Jehobah Yana “Bayana Ƙarshe Tun Daga Mafarin”
“Mai-bayana ƙarshe tun daga mafarin, tun zamanin dā kuma al’amuran da ba a rigaya a aika ba tukuna.”—ISHAYA 46:10.
1, 2. Menene abin mamaki game da abubuwa da suka faru a lokacin cin Babila, kuma menene wannan gaskiya ya nuna game da Jehobah?
CIKIN duhun dare, sojoji abokan gaba suka yi sanɗa cikin kogin Yufiretis zuwa in da suke fako, wato, babban birnin Babila. Sa’ad da suka yi kusa da ƙofar garin, suka ga abin mamaki. An bar manyan ƙofofi biyu na garin buɗe! Suka fita daga cikin kogi, suka hau suka shige cikin birnin. A take suka kama birnin. Shugabansu Cyrus nan take ya fara iko da ƙasar da ya ci a yaƙi daga baya kuma ya kafa doka ya saki Isra’ilawa daga bauta. Dubbai suka koma ƙasarsu domin su kafa bauta ta Jehobah a Urushalima.—2 Labarbaru 36:22, 23; Ezra 1:1-4.
2 Waɗannan abubuwa da suka faru a shekara ta 539 zuwa 537 K.Z. a yau abu ne da ’yan tarihi suka tabbata. Abin mamaki ma shi ne cewa an san wannan abin zai faru wajen shekaru 200 kafin ya faru. Jehobah ya ruhi annabinsa Ishaya ya kwatanta faɗuwar Babila shekaru masu yawa kafin ya faru. (Ishaya 44:24–45:7) Allah ya bayyana yanayin yadda za a ci Babila da kuma sunan shugaban da zai ci Babila.a Da yake magana da Isra’ilawa, waɗanda su ne shaidunsa a dā, Jehobah ya ce: “Ku tuna da al’amura na dā: gama ni ne Allah, babu wanina; ni Allah ne, kuma babu wani mai-kama da ni; mai-bayana ƙarshe tun daga mafarin, tun zamanin dā kuma al’amuran da ba a rigaya a aika ba tukuna.” (Ishaya 46:9, 10a) Jehobah hakika Allah ne da ya san abin da zai faru a nan gaba.
3. Amsoshin waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?
3 Yaya zurfin yadda Allah ya san abin da zai faru a nan gaba? Jehobah ya san abin da kowanenmu zai yi ne a nan gaba? Shin ya riga ya ƙaddara rayuwarmu ce? Za mu bincika amsa da Littafi Mai Tsarki ya bayar ga waɗannan tambayoyi da kuma wasu da suka dangance su a wannan da kuma talifi na gaba.
Jehobah, Allah na Annabci Ne
4. Wanene ne Tushen annabce-annabcen da suke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki?
4 Da yake ya san abin da zai faru a nan gaba, Jehobah ya huri bayinsa a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki su rubuta annabce-annabce masu yawa, waɗanda suka sa mu fahimci abin da Allah yake da niyyar yi kafin ya faru. “Ga shi, al’amura na dā sun tabbata, sabobin al’amura kuwa ni ke bayanawa,” Jehobah ya sanar. “Tun ba su ɓullo ba in ba ku labarinsu.” (Ishaya 42:9) Lallai mutanen Allah suna da gata!
5. Wane hakki ne yake ga sanin abin da Jehobah zai yi a nan gaba?
5 Annabi Amos ya tabbatar mana cewa: “Ubangiji Yahweh ba za ya yi kome ba, sai shi bayyana asirinsa ga bayinsa annabawa.” Irin wannan sanin abin da zai faru nan gaba yana kawo hakki. Ka lura da kwatanci mai kyau da Amos ya yi a gaba: “Zaki ya yi ruri, wanene ba za ya ji tsoro ba?” Kamar yadda idan zaki ya yi ruri, yana sa mutum da dabba da suke wurin su motsa, haka ma annabawa kamar su Amos suke sanar da maganar Jehobah. “Ubangiji ya rigaya ya faɗi, wa za ya rasa yin annabci?”—Amos 3:7, 8.
“Maganar” Jehobah Za Ta “Cika”
6. A wace hanya ce “ƙudurin” Jehobah ya cika game da ƙarshen Babila?
6 Ta bakin annabinsa Ishaya, Jehobah ya ce: “Ƙudurina za ya tabbata, zan kuma cika dukan nufina.” (Ishaya 46:10b) “Ƙudurin” Allah, wato, abin da ya yi niyyar yi game da Babila, ya haɗa da kiran Cyrus daga Fasiya ya ci Babila a yaƙi kuma ya kawo ƙarshenta. Jehobah ya bayyana wannan ƙuduri da daɗewa. Kamar yadda muka riga muka lura, haka ya tabbata a shekara ta 539 K.Z.
