Ka Faɗi Maganar Allah Da Gaba Gaɗi
‘Ka tafi ka yi magana da jama’ata.’—AMOS 7:15.
1, 2. Wanene Amos, kuma menene Littafi Mai Tsarki ya bayyana game da shi?
WANI firist ya ƙalubalanci wani shaidan Jehovah sa’ad da yake cikin hidimarsa. Firist ɗin ya ce: ‘Ka daina wa’azi! Ka bar wannan wajen!’ Menene shaidan ya yi? Ya bi umurnin ne, ko ko ya ci gaba da faɗin maganar Allah da gaba gaɗi? Za ka sani domin shaidan ya rubuta abin da ya faru masa cikin littafi mai ɗauke da sunansa. Littafin Amos ne na Littafi Mai Tsarki. Kafin mu ga yadda Amos ya fuskanci firist ɗin, bari mu yi bayani game da tarihin Amos.
2 Wanene Amos? Yaushe ya rayu kuma a ina yake da zama? Mun sami amsoshin waɗannan tambayoyi a Amos 1:1: “Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa . . . a lokacin da Azariya ke sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa ke sarautar Isra’ila.” Amos yana zaune ne a Yahuza. Garinsu Tekowa ne mai nisan mil goma a kudancin Urushalima. Ya yi rayuwarsa a ƙarshen ƙarni na tara K.Z., lokacin da Sarki Azariya yake sarauta a Yahuza, Sarki Yerobowam na II kuma a ƙabilu goma na Isra’ila. Amos makiyayi ne. Amos 7:14, ta ce, “makiyayi” ne, mai kuma “lura da itatuwan ɓaure.” Saboda haka, yana rabin shekara a aikin girbi. Yana nuka ɓaure. Ana irin wannan aikin ne domin a hanzarta nunan ɓauren. Ba ƙaramin aiki ba ne.
‘Ka Tafi ka Yi Magana’
3. Ta yaya koyo game da Amos zai taimake mu idan muna jin cewa ba mu cancanta ba mu yi wa’azi?
3 Amos ya ce cikin gaskiya: “Ni ba annabi ba ne. Wannan ba aiki na ba ne.” (Amos 7:14) Hakika, ba a haifi Amos ɗan annabi ba, kuma ba a koyar da shi ya zama annabi ba. Cikin dukan mutanen Yahuza, Jehovah ya zaɓi Amos ya yi wannan aikin. A wannan lokaci, Allah bai zaɓi sarki ba, ko ƙwararren firist, ko kuma yarima mai hannu da shuni. Wannan ya koya mana darasi na tabbaci. Ƙila ba mu da wani babban matsayi ko kuma yawan ilimi. Amma wannan ya kamata ne ya sa mu ji ba mu cancanci mu yi wa’azin maganar Allah ba? Ko kaɗan! Jehovah zai iya shirya mu mu yi shelar saƙonsa—har ma a yankuna da suke da wuya. Tun da yake abin da Jehovah ya yi wa Amos ke nan, zai dace dukan waɗanda suke so su faɗi maganar Allah da gaba gaɗi su bincika misalin da wannan annabi mai gaba gaɗi ya bari.
4. Me ya sa yake da wuya Amos ya yi annabci a Isra’ila?
4 Jehovah ya umurci Amos: ‘Tafi ka yi magana da jama’ata, wato Isra’ila.’ (Amos 7: 15) Wannan aiki ne mai wuya. A wannan lokacin, masarautar ƙabilu goma na Isra’ila suna zama cikin salama da kwanciyar rai kuma ga wadata. Da yawa sun gina gidajen “damuna” da kuma na “rani” waɗanda aka gina da “dutse” ba da tubali ba. Wasu suna da manyan kujeru da aka yi da haure, kuma suna shan ruwan inabi daga ‘kyawawan gonakin inabinsu.’ (Amos 3:15; 5:11) Domin haka, mutane da yawa ba su damu da wani abu ba. Babu shakka, yankin da aka ba Amos yana kama da waɗanda yawancinmu muke wa’azi ciki a yau.
5. Waɗanne abubuwa ne na rashin adalci wasu Isra’ilawa suke yi?
5 Ba laifi ba ne Isra’ilawa su mallaki abin duniya. Amma wasu Isra’ilawa suna tara abin duniya ne ta hanyoyi na rashin gaskiya. Mawadata suna “wulakanta kasassu,” suna yi wa “matalauta danniya.” (Amos 4:1) Attajirai masu iko, alƙalai, da kuma firistoci suna haɗa kai wajen yi wa matalauta ƙwace. Bari mu koma zamanin, mu lura da abin da waɗannan mutane suke yi.
An Ƙeta Dokar Allah
6. Ta yaya attajirai na Isra’ila suke zaluntar wasu?
6 Da farko mu je kasuwa. A nan attajirai marasa gaskiya suna yin awo da “ma’aunin zalunci” kuma suna “daidaita ma’auni yadda za su cuci mai saya” suna kuma “sayar da ruɓaɓɓen hatsi.” (Amos 8:5, 6) Attajiran suna cutar masu ciniki a yawan abin da suke sayar musu, ga tsada, amma marar kyau. Bayan attajiran sun zalunci matalautan har ba sauran abin da ya rage a hannunsu, dole matalautan su sayar da kansu su zama bayi. Sai, attajiran su saye su, a farashin “takalma bi-shanu.” (Amos 8:6) Don Allah ka ga irin wannan! Waɗannan attajirai masu haɗama ba su ɗauki ’yan’uwansu Isra’ilawa a bakin kome ba sai takalmi! Wannan hakika zaluntar mabukata ne, kuma muguwar ƙeta Dokar Allah ce! Duk da haka, waɗannan attajirai suna kiyaye “Asabar.” (Amos 8:5) Hakika, masu bin addini ne amma a waje kawai.
7. Me ya taimaki attajirai Isra’ilawa su ƙeta Dokar Allah?
7 Ta yaya attajiran nan suka yi nasara wajen ƙeta Dokar Allah, da ta ce: ‘Ka ƙaunaci sauran mutane kamar yadda kake ƙaunar kanka’? (Littafin Firistoci 19:18) Sun yi nasara domin alƙalai—waɗanda ya kamata su sa a bi Dokar—abokansu ne wajen ƙeta doka. A ƙofar birni inda ake shari’a, alƙalai suke ‘karɓan cin hanci, suna hana a yi wa talakawa shari’ar adalci.’ Maimakon su kāre matalautan, sai alƙalan su ci amanarsu domin cin hanci. (Amos 5:10, 12) Alƙalan su ma sun yi watsi da Dokar Allah.
8. Wane irin mugun abu ne firistoci suke kawar da kansu?
8 To, wane aiki firistocin Isra’ila suke yi? Domin mu gano, dole ne mu mai da hankalinmu zuwa ga wani wuri. Dubi irin zunubi da firistoci suka ƙyale a ‘haikalin allahnsu’! Allah ya ce ta bakin Amos: “Tsofaffi da samari [mutum da ubansa] sukan tafi wurin karuwan Haikali. Ta haka suke ɓata sunana mai tsarki.” (Amos 2:7, 8) Dubi irin wannan! Tsoho Ba’isra’ile da ɗansa suka yi lalata da karuwar haikali guda. Kuma waɗannan miyagun firistoci suna kawar da kansu ga irin wannan lalata!—Littafin Firistoci 19:29; Maimaitawar Shari’a 5:18; 23:17.
9, 10. Isra’ilawa suna da alhakin ƙeta wace Dokar Allah, kuma wane kamanci muke gani a yau?
9 Da yake magana game da wasu zunubansu, Jehovah ya ce: “A duk wuraren sujadarsu sukan kwanta a bisa tufafin da suka karɓe jingina. A cikin Haikalin Allahnsu, sukan sha ruwan inabi da suka karɓo daga wurin wanda suke bi bashi.” (Amos 2:8) Hakika, firistocin da kuma dukan mutanen sun yi watsi da dokar da take rubuce a Fitowa 22:26, 27, da ta ce rigar da aka yi jingina da ita ya kamata a mayar kafin faɗuwar rana. Maimakon haka, suna amfani da ita suna shimfiɗarsu sa’ad da suke ci suke sha ga allolin ƙarya. Kuɗin tara da suka karɓa daga matalauta, da su suke sayan ruwan inabi su sha a bukukuwansu na addinin ƙarya. Dubi yadda suka bijire daga bauta mai tsarki!
