“Albarka tā Tabbata ga Waɗanda Suka San Talaucinsu Na Ruhu”
IDAN tsuntsaye suka tashi da safe, sukan yi kuka na ɗan lokaci kafin su tashi neman abinci. Idan yamma ta yi, sukan dawo sheƙarsu, sukan ɗan yi kuka kafin su yi barci. Idan lokaci ya yi, suna saduwa, su yi ƙwai, sa’an nan su ƙyanƙyashe. Sauran dabbobi ma suna bin nasu tsarin rayuwa.
Mu mutane mun bambanta. Hakika, muna cin abinci, muna yin barci, kuma muna haihuwa, amma duka waɗannan abubuwa ba sa gamsar da yawancinmu. Muna so mu san dalilin da ya sa muke duniya. Muna neman ma’anar rayuwarmu. Kuma muna da bege don nan gaba. Waɗannan bukatun suna nuna wani hali na musamman na mutane—ruhaniya, ko kuwa bukatar abubuwa na ruhaniya.
An Halicce Su a Siffar Allah
Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalilin da ya sa mutane suke bukatar abubuwa na ruhaniya, ya ce: “Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su.” (Farawa 1:27) Halittarmu da aka yi a ‘siffar Allah’ na nufin cewa muna iya nuna wasu halaye na Allah, duk da cewa mu masu zunubi ne kuma ajizai. (Romawa 5:12) Alal misali, muna iya ƙera wani abu. Muna da hikima, muradi na yin gaskiya, da kuma ƙauna ta sadaukar da kai ga juna. Bugu da ƙari, muna iya yin tunani a kan abin da ya wuce kuma mu yi gyara don gaba.—Karin Magana 4:7; Mai Hadishi 3:1, 11; Mika 6:8; Yahaya 13:34; 1 Yahaya 4:8.
Iyawarmu ta ruhaniya na bayyana a muradinmu na bauta wa Allah. Ba za mu iya samun farin ciki na gaskiya da na dindindin ba sai dai mun kasance da cikakken dangantaka da Mahaliccinmu. “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu,” in ji Yesu. (Matiyu 5:3) Dole ne mu mai da hankali domin mu biya wannan muradin da gaskiya ta ruhaniya—gaskiya game da Allah, mizanansa, da kuma manufarsa game da ’yan adam. A ina ne za mu iya samun gaskiya ta ruhaniya? A cikin Littafi Mai Tsarki.
“Maganarka Ita Ce Gaskiya”
Manzo Bulus ya rubuta: “Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuwa wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali.” (2 Timoti 3:16) Kalmomin Bulus sun jitu da ta Yesu, wanda ya ce a cikin addu’a ga Allah: “Maganarka ita ce gaskiya.” A yau mun sani cewa wannan Magana ita ce Littafi Mai Tsarki, kuma hikima ce mu tabbata cewa imaninmu da mizananmu sun jitu da ita.—Yahaya 17:17.
Ta gwada imaninmu da Kalmar Allah, muna yin koyi ne da mutanen Biriya ta dā, waɗanda suka tabbata cewa abin da Bulus ya koyar ya jitu da Nassosi. Maimakon ya zargi mutanen Biriya, Luka ya yaba musu domin halinsu. Ya rubuta: “Sun karɓi maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.” (Ayyukan Manzanni 17:11) Domin addinai da kuma koyarwa game da ɗabi’a masu yawa da suka saɓa wa juna a yau, yana da muhimmanci mu yi koyi da mutanen Biriya.
Wata hanya ta gane gaskiya ta ruhaniya ita ce ganin yadda take rinjayar rayuwar mutane. (Matiyu 7:17) Alal misali, rayuwa da ta jitu da gaskiyar Littafi Mai Tsarki ya kamata ta motsa mutum ya zama magidancin kirki, uba na kirki, matar kirki, ko kuwa uwar kirki, domin hakan zai daɗa farin cikin iyali kuma ya kyautata wadatar zuci. “Albarka tā fi tabbata ga waɗanda ke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta,” in ji Yesu.—Luka 11:28.
Kalaman Yesu sun tuna mana Ubansa na sama, wanda ya ce wa Isra’ila ta dā: “Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi. Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum! Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominku kamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba! Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwa da suke bugowa zuwa gāɓa.” (Ishaya 48:17, 18) Wannan kalamin na ƙauna ya kamata ya motsa dukan mutanen da ke ƙaunar alheri da aminci!
Wasu Sun fi Son ‘Kunnensu ya yi Musu Ƙaiƙayi’
Allah ya yi wannan kalami ga Isra’ilawa domin addinan ƙarya sun yaudare su. (Zabura 106:35-40) Ya kamata mu ma mu kāre kanmu daga ƙarya. Game da waɗanda suke da’awar cewa su Kiristoci ne, Bulus ya rubuta: “Lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu na ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu. Za su toshe kunnensu ga jin gaskiya.”—2 Timoti 4:3, 4.
Shugabannin addinai suna sa kunnen mutane ya yi ƙaiƙaiyi ta wajen ƙyale halaye da ke gamsar da sha’awoyi marasa kyau, kamar su zina, luwaɗi, da kuma maye. Littafi Mai Tsarki ya faɗa dalla-dalla cewa duk wanda ya amince da irin waɗannan abubuwa da kuma masu yin su ba za su “sami gado a cikin Mulkin Allah” ba.—1 Korantiyawa 6:9, 10; Romawa 1:24-32.
