“Ka Yi Tafiya Cikin Ratar Ƙasar”
“Ka yi tafiya cikin ratar ƙasar da fāɗinta.”—FARAWA 13:17.
1. Wane umurni mai ban sha’awa ne Allah ya ba Ibrahim?
AAL’ADU da yawa, mutane suna jin daɗin zuwa ƙauye a ƙarshen mako, wataƙila a cikin mota. Wasu kuma sun fi son hawa keke domin su motsa jikinsu kuma su sha kallo. Duk da haka, akwai waɗanda suka fi son tafiya a ƙasa domin su san wurare da kyau. Irin waɗannan tafiye-tafiye suna da iyaka. Amma ka yi tunanin yadda Ibrahim ya ji sa’ad da Allah ya ce masa: “Tashi, ka yi tafiya cikin ratar ƙasar da fāɗinta, gama zan baka ita”!—Farawa 13:17.
2. Ina Ibrahim ya tafi bayan ya bar Masar?
2 Ka yi la’akari da yanayin kalaman nan. Ibrahim ya zauna a Masar da matarsa da kuma wasu. Farawa sura 13 ta gaya mana cewa sun bar Masar su da tumakinsu “zuwa Negeb.” Daga nan Ibrahim “ya yi ta tafiya daga Negeb zuwa Betel.” Sa’ad da rigima ta taso tsakanin masu yi masa kiwo da na ɗan wansa Lutu, sai ya zama dole kowannensu ya nemi yankin kiwonsa, da yardar rai Ibrahim ya bai wa Lutu zaɓi na farko. Lutu ya zaɓi “kwarin Urdun” kwari mai ni’ima “sai ka ce gonar Ubangiji,” kuma daga baya ya zauna a Saduma. Allah ya ce wa Ibrahim: “Daga idanunka sama, daga inda kake, ka dubi kusurwoyin nan huɗu.” Wataƙila inda Ibrahim yake tudu ne a Betel, inda zai iya ganin dukan faɗin ƙasar. Duk da haka, da sauran aiki a gaba. Allah ya gaya masa ya “yi tafiya cikin ratar ƙasar” domin ya saba da wuraren.
3. Me ya sa zana tafiyar da Ibrahim ya yi a zuciyarmu zai iya zama ƙalubale?
3 Ko yaya ne nisan tafiyar da Ibrahim ya yi kafin ya kai Hebron, babu shakka, ya fi yawancinmu sanin Ƙasar Alkawari. Ka yi tunanin wuraren da aka ambata a wannan labarin—Negeb, Betel, Kwarin Urdun, Saduma, da Hebron. Kana ƙoƙarin zana inda wuraren nan suke a zuciyarka? Mutane da yawa suna iske wannan da wuya, domin kalilan a cikin mutanen Jehovah ne suka ziyarci kuma suka yi tafiya a cikin duka kusurwoyin ƙasar da suka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, muna da dalilin sha’awar sani game da wuraren da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Me ya sa?
4, 5. (a) Ta yaya Karin Magana 18:15 take da nasaba da sani da kuma fahimtar ƙasashen Littafi Mai Tsarki? (b) Menene Zafaniya sura 2 ta kwatanta?
4 Kalmar Allah ta ce: “Mutane masu basira, a koyaushe suna da himma, a shirye kuma suke domin su koya.” (Karin Magana 18:15) Akwai abubuwa masu yawa da mutum zai iya koya, amma cikakken sani game da Jehovah Allah da kuma ayyukansa sune abubuwa mafi muhimmanci. Babu shakka, abubuwan da muka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki za su sa mu yi haka. (2 Timoti 3:16) Ka lura cewa wannan ya ƙunshi fahimi. Wanda shi ne iya sanin batu, da kuma fahimtar yadda suke da alaƙa da juna. Wannan haka yake game da wuraren da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, yawancinmu mun san inda Masar take, amma yaya muka fahimci kalamin nan cewa Ibrahim ya bar Masar “zuwa Negeb” daga baya kuma ya wuce zuwa Betel, da Hebron? Ka fahimci dangantakar da ke tsakanin waɗannan wuraren?
5 Wataƙila ka bi tsarin karatu na Littafi Mai Tsarki wanda ya haɗa da Zafaniya sura ta 2. A nan ka karanta sunayen birane, mutane, da kuma ƙasashe. A wannan surar an ambaci Ammon, Ashkelon, Ashdod, Assuriya, Ekron, Gaza, Ka’anan, Nineba, da kuma Saduma. Ka yi nasara wajen zana waɗannan wurare inda mutane suka zauna a zuciyarka, da kuma mutanen da cikar wannan annabci na Allah ya shafa?