10 Isra’ilawa da rashin kunya suna ƙeta manyan dokoki biyu na Dokar—su ƙaunaci Jehovah da kuma sauran mutane. Domin wannan Jehovah ya aiki Amos ya la’anci rashin amincinsu. A yau, ƙasashen duniya, har ma da na Kiristendam suna nuna irin yanayin lalata na Isra’ila ta dā. Ko da wasu suna yin arziki, da yawa suna rashin kuɗi da ciwon sosuwar zuciya domin ayyukan lalata na shugabanni marasa gaskiya na manyan ma’aikatu, na siyasa, da kuma na addinin ƙarya. Amma, Jehovah yana damuwa da waɗanda suke wahala kuma suka motsa su neme shi. Saboda haka, ya ba wa bayinsa na zamanin nan su yi aiki irin na Amos—su yi wa’azin Kalmarsa da gaba gaɗi.
11. Menene za mu iya koya daga misalin Amos?
11 Saboda kamani da ke tsakanin aikin Amos da namu, za mu amfana ƙwarai daga bincika misalinsa. Hakika, Amos ya nuna mana na (1) abin da ya kamata mu yi wa’azinsa, na (2) yadda za mu yi wa’azin, da kuma (3) dalilin da ya sa babu wani ɗan hamayya da zai iya hana aikin wa’azinmu. Bari mu bincika waɗannan abubuwa bi da bi.
Yadda Za Mu Yi Koyi da Amos
12, 13. Ta yaya Jehovah ya nuna cewa bai ji daɗin Isra’ilawa ba, kuma yaya suka amsa hakan?
12 Mu Shaidun Jehovah, hidimarmu ta Kirista ta dangana ne a kan wa’azin Mulkin da kuma almajirantarwa. (Matiyu 28:19, 20; Markus 13:10) Duk da haka, muna kuma wa’azi game da gargaɗin Allah, kamar yadda Amos ya yi shelar cewa Jehovah zai hukunta miyagu. Alal misali, Amos 4:6-11 sun nuna cewa Jehovah ya yi ta nuna rashin jin daɗinsa ga Isra’ila. Ya sa mutanen rashin “abinci,” ya “hana [musu] ruwan sama,” ya buge su da “darɓa, da domana,” kuma ya aika musu “annoba.” Waɗannan abubuwan sun sa Isra’ila ta tuba ne? “Ba ku komo wurina ba,” in ji Allah. Hakika, Isra’ilawa sun ƙi Jehovah sau da yawa.
13 Jehovah ya yi horo ga Isra’ilawa da suka ƙi tuba. Amma, da farko, an yi musu gargaɗi na annabci. Daidai da wannan, Allah ya sanar: “Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, sai da sanin bayinsa annabawa.” (Amos 3:7) Allah ya sanar da Nuhu game da Rigyawa mai zuwa kuma ya gaya masa ya yi gargaɗi. Haka ma Jehovah ya gaya wa Amos ya yi gargaɗi na ƙarshe. Abin baƙin ciki, Isra’ila suka yi banza da saƙon Allah kuma suka ƙi aikata abin da ya dace.
14. Waɗanne kamani ne ke tsakanin zamanin Amos da zamaninmu?
14 Babu shakka za ka yarda da cewa akwai kamani tsakanin zamanin Amos da namu. Yesu Kristi ya yi annabce-annabce game da bala’i mai yawa da za su auku a lokaci na ƙarshe. Ya kuma yi annabcin aikin wa’azi na dukan duniya. (Matiyu 24:3-14) Kamar yadda ya faru a zamanin Amos, yawancin mutane a yau sun yi watsi da alamar lokatan da muke ciki da kuma saƙon Mulki. Ga irin waɗannan mutanen, sakamakon zai zama kamar na Isra’ilawa da suka ƙi su tuba. Jehovah ya yi musu gargaɗi: “Sai ku yi shirin zuwa gaban Ubangiji.” (Amos 4:12) Sun je gaban Allah sa’ad da Assuriya suka ci su a yaƙi. A yau, wannan duniya marar ibada za ta ‘gaban Allah’ a Armageddon. (Wahayin Yahaya 16:14, 16) Saboda haka, sa’ad da Jehovah ya ci gaba da haƙuri, muna masu ariritar mutane duk iyaka yadda suka kai: “Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira.”—Amos 5:6.
Fuskantar Hamayya Yadda Amos Ya Yi
15-17. (a) Wanene Amaziya, kuma ta yaya ya mai da martani ga annabcin Amos? (b) Wane zargi Amaziya ya yi wa Amos?
15 Za mu iya yin koyi da Amos a abin da ya yi wa’azinsa da kuma yadda ya yi wa’azin. An nanata wannan a sura ta 7, inda aka gaya mana game da firist da aka ambata a farkon tattaunawarmu. “Amaziya, [ne] firist, na Betel.” (Amos 7:10) Betel cibiya ce ta addinin ’yan ridda na Isra’ila, da suke bauta wa maraƙi. Saboda haka, Amaziya firist ne na addinin Ƙasar. Menene ya yi game da shelar Amos na gaba gaɗi?
16 Amaziya ya gaya wa Amos: “Kai maƙaryaci ne na ainihi! Koma ƙasar Yahuza ka nemi abin zaman gari, ka yi ta annabcinka a can. Amma a nan Betel kada ka ƙara yin annabci. Nan wurin yin sujada na sarki ne, haikali ne na al’ummai.” (Amos 7:12, 13) Ta haka, Amaziya cewa yake: ‘Je ka gida! Muna da namu addini.’ Ya yi ƙoƙarin kuma ya sa gwamnati ta hana ayyukan Amos, ya gaya wa Sarkin Yarobowam na II: “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a cikin jama’ar Isra’ila.” (Amos 7:10) Hakika, Amaziya ya zargi Amos da cin amana! Ya gaya wa sarki cewa: “Abin da [Amos] ya faɗa ke nan, za a kashe Yarobowam a bakin dāga, a sa jama’ar Isra’ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.”—Amos 7:11.
17 A waɗannan furcin, Amaziya ya yi ƙarairayi uku. Ya ce: “Abin da [Amos] ya faɗa ke nan.” Amma Amos bai taɓa da’awar cewa shi ne tushen annabcin ba. Maimakon haka, koyaushe sai ya ce: “Ubangiji ya ce.” (Amos 1:3) An kuma zargi Amos wai shi ya ce: “Za a kashe Yarobowam a bakin dāga.” Amma, kamar yadda yake rubuce a Amos 7:9, Amos ya yi annabci cewa: “Zan [Jehovah] fāɗa wa zuriyar sarki Yerobowam da yaƙi.” Allah ya annabta wannan bala’i ne ga “zuriyar” Yerobowam. Ban da haka ma, Amaziya ya zargi Amos cewa ya ce: ‘Lalle a sa jama’ar Isra’ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ Amma Amos ya annabta cewa dukan Isra’ilawa da sun komo wurin Allah za su sami albarka. A bayyane yake cewa Amaziya bai faɗi gaskiya ba domin ya samu ya sa doka ta hana aikin wa’azi na Amos.
18. Waɗanne kamani ne yake tsakanin hanyoyin da Amaziya ya yi amfani da su da kuma waɗanda shugabannin addinai suke amfani da su a yau?
18 Ka lura da kamani da ke tsakanin hanyoyi da Amaziya ya yi amfani da su da na waɗanda suke adawa da mutanen Jehovah a yau suke amfani da su? Kamar yadda Amaziya ya yi ƙoƙari ƙwarai domin ya hana Amos, haka ma wasu firistoci, limamai, da ubanni na zamaninmu suke ƙoƙarin su hana aikin wa’azi na bayin Jehovah. Amaziya ya zargi Amos da cin amana. A yau, wasu limamai ma suna zargin Shaidun Jehovah cewa masu ta da zaune tsaya ne a ƙasa. Kamar yadda Amaziya ya nemi taimakon sarki domin ya yaƙi Amos, haka ma limamai sukan juya ga abokansu a siyasa su taimake su wajen tsananta wa Shaidun Jehovah.
’Yan Hamayya Ba Za Su Hana Aikinmu na Wa’azi Ba
19, 20. Yaya Amos ya mai da martani ga hamayyar Amaziya?
19 Ta yaya Amos ya mai da martani ga hamayyar Amaziya? Da farko, Amos ya tambayi firist ɗin: “Ka ce mini in daina yin annabci gāba da jama’ar Isra’ila?” Ba tare da jinkiri ba, annabin Allah mai gaba gaɗi ya ci gaba da faɗan kalmomin da Amaziya ba ya son ji. (Amos 7:16, 17) Amos bai razana ba. Lallai misali ne mai kyau dominmu! Idan ya zo ga yin maganar Allah, ba za mu ƙi biyayya ga Allah ba, har a ƙasashe da ake da irin mutane kamar Amaziya da suke ta da mugun tsanantawa. Kamar Amos, za mu ci gaba da yin wannan shelar: ‘Abin da Allah ya ce ke nan.’ ’Yan hamayya ba za su hana aikinmu na wa’azi ba, domin “Ubangiji kuwa yana tare” da mu.—Ayyukan Manzanni 11:19-21.
20 Ai da ya kamata Amaziya ya sani cewa burgarsa za ta kasance banza. Amos ya riga ya bayyana dalilin da ya sa babu wani a duniya da zai iya hana shi magana—kuma wannan ne batu na uku da za mu bincika. A Amos 3:3-8, Amos ya yi jerin tambayoyi da kwatanci ya nuna cewa ruwa ba ya tsami a banza. Sai ya yi wannan bayani: “Zaki ya yi ruri! Wa ba zai ji tsoro ba? Sa’ad da Ubangiji ya yi magana! Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?” A wata hanya, Amos ya gaya wa masu sauraronsa ne cewa: ‘Yadda ba za ka tsaya ba idan ka ji rurin zaki, haka ma ba zan iya ƙin yin wa’azin maganar Allah ba sa’ad da na ji Jehovah ya ba da umurnin a yi hakan.’ Tsoron Allah, ko kuma darajar Jehovah ya motsa Amos ya yi magana da gaba gaɗi.
21. Ta yaya muke amsa umurnin Allah mu yi wa’azin bishara?
21 Mu ma mun ji aikar Jehovah mu je mu yi wa’azi. To, yaya muke ji? Kamar Amos da kuma mabiyan Yesu na farko, da taimakon Jehovah za mu yi maganarsa da gaba gaɗi. (Ayyukan Manzanni 4:23-31) Babu tsanani da ’yan hamayya za su yi ko kuma rashin so na waɗanda muke musu wa’azi da zai sa mu yi tsit. Kasancewa da himma irin na Amos, Shaidun Jehovah a dukan duniya sun motsa su ci gaba da yin shelar bishara da gaba gaɗi. Hakkinmu ne mu yi wa mutane gargaɗi game da hukuncin Jehovah mai zuwa. Me wannan hukuncin ya ƙunsa? Za a amsa wannan tambayar a talifi mai zuwa.
Yaya Za Ka Amsa?
• A wane irin yanayi ne Amos ya cika aiki da Allah ya ba shi?
• Kamar Amos, me ya kamata mu yi wa’azinsa?
• Da wane irin hali ya kamata mu yi aikinmu na wa’azi?
• Me ya sa ’yan hamayya ba su iya hana aikinmu na wa’azi ba?
[Hoto a shafi na 8]
Allah ya zaɓi Amos, mai lura da ɓaure, ya yi aikinsa
[Hotuna a shafi na 11]
Kamar Amos, kana shelar saƙon Jehovah da gaba gaɗi kuwa?