Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 7/1 pp. 22-26
  • Masu “Ɗauke Da Albishir Mai Daɗi”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Masu “Ɗauke Da Albishir Mai Daɗi”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Albishir da Kowa Ke Bukatan Ji
  • Abin da Ya Sa Muke Wa’azin Bishara
  • Saƙonmu—Bisharar Mulkin Allah
  • Saƙon da Zai “Warkar da Waɗanda Suka Karai a Zuci”
  • Yadda Saƙon Mulki Yake Taimako
  • “Roƙona ga Allah Saboda Su”
  • Su Wane ne Suke Wa’azin Labari Mai Dadi?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Fa’idodin Bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Albishirinku!
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • Akwai Bishara Da Dukan Mutane Suke Bukata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 7/1 pp. 22-26

Masu “Ɗauke Da Albishir Mai Daɗi”

“Me ya fi wannan kyau? A ga manzo yana . . . ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama.”—ISHAYA 52:7.

1, 2. (a) Waɗanne abubuwa masu ban tsoro ne suke faruwa a yau? (b) Yaya mutane da yawa suke ji game da jin labarai marasa daɗi kowane lokaci?

A YAU mutane a dukan duniya suna jin cewa suna nutsewa cikin labarai marasa daɗi. Sa’ad da suka buɗe rediyonsu suna jin rahotanni masu ban tsoro game da cututtuka masu kisa da ke damun duniya. Sa’ad da suka kunna talabijin suna ganin hotunan yara mayunwata masu neman taimako. Sa’ad da suka karanta jarida, suna ganin rahotanni game da fashewar bom da ke ragargaje gidaje wanda ke kashe mutane da yawa da ba su san hawa ba ba su san sauka ba.

2 Hakika, abubuwa masu ban tsoro suna faruwa kullum. Yanayin duniyar nan yana canjawa yana daɗa zama mummuna. (1 Korantiyawa 7:31) Wata jarida a Yammacin Turai ta ce, wani lokaci kamar dai dukan duniya “za ta kama wuta.” Babu shakka, yawancin mutane suna wahala! Wani mutum da aka yi ƙaulinsa a wani bincike game da labaran talabijin a Amirka, ya faɗi yadda miliyoyin mutane suke ji sa’ad da ya ce: ‘Raina yana ɓacewa ƙwarai, bayan na saurari labarai. Labaran babu daɗi ko kaɗan. Sai ka ji ba ka da na yi.’

Albishir da Kowa Ke Bukatan Ji

3. (a) Wace bishara ce Littafi Mai Tsarki ke sanarwa? (b) Me ya sa bisharar Mulki ke da tamani a gare ka?

3 A wannan duniya ta baƙin ciki, za a iya samun labari mai daɗi kuwa? Hakika za a iya samu! Abin sanyaya zuciya ne mu sani cewa Littafi Mai Tsarki ya yi shelar albishir mai daɗi. Albishir ne cewa Mulkin Allah zai kawo ƙarshen ciwo, yunwa, aikata laifi, yaƙi, da dukan ire-iren zalunci. (Zabura 46:9; 72:12) Ba wannan ba ne albishir da kowa ke son ya ji? Babu shakka, Shaidun Jehobah suna ganin cewa ya kamata kowa ya ji. Saboda haka, aka san su a ko’ina domin ƙoƙarin da suke yi na gaya wa mutanen al’ummai bishara ta Mulkin Allah.—Matiyu 24:14.

4. Waɗanne fannoni na hidimarmu ne za mu tattauna a wannan talifi, da kuma na gaba?

4 Menene za mu yi domin mu ci gaba da wannan wa’azin bisharar da kyau—har ma a yankunan da ba sa sauraro sosai? (Luka 8:15) Taƙaita fannoni uku masu muhimmanci game da aikinmu na wa’azin babu shakka, zai taimaka mana. Za mu duba (1) nufinmu, ko kuwa dalilin da ya sa muke wa’azi; na (2) saƙonmu; ko kuwa abin da muke wa’azinsa; da (3) hanyoyin, ko kuwa yadda muke wa’azi. Idan muka kasance da nufin da ya dace, idan an fahimci saƙonmu, kuma hanyoyinmu na yin sa suna da kyau, za mu ba mutane masu yawa zarafin jin labari mafi kyau—bishara ta Mulkin Allah.a

Abin da Ya Sa Muke Wa’azin Bishara

5. (a) Mecece take motsa mu mu saka hannu a hidima fiye da kome? (b) Menene ya sa za mu iya cewa yin biyayyarmu ga umurnin Littafi Mai Tsarki mu yi wa’azi yana nuna ƙauna ga Allah?

5 Bari mu tattauna fanni na ɗaya—muradinmu. Me ya sa muke wa’azin bishara? Domin dalilin da ya sa Yesu ya yi. Ya ce: “Ina ƙaunar Uban.” (Yahaya 14:31; Zabura 40:8) Ƙaunar Allah ce ke motsa mu. (Matiyu 22:37, 38) Littafi Mai Tsarki ya nuna nasabar ƙaunar Allah da hidima sa’ad da ya ce: “Ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa.” (1 Yahaya 5:3; Yahaya 14:21) Umurnan Allah sun haɗa da ‘a je a almajirtar’ ne? (Matiyu 28:19) Hakika. Yesu ya faɗi waɗannan kalaman, amma sun fito ne daga wurin Jehobah. Ta yaya? Yesu ya bayyana: “Ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai yadda Uba ya koya mini, haka nake faɗa.” (Yahaya 8:28; Matiyu 17:5) Saboda haka, ta wajen bin umurnin yin wa’azi, muna nuna wa Jehobah cewa muna ƙaunarsa.

6. A waɗanne hanyoyi ne ƙaunar Allah take motsa mu mu yi wa’azi?

6 Bugu da ƙari, ƙauna ga Jehobah tana motsa mu mu yi wa’azi domin muna so mu kawar da ƙaryace-ƙaryacen da Shaiɗan ke yaɗawa game da shi. (2 Korantiyawa 4:4) Shaiɗan ya tuhumi amincin sarautar Allah. (Farawa 3:1-5) Mu Shaidun Jehobah, muna so mu saka hannu wajen fallasa tsegumin Shaiɗan kuma mu tsarkake sunan Allah a gaban al’ummai. (Ishaya 43:10-12) Ƙari ga haka, muna saka hannu a hidima domin mun san halayen Jehobah da hanyoyinsa. Mun kusance shi kuma muna da muradi mai ƙarfi na gaya wa mutane game da Allahnmu. Hakika, nagartar Jehobah da kuma hanyoyinsa na adalci suna ba mu farin ciki da ba za mu daina yin magana game da shi ba. (Zabura 145:7-12) Mun motsa mu faɗi game da yabonsa da kuma “mafifitan al’amuran[sa]” ga waɗanda za su saurara.—1 Bitrus 2:9; Ishaya 43:21.

7. Ban da ƙaunar da muke yi wa Allah, domin wane dalili mai muhimmanci ne muke saka hannu a aikin wa’azi?

7 Akwai wani dalili mai muhimmanci da ya sa muke ci gaba da saka hannu a hidima: Muna so mu kawo sauƙi ga mutanen da labarai marasa daɗi suka shafa da kuma waɗanda suke wahala domin dalilai dabam dabam. A wannan, muna ƙoƙarin mu yi koyi da Yesu. Alal misali, duba abin da aka kwatanta a Markus sura 6.

8. Menene labarin da ke Markus sura 6 ya nuna game da yadda Yesu yake ji game da mutane?

8 Manzanni sun dawo daga wa’azi suka gaya wa Yesu game da dukan abin da suka yi da kuma abin da suka koyar. Yesu ya lura cewa manzannin sun gāji, sai ya gaya musu cewa su bi shi domin su “ɗan huta.” Sai suka tafi cikin jirgin ruwa zuwa wurin da ba kowa. Mutane suka bi su, suka bi su ta tudu, nan da nan suka tarar da su. Menene Yesu ya yi? “Ya ga taro mai yawa,” in ji labarin, ‘ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke ba makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa.’ (Markus 6:31-34) Ko da yake, ya gāji, Yesu ya ji tausayinsu kuma ya ci gaba da yi musu bishara. Babu shakka, Yesu ya ji tausayin mutanen sosai.

9. Menene muka koya daga labarin da ke Markus sura 6 game da muradinmu na yin wa’azi?

9 Menene muka koya daga wannan labarin? Da yake mu Kiristoci ne, dole ne mu yi wa’azin bishara da kuma almajirantarwa. Mun fahimci cewa hakkinmu ne mu yi bishara tun da yake nufin Allah ne “dukkan mutane su sami ceto.” (1 Timoti 2:4) Muna yin wa’azi ba domin hakki ba ne kawai, amma domin muna juyayi. Idan muka ji tausayin mutane yadda Yesu ya yi, zuciyarmu za ta motsa mu mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu ci gaba da yi musu bishara. (Matiyu 22:39) Idan muna da nufin da ya dace na yin hidima, hakan zai motsa mu mu yi wa’azin bishara babu ja da baya.

Saƙonmu—Bisharar Mulkin Allah

10, 11. (a) Ta yaya ne Ishaya ya kwatanta saƙon da muke wa’azinsa? (b) Ta yaya ne Yesu ya kawo “albishir mai daɗi,” kuma ta yaya ne bayin Allah na zamani suka bi misalin Yesu?

10 Fanni na biyu na hidimarmu fa—saƙonmu? Menene muke wa’azinsa? Annabi Ishaya ya ba da kwatanci mai kyau na saƙon da muke sanarwa: “Me ya fi wannan kyau? A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu, ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama. Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona, ‘Allahnki sarki ne!’ ”—Ishaya 52:7.

11 Furci mafi muhimmanci a wannan nassin “Allahnki sarki ne,” ya tuna mana saƙon da dole ne mu yi shelarsa, wato, bisharar Mulkin Allah. (Markus 13:10) Wannan ayar ta bayyana jigo mai kyau na saƙonmu. Ishaya ya yi amfani da kalmomi kamar su “salama,” “albishir mai daɗi,” da “nasara.” Ƙarnuka bayan Ishaya, a ƙarni na farko A.Z., Yesu Kristi ya cika wannan annabcin a hanya ta musamman ta wajen kafa misali a shelar albishir mai daɗi da himma, wato, zuwan Mulkin Allah. (Luka 4:43) A zamanin nan, musamman tun shekara ta 1919, Shaidun Jehobah sun bi misalin Yesu ta yin shelar bishara ta Mulkin Allah da ya kafa da himma da kuma albarkar da zai kawo.

12. Ta yaya ne bisharar Mulki ta shafi waɗanda suka gaskata da ita?

12 Ta yaya ne bishara ta Mulki ta shafi waɗanda suka gaskata da ita? A yau, kamar yadda yake a zamanin Yesu, bishara tana ba da bege kuma tana sanyaya zukata. (Romawa 12:12; 15:4) Tana ba masu zuciyar kirki bege domin sun koyi cewa akwai tabbatattun dalilai na gaskata cewa lokaci mafi kyau na zuwa a nan gaba. (Matiyu 6:9, 10; 2 Bitrus 3:13) Wannan begen na taimaka wa masu tsoron Allah su kasance da ra’ayi mai kyau. Mai zabura ya faɗi cewa ba sa “tsoron jin mugun labari.”—Zabura 112:1, 7.

Saƙon da Zai “Warkar da Waɗanda Suka Karai a Zuci”

13. Ta yaya ne annabi Ishaya ya kwatanta albarkatu na nan take da waɗanda suka gaskata da bisharar ke samu?

13 Ƙari ga haka, bisharar da muke wa’azinta tana sanyaya zuciya kuma tana kawo albarka ga waɗanda suka saurara. Ta yaya? Annabi Ishaya ya kwatanta wasu daga cikin albarkatun sa’ad da ya annabta: “Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, in warkar da waɗanda suka karai a zuci, in yi shelar kwance ɗaurarru, da kuma ’yanci ga waɗanda ke cikin kurkuku. Ya aike ni in yi shela, cewa lokaci ya yi da Ubangiji zai ceci mutanensa, ya kuma ci nasara a kan abokan gābansu. Ya aike ni domin in ta’azantar da masu makoki.”—Ishaya 61:1, 2; Luka 4:16-21.

14. (a) Menene wannan furcin “warkar da waɗanda suka karya a zuci” ke nunawa game da saƙon Mulki? (b) Ta yaya muke nuna damuwar Jehobah ga waɗanda suka karai a zuci?

