasta wa mutane su soma bin addini. (Matta 28:19, 20; Ayukan Manzanni 28:23, 24) Augustine ya yi amfani da addini don ya shugabanci mutane.

Shaiɗan, wanda ɗan tawaye ne, shi ne yake zuga lalaci na addini. Ya zuga mutane masu addini a ƙarni na farko su yi ƙoƙari su ɓata ikilisiyoyin Kirista. Littafi Mai Tsarki ya ce game da waɗannan mutanen: “Irin waɗannan masu-ƙaryan manzanci ne, ma’aikata masu-ha’inci, suna mayasda kansu manzannin Kristi. Wannan kuwa ba abin al’ajibi ba ne; gama har Shaiɗan da kansa ya kan mayarda kansa kamar mala’ika na haske. Ba wani abu ne fa masu-hidimansa kuma su mayarda kansu masu-hidiman adalci.”—2 Korinthiyawa 11:13-15.

Har ila Shaiɗan yana amfani da addinan da suke da’awa cewa su Kiristoci ne, masu ɗabi’a mai kyau, kuma suna wayar da kan mutane domin su yi rayuwa bisa mizanan Shaiɗan maimakon na Allah. (Luka 4:5-7) Wataƙila ka lura cewa limamai da yawa a yau suna amfani da addini domin su ɗaukaka kansu da manyan laƙabi kuma su sami kuɗi daga garkensu. Gwamnatoci kuma suna amfani da addini su rinjayi talakawansu su ba da ransu a yaƙi.

Iblis yana amfani da addini sosai fiye da yadda mutane suke tsammani. Kana iya tunanin cewa Shaiɗan da mutane ne kalilan masu tsattsauran ra’ayi na addini. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce, “wanda ana ce da shi Iblis da Shaiɗan, [yana] ruɗin dukan duniya.” Littafi Mai Tsarki ya daɗa cewa: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9; 1 Yohanna 5:19) Ta yaya Allah yake ji game da shugabannai da suke amfani da addini su jawo mutane wajensu?

“Da Wane Nufi?”

Idan kana mamaki game da halayen wasu cocin Kiristendom, ka san cewa Allah Maɗaukaki yana baƙin ciki sosai da su. Kiristendom suna da’awa cewa sun yi alkawari da Allah; Isra’ila ta dā ma ta yi irin wannan da’awar. Dukansu sun yi rashin aminci. Yadda Jehobah ya hukunta Isra’ila ya nuna cewa zai hukunta Kiristendom a yau. Jehobah ya ce: “Ba su kasa kunne ga maganata ba; don shari’ata kuwa, sun ƙi ta. Da wane nufi a ke kawo mani lubban daga Sheba?. . . hadayunku na ƙonawa ba abin karɓa ba ne.” (Irmiya 6:19, 20) Allah ba ya karɓan ayyukan bauta da masu riya suke yi. Ba ya son bukukuwansu da addu’o’insu. Ya gaya wa Isra’ila: “Ayanannun idodinku raina yana ƙinsu: sun zama kaya gareni; na gaji da ɗaukansu. Sa’anda ku ke buɗen hannuwanku, zan ɓoye maku idanuna: i, sa’anda ku ke yi mani yawan addu’o’i, ba ni ji ba.”—Ishaya 1:14, 15.

Jehobah yana son idodin da coci suke yi ne, da suka samo asalinsu wajen ɗaukaka allolin ƙarya? Yana jin addu’o’in limamai da suke ɓata koyarwar Kristi ne? Shin Allah yana amincewa da addinin da ya ƙi dokarsa ne? Ka tabbata yana aikatawa ga idodi na addini a yau yadda ya aikata ga hadayun Isra’ila ta dā, ya ce game da su: “Da wane nufi?”

Duk da haka, Jehobah yana amincewa da bautar da sahihan mutane suke yi cikin gaskiya. Allah yana farin ciki sa’ad da mutane suka furta godiyarsu ga dukan abin da yake musu. (Malachi 3:16, 17) Za ka zama mutumin kirki ne idan ba ka bauta wa Allah? Za a ce mutumin da ba ya yi wa iyayensa kome mutum kirki ne? Za a kira mutumin da ba ya yi wa Allah kome mutum kirki? Hakika, ya kamata mu so Allah na gaskiya, da yake shi ne mafarin rai. A talifi na gaba, za mu ga yadda bauta ta gaskiya take ɗaukaka Allah da kuma yadda take amfanar mu.

[Hasiya]

a “A shekarun 1960 ne al’adar addini ta soma faɗiwa a ƙasashe da yawa.”—The Decline of Christendom in Western Europe, 1750-2000.)

[Hoto a shafi na 4]

Coci sun ba da tabbacin cewa Allah ne ya halicci dukan abubuwa?

[Hoto a shafi na 5]

Ya kamata mai bauta wa Allah ya kasance cikin wannan yanayin?

[Hoto a shafi na 5]

Yaya Allah yake ɗaukan irin wannan bikin?

[Inda aka Dauko]

AP Photo/Georgy Abdaladze

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba