“Ku Natsu”
“Marar-wayo yana gaskata kowacce magana: amma mai-hankali ya kan lura da al’amuransa da kyau.”—MISALAI 14:15.
1, 2. (a) Menene abin da Lutu ya shaida a Saduma ya koya mana? (b) Menene kalmar nan “ku natsu” take nufi?
SA’AD da Ibrahim ya ce wa Lutu ya fara zaɓan gefen da ya ke so a ƙasar, Lutu ya zaɓi yanki mai dausayi wadda “kamar gonar Ubangiji ce.” Kamar wannan shi ne wuri mafi kyau da Lutu zai zauna da iyalinsa, domin “ya zaɓa ma kansa dukan Filin Urdun” kuma ya kafa zango kusa da Saduma. Amma, abubuwa na zahiri sun ruɗe shi, domin waɗanda suke zaune kusa da shi “mutanen Sodom miyagu ne, masu-zunubi ne kuma ƙwarai a gaban Ubangiji.” (Farawa 13:7-13) Yayin da abubuwa suka ci gaba da faruwa, Lutu da iyalinsa sun yi asara ƙwarai. Daga baya, shi da ’ya’yansa mata suka koma da zama cikin kogo. (Farawa 19:17, 23-26, 30) Abin da yake gani yana da kyau a zahiri, sai bai kasance haka ba.
2 Labarin abin da ya sami Lutu ya koya wa bayin Allah darassi a yau. Sa’ad da ya kasance za mu yanke shawara, dole ne mu kula da haɗarurruka da ke akwai kuma kada mu yarda ganin farko ya ruɗe mu. Ya dace da Kalmar Allah ta umurce mu: “ku natsu.” (1 Bitrus 1:13) Kalmar Helenanci da aka fassara “ku natsu” na nufin “ka mai da hankali.” In ji wani manazarcin Littafi Mai Tsarki R.C.H. Lenski, ya ce mai da hankali na nufin “natsuwa, da kuma yanayin zuciya da ta kahu wadda take gwada da kuma kimanta abubuwa yadda ya kamata, wanda haka ke sa mu tsai da shawara mai kyau.” Bari mu tattauna wasu yanayi da ya kamata mu nuna natsuwa.
Bincika Irin Kasuwanci
3. Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali sa’ad da wani ya zo wurinmu da wani zarafi na kasuwanci?
3 A ce wani mutum mai martaba ya ba ka damar yin aiki, wataƙila ɗan’uwa ne mai bauta wa Jehobah. Yana da tabbacin nasarar da za ka iya samu kuma ya ƙarfafa ka ka saka hannu da wuri domin ka da a barka a baya. Kana iya soma tunanin cewa wannan damar za ta kawo wa kai da iyalinka rayuwa mai daɗi, wataƙila kuma ka soma tunanin cewa hakan zai ba ka damar ƙara lokaci a biɗar abubuwa na ruhaniya. Amma, Misalai 14:15 ta yi gargaɗi: “Marar-wayo yana gaskata kowacce magana: amma mai-hankali ya kan lura da al’amuransa da kyau.” Domin farin cikin da ke tattare da soma sabuwar sana’a, ana iya yin watsi da kasadar da hakan ya ƙunsa, da kuma rashin tabbaci na kasuwancin. (Yaƙub 4:13, 14) A irin wannan yanayin, ya kamata ka natsu!
4. Ta yaya za mu ‘lura da al’amuranmu’ sa’ad da muke auna tayi na kasuwanci?
4 Mutum mai hikima yakan bincika tayin kasuwancin da aka yi masa a hankali kafin ya yanke shawara. (Misalai 21:5) Irin wannan binciken a yawancin lokaci, yana bayyana ɓoyayyun haɗarurruka. Yi la’akari da yanayi na gaba: Wani mutum yana son ya ranci kuɗi domin ya soma kasuwanci kuma ya yi maka alkawarin cewa za ka ci riba sosai idan ka ranta masa kuɗin. Riba da za ka samu na iya jan ra’ayin ka, amma waɗanne haɗarori ne ke tattare da haka? Wanda ya yi rancen ya yarda zai biya kuɗin ko da yaya kasuwancin ya kasance, ko kuwa biyan bashin ya dangana ne a kan nasarar da aka samu a kasuwancin? Abin da ake nufi shi ne, za ka yarda ka yi hasarar kuɗinka idan kasuwancin ta faɗi? Za ka iya yin tambaya: “Me ya sa ake yin rance daga mutane? Bankuna suna ganin cewa irin kasuwancin yana da haɗari ne ƙwarai?” Idan ka yi tunani sosai game da haɗarurruka, hakan zai taimake ka ka bincika tayin sosai.—Misalai 13:16; 22:3.