14 Annabcin ya ce game da wa’azin bishara, Yesu zai “warkar da waɗanda suka karai a zuci.” Ishaya ya yi amfani da kwatanci mai kyau! In ji wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki, kalmar Ibrananci da aka fassara “warkar da” sau da yawa “ana amfani da wannan kalmar idan ana zancen ‘ɗaurewa’ da bandeji, jinyar masu rauni da kuma warkar da su.” Nas tana iya ɗaure wurin da mutum ya ji rauni da bandeji don ta taimaka masa. Haka nan, sa’ad da suke wa’azin saƙon Mulki, masu shela suna taimaka wa dukan waɗanda suka saurare su da suke wahala a wata hanya. Ta wajen taimaka wa waɗanda suke da bukata, suna nuna damuwar Jehobah. (Ezekiyel 34:15, 16) Mai zabura ya ce game da Allah: “Yakan warkar da masu karyayyiyar zuciya, yakan ɗaure raunukansu.”—Zabura 147:3.

Yadda Saƙon Mulki Yake Taimako

15, 16. Wane labari na rayuwa ne ya kwatanta yadda saƙon Mulki ke taimakawa da kuma ƙarfafa waɗanda suke bukatan taimako?

15 Labarai masu yawa sun kwatanta yadda saƙon Mulki ke taimakawa da kuma ƙarfafa waɗanda suka karai a zuci. Ka yi la’akari da Oreanna, wata tsohuwa a Amirka ta Kudu wadda ta riga ta fid da rai a rayuwa. Wata Mashaidiyar Jehobah ta fara ziyartar Oreanna kuma ta fara karanta mata Littafi Mai Tsarki da kuma littafin nan Littafi na Na Labarun Bible.b Da farko, matar mai baƙin ciki tana saurarar karatun a kwance a kan gado idanunta a rufe, tana numfashi sama-sama. Ba da daɗewa ba, ta fara zama a kan gadonta sa’ad da ake yi mata karatun. Bayan wasu lokatai, sai ta fara zama a kan kujera a ɗakinta tana jiran malamarta ta Littafi Mai Tsarki. Bayan haka, matar ta fara halartar taron Kirista a Majami’ar Mulki. Domin abubuwa da ta koya a waɗannan tarurruka sun ƙarfafa ta, ta fara ba da mujallu na Littafi Mai Tsarki ga duk wanda zai wuce a gaban gidanta. A shekararta ta 93, Oreanna ta yi baftisma ta zama ɗaya cikin Shaidun Jehobah. Saƙon Mulki ya sabonta muradinta na rayuwa.—Karin Magana 15:30; 16:24.

16 Saƙon Mulki na ba da cikakken taimako ga waɗanda suka sani cewa sun kusa mutuwa domin rashin lafiya. Alal misali, Maria da ke Yammacin Turai. Tana ciwon ajali, kuma ta fid da rai. Mai baƙin ciki ce sosai sa’ad da Shaidun Jehobah suka sadu da ita. Amma, sa’ad da ta koyi nufin Allah, rayuwarta ta kasance da ma’ana. Ta yi baftisma ta zama mai ƙwazo a aikin wa’azi. A shekaru biyu na ƙarshen rayuwarta an ga tana farin ciki kuma tana da bege. Maria ta mutu tana da cikakken bege na tashin matattu.—Romawa 8:38, 39.

17. (a) Ta yaya ne saƙon Mulki ke shafan rayuwar waɗanda suka gaskata da ita? (b) A waɗanne hanyoyi ne kai da kanka ka shaida cewa Jehobah “yakan ta da waɗanda aka wulakanta”?