7. Me ya sa za mu tabbata cewa “maganar” Jehobah a koyaushe za ta yi nasara?
7 Kusan shekaru ɗari huɗu kafin Cyrus ya ci Babila a yaƙi, Sarki Yehoshafat na Yahuda ya fuskanci sojojin haɗin gambiza na Amman da na Mowab. Ya yi addu’a da gaba gaɗi: “Ya Ubangiji, Allah na ubaninmu, ba kai ne Allah cikin sama ba? Ba kai ne mai-mulkin dukan mulkoki na al’ummai? a cikin hannunka kuma iko da ƙarfi su ke, har ba mai-tsaya maka.” (2 Labarbaru 20:6) Ishaya ya furta irin wannan dogarar sa’ad da ya ce: “Ubangiji mai-runduna ya ƙaddara, wa za ya kawar fa? hannunsa a miƙe ya ke, wa za ya juyadda shi?” (Ishaya 14:27) Bayan ya yi hauka aka mai da masa hankalinsa, Sarki Nebuchadnezzar na Babila ya ƙasƙantar da kansa ya ce: “Ba kuwa mai-tsayasda hannuwansa [Allah], ba kuwa mai-ce masa, Mi ka ke yi?” (Daniel 4:35) Hakika, Jehobah ya tabbatar wa mutanensa: “Maganata, . . .ba za ta koma wurina wofi ba, amma za ta cika abin da na nufa, za ta yi albarka kuma a cikin saƙona.” (Ishaya 55:11) Mun tabbata cewa maganar Jehobah tana tabbata a kullum. Ƙudurin Allah ba shakka zai cika.
“Madawwamin Nufi” na Allah
8. Menene “madawwamin nufi” na Allah?
8 A wasiƙarsa ga Kiristocin Afisawa, manzo Bulus ya ce Allah yana da “madawwamin nufi.” (Afisawa 3:11) Wannan ba wani tsarin aiki ba ne, kamar a ce dole ne Allah ya zana yadda yake so ya yi aiki. Maimakon haka, yana da nasaba ne da ƙudurin Jehobah ya cika abin da ya yi niyya tun da farko ga ’yan adam da kuma duniya. (Farawa 1:28) Domin a taimake mu mu fahimci tabbacin nufin Allah, yi la’akari da annabci na farko da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki.
9. Ta yaya Farawa 3:15 ta shafi nufin Allah?
9 Alkawarin da yake Farawa 3:15 ya nuna cewa ba tare da ɓata lokaci ba bayan Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi, Jehobah ya tabbatar cewa mata ta alama za ta haifi zuriya ko kuma ɗa. Jehobah kuma ya san sakamakon gabā da zai kasance tsakanin matar da kuma Shaiɗan da kuma tsakanin zuriyarsu. Ko da yake Jehobah zai ƙyale a ƙuje duddugen zuriyar matar, a lokacin da Allah ya zaɓa, Zuriyar zai ƙuje kan macijin ko kuma Shaiɗan Iblis. Amma kafin nan, nufin Jehobah ya ci gaba cikin zuriyar da ya zaɓa har zuwa kan Yesu da ya kasance Almasihu da aka yi alkawarinsa.—Luka 3:15, 23-38; Galatiyawa 4:4.
Abin da Jehobah Ya Ƙaddara
10. Shin Jehobah ya riga ya ƙaddara ne tun daga farko cewa Adamu da Hauwa’u za su yi zunubi? Ka ba da bayani.
10 Da yake magana game da matsayin Yesu a nufin Allah, manzo Bitrus ya rubuta: “[Yesu] wanda aka rigaya saninsa lallai gaban kafuwar duniya, amma a ƙarshen zamanu ya bayanu sabili da ku.” (1 Bitrus 1:20) Shin Jehobah ya riga ya sani ne tun daga fari cewa Adamu da Hauwa’u za su yi zunubi kuma za a bukaci hadaya da Yesu Kristi ya bayar? A’a. Kalmar nan “kafuwa” fassara ce daga kalmar Hellenanci da take nufin “zubar da iri.” (1 Bitrus 1:20) An “zubar da iri,” ne ko kuma an sami ciki ne kafin Adamu da Hauwa’u su yi zunubi? A’a. Bayan sun yi rashin biyayya ne Adamu da Hauwa’u suka haifi ’ya’ya. (Farawa 4:1) Saboda haka, bayan sun yi tawaye amma kafin Adamu da Hauwa’u su haifi ’ya’ya ne, Jehobah ya ƙaddara bayyanar “zuriya.” Mutuwar Yesu da kuma tashinsa daga matattu sun yi tanadin tsarin ƙauna na fansa, inda zunubi da muka gada da kuma dukan ƙoƙarin Shaiɗan za a wofintar da su.—Matta 20:28; Ibraniyawa 2:14; 1 Yohanna 3:8.
11. Wane aukuwa ne Jehobah ya ƙaddara wajen cika nufinsa?
11 Allah kuma ya ƙaddara wani abin da zai faru wajen cika nufinsa. Wannan ya bayyana daga abin da Bulus ya rubuta zuwa ga Afisawa, cewa Allah zai “tattara dukan abu cikin Kristi, abubuwan da ke cikin sammai, da abubuwan da ke bisa duniya.” Game da “abubuwan da ke cikin sammai,” wato, waɗanda aka zaɓa su yi sarauta da Kristi, Bulus ya yi bayani: Mu “ƙadararru bisa ga nufin wannan da ke aikata dukan abu bisa ga shawarar nufinsa.” (Afisawa 1:10, 11) Hakika, Jehobah ya ƙaddara tun dā iyakacin adadin mutanen da za su zama zuriyar mace ta Allah kuma su yi aiki tare da Kristi wajen ba da amfanin fansa. (Romawa 8:28-30) Manzo Bulus ya kira wannan “tsattsarkar al’umma.” (1 Bitrus 2:9) An ba wa manzo Yohanna gatar sanin adadin waɗanda za su yi sarauta tare da Kristi a wahayi; su 144,000. (Ru’ya ta Yohanna 7:4-8; 14:1, 3) Suna tallafa wa Sarki Kristi, suna hidima “domin yabon ɗaukakarsa [Allah]” ne.—Afisawa 1:12-14.
12. Ta yaya muka sani cewa mutane 144,000 ba a ƙaddara wa kowannensu ba?
12 Ƙaddarar mutane 144,000 ba ya nufin cewa an riga an ƙaddara cewa wasu mutane za su bauta wa Allah cikin aminci a wannan hanya. Hakika, gargaɗi da ke rubuce cikin Nassosin Kiristoci na Hellenanci an rubuta shi ne musamman domin a yi wa shafaffu ja-gora da kuma ƙarfafa su domin su riƙe amincinsu kuma su tabbatar da kansu sun cancanci wannan kira na samaniya. (Filibbiyawa 2:12; 2 Tassalunikawa 1:5, 11; 2 Bitrus 1:10, 11) Jehobah ya sani tun dā cewa mutane 144,000 za su ƙware su yi hidima domin nufinsa. Ko su wa waɗannan za su kasance, wannan ya dangana ne ga yadda waɗanda aka kira suka yi rayuwarsu, zaɓi ne da kowane mutum dole ne ya yi da kansa.—Matta 24:13.
Abin da Jehobah Ya Sani Kafin Ya Faru
13, 14. Da menene yadda Jehobah yake amfani da sanin abin da zai faru a nan gaba dole ya jitu, kuma me ya sa?
13 Tun da Jehobah Allah ne na annabci da ƙuduri, ta yaya yake amfani da wannan sanin abu kafin ya faru? Da farko, mun tabbata cewa dukan hanyoyin Allah masu gaskiya ne, masu adalci, masu ƙauna. Sa’ad da yake rubutu zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa na ƙarni na farko A.Z., manzo Bulus ya tabbatar da cewa rantsuwa da kuma alkawari na Allah “abu biyu da ba su sākuwa, inda ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya.” (Ibraniyawa 6:17, 18) A wasiƙarsa zuwa ga Titus, Bulus ya kuma furta wannan, sa’ad da ya rubuta cewa Allah “ba shi iya yin ƙarya.”—Titus 1:2.
14 Bugu da ƙari, ko da yake Jehobah yana da iko marar iyaka, bai taɓa aikata rashin adalci ba. Musa ya kwatanta Jehobah yana cewa “shi Allah mai-aminci ne, marar-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 32:4) Dukan abin da Jehobah ya yi yana jituwa da mutuntakarsa mai ban sha’awa. Ayyukansa suna jituwa da halayensa na musamman, ƙauna, hikima, shari’a, da kuma iko.
15, 16. Wane zaɓi ne Jehobah ya bai wa Adamu a lambun Adnin?
15 Ka yi la’akari da yadda dukan wannan ya shafi abin da ya faru a lambun Adnin. Da yake shi Uba ne mai ƙauna, Jehobah ya yi tanadin dukan abin da mutane suke bukata. Ya ba wa Adamu tunani, da kuma yadda zai yanke shawara. Ba kamar dabbobi ba da ilhami yake musu ja-gora, Adamu yana da zarafin ya zaɓi abin da yake so. Sakamakon haka shi ne cewa Allah ya duba ya gani daga kan kursiyinsa ya ga dukan abu da ya yi, “yana da kyau ƙwarai.”—Farawa 1:26-31; 2 Bitrus 2:12.
16 Sa’ad da Jehobah ya zaɓi ya ba wa Adamu doka kada ya ci daga “itace na sanin nagarta da mugunta,” ya ba da cikakken bayani domin Adamu ya yanke shawarar abin da yake so ya yi. Ya ce Adamu ya ci daga “kowane itacen gona a sāke” sai ɗaya kawai aka yi masa gargaɗi game da haɗarin cin ’ya’yan itacen da aka hana. (Farawa 2:16, 17) Ya gaya wa Adamu sakamakon abin da zai yi. Menene Adamu zai yi?
17. Me ya sa za mu ce yadda Jehobah yake amfani da sanin abin da zai faru a nan gaba, yana zaɓe ne?
17 A bayane yake cewa Jehobah ya zaɓi kada ya ga abin da Adamu da Hauwa’u za su yi, ko da yake yana iya gan kome kafin ya faru. Saboda haka tambayar ba ta ko Jehobah yana iya ganin abin da zai faru a nan gaba ba ne, amma ko zai zaɓi ya yi haka. Ƙari ga haka, muna iya tunani cewa Jehobah, tun da yake Allah ne mai ƙauna, cikin saninsa ba zai ƙaddara tawaye ba, da dukan matsalolinsa na baƙin ciki. (Matta 7:11; 1 Yohanna 4:8) Saboda haka, idan ya shafi yadda Jehobah yake amfani da iyawarsa na sanin abin da zai faru a nan gaba, yana zaɓe ne.
18. Me ya sa yadda Jehobah yake zaɓan yadda zai yi amfani da iyawarsa ba ya nufin kasawa ce a gare shi?
18 Shin yadda Jehobah yake amfani da iyawarsa na sanin abin da zai faru a nan gaba yana nufi ne cewa ba shi da cikakken iko? A’a. Musa ya kwatanta cewa “Fa ne shi, aikinsa cikakke ne.” Ba shi da alhakin zunubin mutane ba. Dukan wahala da muke sha a yau ya fara ne daga rashin biyayya. Manzo Bulus ya yi tunanin cewa “zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da shi ke duka sun yi zunubi.”—Kubawar Shari’a 32:4 5; Romawa 5:12; Irmiya 10:23.
19. Waɗanne tambayoyi ne za a amsa a talifi na gaba?
19 Har zuwa yanzu a tattaunawarmu mun ga cewa babu rashin adalci wurin Jehobah. (Zabura 33:5) Maimakon haka, iyawar Jehobah, halayensa na ɗabi’a, da kuma mizanansa duka sun jitu da nufinsa. (Romawa 8:28) Da yake Allah ne na annabci, Jehobah “mai-bayana ƙarshe tun daga mafarin, tun zamanin dā kuma al’amuran da ba a rigaya a aika ba tukuna.” (Ishaya 46:9, 10) Mun kuma ga cewa yana zaɓe wajen amfani da iyawarsa ya san abin da zai faru a nan gaba. Amma kuma, ta yaya wannan ya shafe mu? Ta yaya za mu tabbata cewa shawararmu ta jitu da nufin Allah na ƙauna? Kuma wace albarka yin haka zai kawo mana? Talifi na gaba zai amsa waɗannan tambayoyi.
[Hasiya]
a Ka dubi mujallar nan Littafi Don Dukan mutane, shafi na 28, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Za Ka Iya Yin Bayani?
• Waɗanne misalai ne na dā suka tabbatar da cewa “maganar” Allah tana “tabbata”?
• Menene Jehobah ya ƙaddara game da ‘madawwamin nufinsa’?
• A wace hanya ce Jehobah yake amfani da iyawarsa na sanin abin da zai faru a nan gaba?
[Hoto a shafi na 20]
Yehoshafat ya dogara ga Jehobah
[Hoto a shafi na 21]
Allah ya annabta mutuwa da kuma tashin Yesu daga matattu
[Hoto a shafi na 22]
Shin Jehobah ya ƙaddara ne abin da Adamu da Hauwa’u za su yi?