5. (a) Wane mataki mai hikima ne Irmiya ya ɗauka sa’ad da ya sayi fili? (b) Me ya sa yana da muhimmanci a rubuta yarjejeniyar duka kasuwanci a kan takarda?
5 Sa’ad da annabi Irmiya ya sayi fili daga wajen ɗan kawunsa, wanda shi ma mai bauta wa Jehobah ne, ya yi takardar abin da ya saya a gaban shaidu. (Irmiya 32:9-12) Mutum mai hikima a yau zai tabbata cewa an rubuta yarjejeniya game da kasuwancin da ya shiga, ko da tare da danginsa ko kuma ’yan’uwa masu bi.a Idan akwai rubutacciyar yarjejeniya, hakan zai kawar da saɓani kuma za a sami haɗin kai. A wata sassa kuma, idan babu rubutacciyar yarjejeniya hakan na jawo saɓani sa’ad da matsalar kasuwanci ta taso tsakanin bayin Jehobah. Abin baƙin ciki, irin waɗannan matsalolin suna iya jawo ɓacin rai, da kuma hasarar ruhaniya.
6. Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali da haɗama?
6 Dole ne kuma mu mai da hankali da haɗama. (Luka 12:15) Domin muna ganin cewa za mu sami riba mai yawa, hakan zai iya rufe idanunmu ga haɗari da ke tattare da kasuwancin. Har ma wasu da suke morar gata a cikin hidimar Jehobah sun faɗa cikin irin wannan tarkon. Kalmar Allah ta yi mana gargaɗi: “Ku kawarda hankalinku daga ƙaunar kuɗi; ku haƙura da abin da ku ke da shi.” (Ibraniyawa 13:5) Ya kamata Kirista ya tambayi kansa sa’ad da yake tunani game da wani zarafi na kasuwanci, ‘Ya kamata in saka hannu?’ Yin rayuwa mai sauƙi wadda ke bisa bautarmu ga Jehobah zai kāre mu daga “kowace irin mugunta.”—1 Timothawus 6:6-10.
Ƙalubalen da Kiristoci Marasa Aure Suke Fuskanta
7. (a) Waɗanne ƙalubale ne Kiristoci marasa aure suke fuskanta? (b) Ta yaya ne zaɓen abokin aurenmu ya shafi amincinmu ga Allah?
7 Bayin Jehobah da yawa suna so su yi aure, amma har ila ba su sami abokin auren da ya dace ba. A wasu ƙasashe, ana matsawa mutane ƙwarai game da aure. Duk da haka, zarafin samun abokin aure a tsakanin ’yan’uwa masu bi wataƙila ba shi da yawa. (Misalai 13:12) Amma Kiristoci sun fahimci cewa bin umurnin Littafi Mai Tsarki na yin aure “cikin Ubangiji,” batu ne na kasancewa da aminci ga Jehobah. (1 Korinthiyawa 7:39) Domin tsayayya wa matsi da kuma jaraba da suke fuskanta, Kiristoci da ba su yi aure ba suna bukatar su natsu.
8. Wane matsi ne budurwa ’yar Shulem ta fuskanta, kuma yaya ne Kiristoci mata za su iya fuskantar irin wannan ƙalubalen?
8 A cikin Waƙar Waƙoƙi, wata yarinya da aka kira ’yar Shulem ta shiga zuciyar sarkin. Ya so ya jawo hankalinta ta wajen nuna mata dukiya, matsayi, da kuma daɗin baki, ko da yake tana da saurayin da take so. (Waƙar Waƙoƙi 1:9-11; 3:7-10; 6:8-10, 13) Idan ke mace ce Kirista, kina iya shiga zuciyar wani wanda ba ki so. Wani mutum a wajen aikinku, wataƙila wani mai matsayi, yana iya soma yi maki daɗin baki, ya yi maki alheri, ya kuma nemi damar kasancewa tare da ke. Ki mai da hankali da irin wannan. Ko da yake ba ko yaushe ba ne manufar irin wannan mutumin zai kasance na soyayya ko lalata, amma a yawancin lokaci manufarsa ke nan. Kamar budurwa ’yar Shulem, ki kasance “bango.” (Waƙar Waƙoƙi 8:4, 10) Da gaba gaɗi ki ƙi irin wannan sha’awar da ake miki. Ki sanar da abokan aikinki tun da wuri cewa ke Mashaidiyar Jehobah ce, kuma ki yi amfani da kowane zarafi ki yi musu wa’azi. Hakan zai kāre ki.
9. Waɗanne haɗarurruka ne ke akwai na soma dangantaka da bare a kan Intane? (Ka duba akwati da ke shafi na 27.)
9 Dandali a duniyar gizo na Intane da aka shirya don taimaka wa waɗanda ba su yi aure ba su sami wadda za su aura suna ƙaruwa. Wasu sun ɗauki wannan a matsayin hanyar sanin mutanen ne da ba don wannan ba ba za su taɓa sani ba. Amma, soma soyayya da wanda ba ka sani ba na da haɗari. Yana da wuya a gane gaskiya daga ƙarya a kan Intane. (Zabura 26:4) Ba dukan waɗanda suke da’awar cewa su bayin Jehobah ne suke bauta masa ba. Bugu da ƙari, zance a kan Intane na iya sa a soma soyayya mai ƙarfi nan da nan, kuma hakan na iya shafar fahiminmu. (Misalai 28:26) Ko a kan Intane ko ta wasu hanyoyi, ba hikima ba ne mu soma dangantaka na kud da kud da mutumin da ba mu san shi ba sosai.—1 Korinthiyawa 15:33.
10. Ta yaya ne ’yan’uwa masu bi za su iya ƙarfafa Kiristoci marar aure?
10 Jehobah yana “cike da tausayi” ga bayinsa. (Yaƙub 5:11) Ya sani cewa ƙalubalen da ke fuskantar Kiristoci waɗanda ba wai ba sa son su yi aure ba ne, a wani lokaci yana da ban ciwo, kuma yana ɗaukan amincinsu da tamani. Ta yaya ne wasu za su iya ƙarfafa su? Ya kamata mu dinga yaba musu a kai a kai domin biyayyarsu da kuma ruhun ba da kai. (Alƙalawa 11:39, 40) Muna iya saka su cikin shirye-shiryenmu na tarayya mai ƙarfafawa. Ka yi haka kuwa ba da daɗewa ba? Bugu da ƙari, muna iya yi musu addu’a, mu roƙi Jehobah ya taimaka musu su riƙe daidaituwarsu na ruhaniya su kuma samu farin ciki a bautar da suke yi masa. Ta wajen damuwarmu ta gaske, bari mu nuna cewa mun san tamanin waɗannan mutanen masu aminci kamar yadda Jehobah ya sani.—Zabura 37:28.
Fuskantar Rashin Lafiya
11. Waɗanne ƙalubale ne rashin lafiya ke iya jawo wa?
11 Ba shi da sauƙi sa’ad da mu ko wani ƙaunatacce yake rashin lafiya mai tsanani! (Ishaya 38:1-3) Sa’ad da muke neman magani mai kyau, yana da muhimmanci mu manne wa mizanai na Nassi. Alal misali, Kiristoci suna yin biyayya ga dokar Littafi Mai Tsarki na guje wa jini, kuma suna ƙin kowane irin hanyoyin magani ko na gano ciwo da ya ƙunshi sihiri. (Ayukan Manzanni 15:28, 29; Galatiyawa 5:19-21) Ga waɗanda ba su da ilimi game da hanyar magani kuwa, zaɓen kulawa na iya zame masu aiki. Menene zai iya taimaka mana mu natsu?