17 Irin waɗannan rahotannin na nuna abin da saƙon Mulki ke iya yi a rayuwar waɗanda suke son gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Waɗanda suke makokin mutuwar wanda suke ƙauna, suna samun ƙarfafa sa’ad da suka koyi game da begen tashin matattu. (1 Tasalonikawa 4:13) Mutanen da suke talauci kuma suke kokawar ciyar da iyalinsu suna samun daraja da gaba gaɗi sa’ad da suka koyi cewa Jehobah ba zai taɓa yasar da su ba idan suka kasance da aminci a gare shi. (Zabura 37:28) Da taimakon Jehobah, waɗanda baƙin ciki ya sha musu kai, a hankali suna samun ƙarfafa da suke bukata don su jimre—a wani yanayi, sun sha kan irin wannan rashin lafiyar. (Zabura 40:1, 2) Hakika, domin ƙarfafawar da ake samu ta Kalmarsa, Jehobah yanzu yana “ta da waɗanda aka wulakanta.” (Zabura 145:14) Ta wurin lura da yadda bishara ta Mulkin Allah ke ta’azantar da waɗanda suka karai a zuci a yankinmu da kuma ikilisiyarmu ta Kirista, ana tuna mana a kai a kai cewa muna da labarai mafiya kyau a yau!—Zabura 51:17.

“Roƙona ga Allah Saboda Su”

18. Ta yaya ne ƙin bisharar da Yahudawa suka yi ya shafi Bulus, kuma me ya sa?

18 Ko da yake saƙonmu ne ke ɗauke da labarai mafi kyau, yawanci sun ƙi shi. Ta yaya ne wannan zai shafe mu? Yadda ya shafi manzo Bulus. A yawancin lokaci yana yi wa Yahudawa wa’azi, amma yawancinsu sun ƙi wannan saƙo na ceto. Ƙinsu ya shafi Bulus sosai. Ya ce: “Ina da matuƙar baƙin ciki da kuma takaici marar yankewa a zuciyata.” (Romawa 9:2) Bulus ya ji tausayin Yahudawan da ya yi wa wa’azi. Ya yi baƙin ciki domin sun ƙi bishara.

19. (a) Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa muna iya sanyin gwiwa a wasu lokatai? (b) Menene ya taimaka wa Bulus ya ci gaba da aikinsa na wa’azi?

19 Mu ma muna yin wa’azin bishara cikin juyayi. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa muna iya sanyin gwiwa sa’ad da mutane suka ƙi saƙon Mulki. Irin wannan halin ya nuna cewa muna damuwa sosai da lafiyar ruhaniyar waɗanda muke yi wa wa’azi. Amma dai, ya kamata mu tuna misalin manzo Bulus. Menene ya taimaka masa ya ci gaba da aikin wa’azi? Ko da yake ƙin bisharar da Yahudawa suka yi ya sa shi baƙin ciki, Bulus bai karaya da Yahudawa ba, ko ya yi tunanin cewa ba za a iya taimaka musu ba. Begensa shi ne cewa akwai wasu da za su karɓi Kristi. Saboda haka, Bulus ya rubuta yadda yake ji game da kowane Bayahude: “Muradin zuciyata da kuma roƙona ga Allah saboda su, shi ne su sami ceto.”—Romawa 10:1.

20, 21. (a) Game da hidimarmu, ta yaya ne za mu iya bin misalin Bulus? (b) Wane fanni na hidimarmu ne za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Ka lura da abubuwa biyu da Bulus ya taƙaita. Muradin zuciyarsa ne cewa wasu su sami ceto, kuma ya roƙi Allah game da waɗannan. A yau, muna bin misalin Bulus. Muna da sha’awar samun duk wanda ke da zuciyar kirki game da bishara. Muna ci gaba da yin addu’a ga Jehobah don samun irin waɗannan mutanen domin mu taimaka musu su bi tafarkin da zai kai su ga samun ceto.—Karin Magana 11:30; Ezekiyel 33:11; Yahaya 6:44.

21 Amma dai, domin mu kai saƙon Mulki ga mutane masu yawa, muna bukatar mu mai da hankali ba kawai ga dalili da kuma abin da muke wa’azi ba, amma yadda muke wa’azi. Za a tattauna wannan batun a talifi na gaba.

[Hasiya]

a Wannan talifin zai tattauna fannoni na ɗaya da na biyu. Talifi na biyu zai tattauna na uku.

b Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

Menene Ka Koya?

• Domin waɗanne dalilai ne muke saka hannu a hidima?

• Menene ainihin saƙon da muke wa’azinsa?

• Waɗanne albarkatu ne waɗanda suka karɓi saƙon Mulki suka shaida?

• Menene zai taimaka mana mu ci gaba da hidimarmu?

[Hotuna a shafi na 24]

Saƙon Mulki na ƙarfafa waɗanda suka karai a zuci

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba