“Ka Yi Mana Ƙarin Bayani!”
ANEZLOBNAYA, a ƙasar Rasha, wasu ɗaliban adabi a makarantar sakandare suna nazarin littattafan wani marubuci na Rasha, Mikhail Bulgakov. A cikin littattafan, akwai wanda ya kwatanta Yesu Kristi a hanya marar kyau, amma ya kwatanta Shaiɗan a matsayin jarumi. Bayan tattaunawa a ajin, malamar ta ba ’yan ajin jarabawa daga cikin littafin. Amma, ɗaya daga cikin ɗaliban, wani Mashaidin Jehobah ɗan shekara 16, mai suna Andrey, cikin tarbiyya ya ce ba zai yi jarabawar ba domin lamirinsa bai bar shi ya karanta irin wannan littafin ba. Amma ya nemi izini ya rubuta labari game da yadda ya ɗauki Yesu Kristi. Malamar ta yarda.
A cikin labarinsa, Andrey ya ce ko da yake yana daraja ra’ayin wasu, a ganinsa hanya mafi kyau na koya game da Yesu ita ce ta karanta ɗaya daga cikin Linjilar huɗu. Ta haka, “za ku koyi game da rayuwa da kuma koyarwar Yesu daga waɗanda suka shaida aukuwar kuma suka rubutata.” Andrey ya daɗa: “Wani abin damuwa shi ne yadda aka kwatanta Shaiɗan. Wasu suna iya jin daɗin karanta littafin da aka kwatanta Shaiɗan jarumi amma ni ba zan iya ba.” Ya bayyana cewa Shaiɗan mugun ruhu ne mai iko wanda ya bijire daga Allah, kuma shi ne ya jawo mugunta, azaba, da kuma wahala ga mutane. Andrey ya kammala labarinsa: “Ban yarda ba cewa karanta wannan littafin zai taimake ni. Hakika, ba ni da wata matsala da Bulgakov. Amma, na gwammace in karanta Littafi Mai Tsarki don in san tarihin Yesu Kristi.”
Malamar Andrey ta yi farin ciki sosai da labarin da ya rubuta har ta ce ya shirya labari game da Yesu Kristi da zai gabatar wa ’yan ajin. Andrey ya yarda. A darasinsu na gaba, Andrey ya karanta rahotonsa a gaban duka ’yan ajin. Ya bayyana dalilin da ya sa ya yarda cewa Yesu ne mutumi mafi muhimmanci da ya taɓa rayuwa. Bayan haka, ya karanta sura guda game da mutuwar Yesu daga littafin Matta na Littafi Mai Tsarki. Tun da yake lokacin da aka ba shi ya kawo ƙarshe, Andrey yana son ya kammala bayaninsa, amma ’yan ajinsa suka umurce shi: “Ka yi mana ƙarin bayani! Menene ya faru bayan haka?” Sai ya ci gaba da karanta labarin Matta game da tashin Yesu daga matattu.
Sa’ad da Andrey ya gama, ’yan ajinsa suka yi masa tambayoyi masu yawa game da Yesu da kuma Jehobah. “Na yi addu’a ga Jehobah ya ba ni hikima, kuma ya amsa addu’a ta,” in ji Andrey. “Na amsa duka tambayoyinsu!” Bayan an tashi makaranta, Andrey ya ba malamarsa kofi guda na littafin nan The Greatest Man Who Ever Lived,a kuma ta karɓa da farin ciki. Andrey ya ce: “Ta ba ni babbar maki don rahoto na kuma ta yaba mini domin abin da na gaskata da shi wanda ban ji kunyarsa ba. Kuma ta gaya mini cewa ta yarda da wasu cikin abubuwan da na gaskata da su.”
Andrey ya yi farin cikin bin lamirinsa da Littafi Mai Tsarki ya koyar ta wajen ƙin karanta littafin da ya raina Jehobah da kuma Ɗansa, Yesu Kristi. Irin wannan ƙudurin ya kāre shi daga ra’ayoyin da ba na nassi ba, kuma ya ba shi dama mai kyau na gaya wa wasu gaskiya na Littafi Mai Tsarki.
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.