12. Ta yaya ne Kirista zai daidaita sa’ad da yake zaɓen hanyar magani?
12 “Mai-hankali ya kan lura da al’amuransa da kyau” ta wajen bincika Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai na Kirista. (Misalai 14:15) A sashen duniya inda babu isassun likitoci da asibitoci, wataƙila maganin gargajiya ne kawai ke akwai. Idan muna son mu karɓi irin wannan magani, muna iya samun bayanin da zai taimaka mana a Hasumiyar Tsaro na 15 ga Afrilu, 1987, shafuffuka na 26-29. Ya bayyana mana haɗarurruka da ke akwai. Alal misali, muna iya bincike game da waɗannan abubuwan: An san wannan mai maganin gargajiyar da yin sihiri ne? Maganin bisa yardar cewa allolin da aka yi wa laifi (ko kuwa ruhohin kakanni) ko maƙiyan da suka yi amfani da maita ne suke jawo rashin lafiya da mutuwa? Ana yin amfani da hadayu, surkulle, da wasu ire-iren sihiri wajen shirya ko amfani da maganin? (Kubawar Shari’a 18:10-12) Irin wannan binciken zai taimaka mana mu bi wannan hurarriyar shawara: “Ku auna abu duka; ku riƙe mai-kyau.”b (1 Tassalunikawa 5:21) Hakan zai taimaka mana mu riƙe daidaituwarmu.
13, 14. (a) Ta yaya za mu iya nuna sanin ya kamata a wajen kula da lafiyar jikinmu? (b) Me ya sa muke bukatar nuna sanin ya kamata sa’ad da muke tattauna batutuwan lafiya da kuma magani da wasu?
13 Muna bukatar mu kasance da sanin ya kamata a dukan fasaloli na rayuwa, har da kula da lafiyar jikinmu. (Filibbiyawa 4:5) Kula yadda ya kamata da lafiyar jikinmu za ta nuna cewa muna nuna godiya ga kyautar rai. Sa’ad da muka fuskanci matsaloli na rashin lafiya, muna bukatar mu mai da masa hankalinmu. Amma, ba za a taɓa samun cikakken lafayi ba har sai lokaci ya kai da Allah zai ‘warkar da al’ummai.’ (Ru’ya ta Yohanna 22:1, 2) Dole ne mu mai da hankali kada mu shagala da lafiyar jikinmu har hakan ya sa mu kawar da bukatunmu na ruhaniya.—Matta 5:3; Filibbiyawa 1:10.
14 Muna bukatar mu nuna daidaituwa da kuma sanin ya kamta sa’ad da muke tattauna batutuwa na lafiyar jiki da kuma magani da wasu. Kada mu yarda waɗannan batutuwan su sha kan tattaunawarmu sa’ad da muka taru don zumunci na ruhaniya a taron Kiristoci da kuma manyan taro. Bugu da ƙari, shawara game da magani ya ƙunshi mizanai na Littafi Mai Tsarki, lamirin mutum, da kuma dangantakarsa da Jehobah. Saboda haka, ba ƙauna ba ce mu cusa ra’ayinmu a kan ɗan’uwa mai bi ko kuwa mu matsa ma sa ya ƙi abin da lamirinsa ya zaɓa. Ko da yake ana iya tuntuɓar waɗanda suka kware a cikin ikilisiya don taimako, kowane Kirista ne zai “ɗauki kayan kansa” na hakkin yanke shawarar da ya yi, kuma kowanenmu “za ya kawo lissafin kansa ga Allah.”—Galatiyawa 6:5; Romawa 14:12, 22, 23.
