Gaba Gaɗi A Lokacin Hamayya
WANI taron ’yan banza sun tilasta wa Gayus da Aristarkus abokai biyu na manzo Bulus su shiga gidan wasa na Afisa. A wajen, taron da suka fusata suka ɗaga murya gaba ɗaya na awa biyu suna cewa: “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!” (Ayyukan Manzanni 19:28, 29, 34) Shin abokan Bulus sun tsaya tsayin daka ne sa’ad da suke fuskantar wannan hamayyar? Menene ya jawo wannan yanayin?
Bulus ya yi wa’azi a birnin Afisa na kusan shekara uku babu matsala. Domin haka, Afisawa da yawa suka daina bauta wa gumaka. (Ayyukan Manzanni 19:26; 20:31) Afisa na da ƙaramin ɗakin bauta na gunkin azurfa da ke a Artimas, allaniya ce mai kawo ni’ima, wadda babban haikalinta na gaban birnin. Ana ɗora ƙananan alamun waɗannan gumaka na haikalin a hannu kamar kambu ko kuma a saka a gidaje. Kiristoci ba sa sayan irin waɗannan gumaka.—1 Yahaya 5:21.
Dimitriyus, ɗaya cikin masu ƙera azurfa yana ganin hidimar Bulus za ta ɓata musu kasuwa inda suke samun riba sosai. Ta wajen amfani da rabin gaskiya da ƙarin gishiri, ya shawo kan sauran maƙeran cewa dukan mutanen Asiya Ƙarama za su daina bauta wa Artimas. Da maƙeran suka fusata suka ɗaga murya suna yabon Artimas, aka soma zanga-zanga sai dukan birnin ya ruɗe.—Ayyukan Manzanni 19:24-29.
Mutane dubbai suka taru a gidan wasa mai ɗaukan ’yan kallo 25,000. Bulus yana son ya yi wa taron magana, amma abokansa ma’aikata suka ce masa kada ya yi hakan. A ƙarshe, sanannen ma’aikacin birnin ya sa taron suka yi shuru, kuma Gayus da Aristarkus suka tsira, ba abin da ya same su.—Ayyukan Manzanni 19:35-41.
A yau, mutanen Allah suna iya fuskantar ’yan hamayya da masu zanga-zanga sa’ad da suke yin hidimarsu. Sau da yawa suna wa’azin bishara a birane inda ake bautar gumaka, ake lalata, kuma matasa suna mugunta. Duk da haka, suna yin koyi da manzo Bulus wanda ‘bai ji nauyin sanar da mutane a sarari, da kuma gida gida’ a birnin Afisa ba. (Ayyukan Manzanni 20:20) Suna farin ciki sa’ad da suka ga ‘Maganar Jehobah ta ƙara haɓaka, ta kuma fifita ƙwarai.’—Ayyukan Manzanni 19:20.