6. Me ya sa wasu Kiristoci suka san muhimmancin taswirori? (Dubi akwati.)
6 Ɗaliban Kalmar Allah da yawa sun amfana sosai wajen duba taswirar ƙasashen Littafi Mai Tsarki. Ba wai sun yi hakan ba ne kawai domin suna sha’awar taswirori, amma sun san cewa ta yin amfani da taswirori za su ƙara fahimtar Kalmar Allah. Ganin yadda abubuwan da suka sani ke da nasaba da sauran bayanai, taswirori na iya taimakonsu wajen ƙara fahiminsu. Yayin da muke tattauna wasu misalai, kai ma za ka ƙara ƙaunar Jehovah ka kuma sami fahimi a kan labaran da ke cikin Kalmarsa.—Dubi akwati a shafi na 14.
Sanin Nisar Wuraren Zai Kyautata Fahimtarka
7, 8. (a) Wane abu mai ban mamaki ne Samson ya yi a Gaza? (b) Wane bayani ne ya sa abin da Samson ya yi ya ƙara muhimmanci? (c) Ta yaya ne koyo da fahimtar wannan labarin Samson zai iya taimaka mana?
7 Kana iya karatu game da Alƙali Samson da ke zaune a Gaza a Littafin Mahukunta 16:2. Sunan nan Gaza yakan bayyana a cikin rahoton labarai na zamani, saboda haka, wataƙila ka gane inda Samson yake, a yankin Filistiyawa kusa da gaɓar tekun Bahar Rum. [11] Ka lura da abin da Littafin Mahukunta 16:3 ta ce: “Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakar dare. Sa’an nan ya tashi ya kama ƙyauren ƙofar birnin, da madogarai biyu na ƙofar, ya tumɓuke su. Ya saɓe su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da ke a gaban Hebron.”
8 Babu shakka, ƙofofi da madogarai na wuri ƙarfafa kamar Gaza suna da girma da nauyi. Ka yi tunanin kana son ka ɗauki wannan! Samson ya ɗauke su, amma ina ya tafi da su, kuma wace irin tafiya ce ya yi? To dai, Gaza tana gaɓar teku. [15] Amma Hebron tana gabas a tudu mai hawan wajen kafa 3,000—kuma hawa ce sosai! Ba mu san ainihin wurin “dutsen da ke a gaban Hebron” ba amma, birnin mil 37 ne daga Gaza—kuma hawa ne! Sanin nisan tafiyar da Samson ya yi, ya sa za mu ɗauke shi da muhimmanci sosai, ko ba haka ba? Ka tuna dalilin da ya sa Samson ya iya yin waɗannan abubuwan—“Ruhun Ubangiji ya sauko kansa.” (Littafin Mahukunta 14:6, 19; 15:14) A yau, mu Kiristoci ba mu sa rai cewa ruhun Allah zai ba mu ƙarfi mai yawa kamar haka ba. Duk da haka, wannan ruhu mai ƙarfi zai iya ƙara fahimtarmu na zurfafan al’amura na ruhaniya ya kuma ƙarfafa zuciyarmu. (1 Korantiyawa 2:10-16; 13:8; Afisawa 3:16; Kolosiyawa 1:9, 10) Hakika, fahimtar labarin Samson zai sa mu kasance da tabbaci cewa ruhun Allah zai iya taimakon mu.
9, 10. (a) Menene nasarar da Gidiyon ya yi bisa Madayanawa ta ƙunsa? (b) Ta yaya ne fahimtarmu ta yanayin ƙasashen nan za ta sa mu ɗauke su da muhimmanci?
9 Nasarar da Gidiyon ya yi bisa Madayanawa ya taƙaita muhimmancin sanin nisan da hakan ya ƙunsa. Yawancin masu karanta Littafi Mai Tsarki sun sani cewa Alƙali Gidiyon da mayaƙansa sun ci nasara a kan rundunar haɗin gwiwa 135,000 na Madayanawa, Amalekawa, da kuma wasu da suka kafa sansani a filin Yezreyel, kusa da hawan More. [18] Mutanen Gidiyon suka busa ƙaho kuma suka fasa tuluna suka nuna jiniyoyinsu, sai suka yi kururruwa: “Takobin Ubangiji da na Gidiyon!” Wannan ya ruɗar da abokan gaba, har suka fara karkashe junansu. (Littafin Mahukunta 6:33; 7:1-22) Duk waɗannan abubuwan sun faru ne cikin dare a ɗan ƙanƙanin lokaci? Ka ci gaba da karatun surori 7 da 8 na Littafin Mahukunta. Za ka ga cewa Gidiyon ya ci gaba da wannan harin. Yawancin wuraren da aka ambata ba a san su ba a yau, shi ya sa ba za su bayyana ba a taswirori na Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, an gano isassun wurare da za su taimaka mana domin mu san abubuwan da Gidiyon ya yi.
