Abin da Za a Tuna
WANE abu ne wannan? Mutuwar wani mutum ne da ya mutu kusan shekara 2,000 da ta shige. “Ina ba da raina in ɗauko shi kuma” ya ce. “Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi.” (Yahaya 10:17, 18) Wannan mutumin Yesu Kristi ne.
Yesu ya umurci mabiyansa su tuna da mutuwarsa. Ana kuma kiran wannan ‘jibin maraice na Ubangiji,’ ko kuma “jibin Ubangiji.” (1 Korantiyawa 11:20) Shaidun Jehobah da kuma abokanansu za su kiyaye wannan abin da Yesu ya kafa domin a tuna mutuwarsa a ranar Alhamis, 24 ga Maris, 2005 bayan faɗuwar rana.
Jawabi daga Littafi Mai Tsarki zai yi bayani game da ma’anar gurasa marar yisti da kuma jar giya da aka yi amfani da su a wannan lokaci. (Matiyu 26:26-28) Jawabin kuma zai amsa tambayoyin nan: Sau nawa ya kamata Kiristoci su yi wannan tuni? Waye ya kamata ya ci waɗannan alamun gurasa da giya? Waye ya amfana daga mutuwar Yesu? Wannan tuni mai muhimmanci zai taimaki kowa ya fahimci dalilin rayuwa da kuma mutuwar Yesu.
Ana gayyatarka zuwa wannan kiyaye Tuni na Mutuwar Yesu. Don Allah ka tambayi Shaidun Jehobah da suke yankinku domin wurin taro da kuma lokaci.