Babu shakka, ba shi da sauƙi a bi mizanan Littafi Mai Tsarki, musamman a lokacin da aka fuskanci ba’a, amma ana iya yin hakan. A cikin Shaidun Jehobah akwai mutane masu yawa da a dā ’yan ƙwaya ne, mashaya, mazinata, mafaɗata, ɓarayi, da kuma maƙaryata. Duk da haka, sun yi amfani da Kalmar Allah kuma da taimakon ruhu mai tsarki, sun yi canji a rayuwarsu domin su “yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji.” (Kolosiyawa 1:9, 10; 1 Korantiyawa 6:11) Da yake sun yi salama da Allah, sun sami kwanciyar hankali, kuma kamar yadda za mu gani, sun sami cikakken bege na nan gaba.
Begen Mulki
Mulkin Allah zai cika begen Littafi Mai Tsarki na salama ta dindindin ga mutane masu biyayya. “Mulkinka yā zo, a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a sama,” in ji Yesu a addu’arsa ta misali. (Matiyu 6:10) Hakika, Mulkin Allah ne kaɗai zai iya ba da tabbacin cewa nufin Allah zai kasance a duniya. Me ya sa? Domin wannan Mulkin sama—gwamnati a hannun Yesu Kristi—shi ne hanyar da Allah ke nuna ikon mallakarsa bisa duniya.—Zabura 2:7-12; Daniyel 7:13, 14.
A matsayinsa na Sarkin Mulkin sama, Yesu Kristi zai ’yantar da mutane masu biyayya daga dukan ire-iren bauta, har da zunubin Adamu da kuma gadon rashin lafiya da kuma mutuwa da muka yi. Wahayin Yahaya 21:3, 4 ya ce: “Kun ga, mazaunin Allah na tare da mutane. [Jehobah Allah] . . . zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”
Salama za ta dawwama a dukan duniya. Me ya sa za mu kasance da wannan tabbacin? An bayyana dalilin a Ishaya 11:9 wadda ta ce: “A kan Sihiyona, dutse tsattsarka, [a tsakanin talakawan Mulkin] ba wani macuci ko mugu. Ƙasar za ta cika da sanin Ubangiji kamar yadda tekuna ke cike da ruwa.” Hakika, dukan mutane a duniya za su kasance da cikakken sani na Allah kuma za su yi masa biyayya. Wannan begen ya faranta maka zuciya kuwa? Idan haka ne, yanzu ne lokacin da ya kamata ka soma neman ‘sanin Jehobah.’
Za ka Saurari Saƙon Mulkin Kuwa?
Ta wurin Mulkin, Allah zai kau da dukan ayyukan Shaiɗan kuma zai ilimantar da mutane a hanyoyinsa na adalci. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne da Yesu ya mai da hankali a koyawarsa game da wannan Mulkin. Ya ce: “Dole sai in yi bishara ta mulkin Allah, . . . gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luka 4:43) Kristi ya umurci almajiransa su gaya wa mutane wannan saƙon. (Matiyu 28:19, 20) Ya annabta, “za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.” (Matiyu 24:14) Ƙarshe na kusatowa sosai. Saboda haka, yana da muhimmanci mutane masu zuciyar kirki su saurari wannan bishara ta ceton rai!
Albert ya ji saƙon Mulki sa’ad da matarsa da ɗansa suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Da farko, Albert yana nuna shakka. Har ma ya umurci wani limami ya ziyarci matarsa da ɗansa domin ya fallasa Shaidun. Amma limamin ba ya son ya saka hannu. Saboda haka, Albert ya yanke shawara cewa zai saurari tattaunawar Littafi Mai Tsarkin domin ya fid do da kurakurai. Bayan nazari na farko, ya soma nazari, kuma yana ɗokin samun ƙarin sani. Ya bayyana dalilin da ya sa halinsa ya canja. “Wannan shi ne abin da nike nema,” in ji shi.
A ƙarshe, Albert ya soma biyan muradinsa na ruhaniya, kuma bai taɓa ja da baya ba. Gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta ba shi abin da yake ta nema a dukan rayuwarsa—wato, magance rashin gaskiya da cin hanci da suka kewaye mutane da kuma bege don nan gaba. Gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta ba shi kwanciyar rai. Ka biya murandinka na bukatu na ruhaniya kuwa? Idan kana son ƙarin bayani, Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka.
[Box/Hotuna a shafi na 5]
An Biya Maka Bukatarka Ta Ruhaniya?
Abinci na ruhaniya da kake samu yana gamsar da kai? Muna gayyatarka ka karanta waɗannan tambayoyi na gaba kuma ka zaɓi waɗannan za ka iya ba da amsarsu daidai.
□ Wanene Allah, kuma menene sunansa?
□ Wanene Yesu Kristi? Kuma me ya sa ya mutu? Ta yaya mutuwarsa ta amfane ka?
□ Shin da Iblis kuwa? Idan da Iblis, daga ina ya fito?
□ Menene yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu?
□ Menene nufin Allah domin duniya da kuma ’yan adam?
□ Menene Mulkin Allah?
□ Menene mizanin Allah na ɗabi’a?
□ A iyali, wane hakki Allah ya ɗora wa mata da mijinta? Waɗanne mizanai ne na Littafi Mai Tsarki suke kawo farin ciki a iyali?
Idan ba ka da tabbacin amsar waɗannan tambayoyi, kana iya tambaya a ba ka mujallar nan Menene Allah Yake Bukata a Garemu? Shaidun Jehobah ne suka wallafa a kusan harsuna 300, wannan mujallar ta tattauna batutuwa 16 kuma ta amsa dukan tambayoyi da aka yi a baya.
[Hotuna a shafi na 3]
Ba kamar dabbobi ba, mutane suna da bukatu na ruhaniya
[Hoto a shafi na 4]
“Saboda kunnensu na ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa”—2 Timoti 4:3
[Hoto a shafi na 6]
Mulkin Almasihun Allah zai kawo salama na dindindin