Sa’ad da Muke Fuskantar Yanayi Mai Wuya
15. Ta yaya ne yanayi mai wuya ke iya zama ƙalubale?
15 Yanayi mai wuya na iya sa bayin Jehobah masu aminci su yi magana ko su aikata abin da ba daidai ba. (Mai-Wa’azi 7:7) Sa’ad da yake fuskantar jaraba mai tsanani, Ayuba ya kasance da rashin daidaituwa wanda hakan ya sa aka daidaita tunaninsa. (Ayuba 35:2, 3; 40:6-8) Ko da yake “Musa mai-tawali’u ne ƙwarai, gaba da kowane mutum da ke zaune a bisa fuskar duniya,” akwai lokacin da ya ji haushi kuma ya yi magana cikin fushi. (Litafin Lissafi 12:3; 20:7-12; Zabura 106:32, 33) Dauda ya nuna kamun kai sa’ad da ya ƙi kashe Sarki Saul, amma sa’ad da Nabal ya zage shi kuma ya zuba wa mutanensa ashar, Dauda ya yi fushi kuma ya yi rashin hikimarsa. Sai da Abigail ta saka baki, Dauda ya dawo cikin hankalinsa, kuma hakan ya hana shi yin mugun kuskure.—1 Samuila 24:2-7; 25:9-13, 32, 33.
16. Menene zai taimaka mana mu kauce wa aikatawa cikin fushi?
16 Muma muna iya fuskantar yanayi mai wuya da ke iya sa mu rasa hikimarmu. Bincika ra’ayin wasu a hankali kamar yadda Dauda ya yi, zai iya taimaka mana mu kauce wa aikatawa cikin fushi da kuma faɗawa cikin zunubi. (Misalai 19:2) Bugu da ƙari, Kalmar Allah ta gargaɗe mu: “Ku ji tsoro, kada kuwa ku yi zunubi: ku yi shawara da zuciyarku a bisa shimfiɗarku, ku yi shuru.” (Zabura 4:4) Inda ya yiwu, abin hikima ne mu natsu kafin mu ɗauki mataki ko yanke shawara. (Misalai 14:17, 29) Muna iya yin addu’a ga Jehobah, “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi.” (Filibbiyawa 4:6, 7) Wannan salamar daga Allah za ta ƙarfafa mu kuma za ta taimaka mana mu natsu.
17. Me ya sa dole ne mu dogara da Jehobah don mu natsu?
17 Duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na aikatawa cikin hikima da kuma kauce wa haɗarurruka, dukanmu mukan yi kuskure. (Yaƙub 3:2) Yana yiwuwa mu ɗauki wani mugun mataki ba tare da muna sane ba. (Zabura 19:12, 13) Fiye da haka, mu mutane ba ma iya kuma ba mu da ikon kiyaye takawarmu, Jehobah ne kaɗai ke da wannan ikon. (Irmiya 10:23) Muna yi masa godiya domin wannan tabbacin da ya ba mu: “Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.” (Zabura 32:8) Hakika, da taimakon Jehobah, muna iya nuna natsuwa.
[Hasiya]
a Domin ƙarin bayani a kan rubutacciyar yarjejeniya na kasuwanci, dubi Hasumiyar Tsaro, na 1 ga Agusta, 1997, shafuffuka na 30-31; 15 ga Nuwamba , 1986, shafuffuka na 16-17; da kuma Awake! 8 ga Fabrairu, 1983, shafuffuka na 13-15 na Turanci, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
b Wannan zai amfane waɗanda suke so su yi amfani da wata hanyar magani da ake jayayya a kai wajen magance wasu cututtuka.
Yaya za ka Amsa?
Ta yaya za mu iya nuna natsuwa
• idan aka ba mu zarafin yin kasuwanci?
• sa’ad da muke neman abokin aure?
• sa’ad da muke fuskantar rashin lafiya?
• sa’ad da muke cikin yanayi mai wuya?
[Akwati a shafi na 27]
Za ka dogara ne da Shi?
Bayanan da suke gaba sun fito ne a cikin Intane don waɗanda ba su yi aure ba:
“Duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu, babu tabbacin samun cikakken bayani game da mutumin.”
“Ba mu iya ba da tabbacin gaskiya da kuma amfanin duk wani bayani game da marasa aure.”
“Ra’ayi, shawara, kalamai, tayi, ko wasu bayanai da ke nan ciki na marubutan ne . . . kuma kada a dogara da su.”
[Hoto a shafi na 25]
“Mai-hankali ya kan lura da al’amuransa da kyau”
[Hotuna a shafuffuka na 26, 27]
Ta yaya ne Kiristoci mata za su iya yin koyi da budurwa ’yar Shulem?
[Hoto a shafi na 28]
“Ku auna abu duka; ku riƙe mai-kyau.”