Kuɗi da Ɗabi’a Darasi Daga Tarihi
A RANAR 7 ga Afrilu, a shekara ta 1630, kusan mutane ɗari huɗu cikin jirgin ruwa huɗu suka tashi daga Ingila zuwa Amirka. Mutane da yawa a cikinsu masu ilimi ne sosai. Wasu ’yan kasuwa ne masu arziki. Wasu suna cikin majalisar wakilai. Ana wahalar tattalin arziki a Ingila, kuma yaƙi na shekara talatin da ake yi a Turai (1618-1648) ya sa yanayin ya yi muni sosai. Hakan ya sa mutanen suka bar gidajensu, sana’arsu, da dangi don neman rayuwa mafi kyau.
Wannan ƙungiyar ’yan kasuwa ba masu neman nasara ba ne kawai. Amma, mutane ne masu tarbiyya masu himma da suke guduwa daga tsanantawa na addini.a Burinsu shi ne su kafa yankin mutane masu tsoron Allah inda su da zuriyarsu za su yi nasarar samun abin biyan bukata ban da bijirewa daga mizanan Littafi Mai Tsarki. Ba da daɗewa ba, bayan da suka sauka a garin Salem na Massachusetts, suka kama wani ƙaramin fili da ke gāɓar teku suka ce nasu ne. Suka kira wannan sabon wurin Boston.
Samun Daidaitawa na da Wuya
Gwamnarsu kuma shugabansu, John Winthrop, ya yi iya ƙoƙarinsa don mutanen ɗaɗɗaya su sami arziki kuma jama’ar sabon yankin su amfana. Yana son mutanen su sami kuɗi kuma su kasance masu halin kirki. Amma wannan ya yi wuya. Da yake ganin za a sami kaluɓale, ya yi wa abokansa magana sosai game da arziki tsakanin mutane “masu tsoron Allah.”
Kamar sauran shugabanni masu tarbiyya, Winthrop ya gaskata cewa biɗan arziki ba laifi ba ne. Ya ce ainihin dalilin neman arziki don a taimaki wasu ne. Ta haka, idan mutum yana da arziki sosai, zai fi yin alheri. ’Yar tarihi Patricia O’Toole ta ce: “Wasu cikin masu bin tarbiyyar ba su yarda da wannan ra’ayin ba. Samun arziki alamar albarkar Allah ce kuma hakan zai iya sa mutum yin fahariya . . . da kuma zunubai na jiki.”
Don a kauce wa zunubai na arziki da kuma alatu, Winthrop ya ce a yi amfani da arziki daidai kima da kuma kame kai. Amma ba da daɗewa ba, son samun riba na mutanensa ya saɓa wa ƙoƙarin da ya yi don su bi Allah kuma su ƙaunaci juna. Mutanen suka soma jayayya don suna ɗaukan cewa Winthrop yana sa baki a harkokinsu yadda bai kamata ba. Wasu suka soma cewa a zaɓi waɗanda za su riƙa tsai da shawara. Wasu suka nuna nasu ra’ayin ta wajen ƙaura zuwa garin Connecticut don su biɗi nasu harkoki.
O’Toole ta ce, “zarafi, ni’ima, da dimokuraɗiyya sun yi tasiri a rayukan masu tarbiyya na garin Massachusetts, kowannensu ya fi son biɗan burinsa, sun ƙi su bi ra’ayin Winthrop na yin amfani da arzikinsu su taimaki mutane.” A shekara ta 1649, Winthrop ya mutu kusan ba shi da ko kobo, yana da shekara 61. Ko da yake ƙungiyar ta kusan rushewa sun tsira duk da wahala da suka sha, Winthrop ya mutu bai rayu ya ga mafarkinsa ya kasance gaskiya ba.
An Ci Gaba da Nema
Ba Winthrop kaɗai ba ne yake son duniya mafi kyau. Kowace shekara dubbai suna ƙaura daga Afirka, kudu maso gabashin Asiya, Gabashin Turai, Amirka ta Arewa, suna neman rayuwa mafi kyau. Wasu cikinsu suna karanta sababbin littattafai masu yawa, suna halartar taro, suna kuma kallon Duniyar Gizo da ake yi kowace shekara inda ake yi musu alkawarin abin da za su yi su sami arziki. A bayane yake cewa mutane da yawa har ila suna ƙoƙarin samun kuɗi da fatan ba za su yasar da ɗabi’arsu ba.
Hakika, sakamakon abin baƙin ciki ne. Waɗanda suke neman arziki sau da yawa suna yasar da ɗabi’arsu har da imaninsu don neman abin duniya.
[Hasiya]
a Mutanen ’yan Farostatan ne cikin Cocin Ingila da suke son su tsabtace cocinsu daga kowane tasiri na Cocin Katolika a ƙarni na 16.