10 Gidiyon ya bi sauran rundunar haɗin gwiwa har gaba da Beth-shittah daga nan kuma zuwa kudancin Abel-mehola kusa da Urdun. (Littafin Mahukunta 7:22-25) Labarin ya ce: ‘Gidiyon ya zo Urdun sai ya haye tare da mutum ɗari uku ɗin nan da ke tare da shi. Ko da ya ke sun gaji, duk da haka, suka yi ta runtumar magabta.’ Bayan sun haye, Isra’ilawa suka bi magabtansu zuwa kudancin Sukkot da Feniyel kusa da Yabbok, daga nan zuwa hawan da ke Yogbeha (kusa da Amman na zamani da ke Jodan). Wannan yaƙi ne tare da gudu na tsawon mil 50. Gidiyon ya kame kuma ya kashe sarakuna biyu na Madayanawa; daga bisani ya dawo garinsa, Ofra, kusa da inda aka fara yaƙin. (Littafin Mahukunta 8:4-12, 21-27) Babu shakka, abubuwan da Gidiyon ya yi sun wuce busa ƙaho, ɗaga jiniyoyi, da kururruwa na ’yan mintoci. Kuma ka yi tunanin yadda wannan ya ƙara shafan kalamin da aka yi game da mutane masu bangaskiya: “Lokaci zai ƙure mini wajen ba da labarin su Gidiyon, [da kuma sauran] suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka wajen yaƙi.” (Ibraniyawa 11:32-34) Ko da yake Kiristoci suna iya gajiya a zahiri, ba abu mai muhimmanci ba ne mu ci gaba da yin nufin Allah?—2 Korantiyawa 4:1, 16; Galatiyawa 6:9.
Yaya Mutane Suke Tunani Kuma Suke Aikatawa?
11. Wace irin tafiya ce Isra’ilawa suka yi kafin su kai Kadesh da kuma bayan haka?
11 Wasu suna iya duba taswirorin Littafi Mai Tsarki domin su nemi wurare, amma kana tsammanin cewa taswirori za su ba da fahimi ne ga tunanin mutane? Ga misalin Isra’ilawa da suka fara tafiya daga Dutsen Sinai zuwa Ƙasar Alkawari. Bayan sun yi wasu ’yan tsaye-tsaye a kan hanya, daga bisani suka kai Kadesh (ko Kadesh-barneya). [9] Maimaitawar Shari’a 1:2 ta nuna cewa wannan tafiya ce ta kwana 11, mai nisar mil 170. Daga nan ne Musa ya aika ’yan leƙen asiri 12 zuwa Ƙasar Alkawari. (Littafin Ƙidaya 10:12, 33; 11:34, 35; 12:16; 13:1-3, 25, 26) ’Yan leƙen asirin suka tafi arewacin Negeb, wataƙila sun wuce ta Beer-sheba, daga nan zuwa Hebron, kuma suka kai iyakar arewacin Ƙasar Alkawari. (Littafin Ƙidaya 13:21-24) Domin sun saurari munanan rahotanni na ’yan leƙen asirin guda goma, shi ya sa Isra’ilawa suka yi ta yin tafiya a cikin jeji har tsawon shekaru 40. (Littafin Ƙidaya 14:1-34) Menene wannan ya nuna game da bangaskiyarsu da son ransu na dogara ga Jehovah?—Maimaitawar Shari’a 1:19-33; Zabura 78:22, 32-43; Yahuza 5.
12. Menene za mu iya cewa game da bangaskiyar Isra’ilawa, kuma me ya sa wannan wani abu ne da za mu yi tunani a kai?
12 Ka yi tunanin wuraren nan. Da a ce Isra’ilawa sun ba da gaskiya kuma sun bi shawarar Joshuwa da Kaleb, da sun yi tafiya mai nisa kafin su kai Ƙasar Alkawari? Kadesh na da nisar kusan mil goma daga Beer-lahai-roi, inda Ishaku da Rifkatu suka taɓa zama. [7] Wurin nan bai kai mil 60 ba zuwa Beer-sheba, wadda ita ce gefen kudancin Ƙasar Alkawari. (Farawa 24:62; 25:11; 2 Sama’ila 3:10) Bayan sun yi tafiya daga Masar zuwa Dutsen Sinai da kuma tafiyar mil 170 zuwa Kadesh, kamar suna bakin ƙofar Ƙasar Alkawari ne. A yanayinmu, muna bakin ƙofar Aljannar da aka yi mana alkawarinta a nan duniya. Wane darasi ne za mu koya? Manzo Bulus ya haɗa yanayin Isra’ilawa da wannan gargaɗin: “Saboda haka sai mu yi himmar shiga inuwan nan, kada wani ya kasa shiga saboda irin wannan rashin biyayya.”—Ibraniyawa 3:16–4:11.
13, 14. (a) A cikin wane irin yanayi ne Gibeyonawa suka ɗauki matakin da ya dace? (b) Menene ya bayyana irin halin Gibeyonawa, kuma wane darasi ne za mu koya daga wannan?
13 Halin da ya bambanta ya bayyana daga labarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da Gibeyonawa, na dogara ga Allah wajen tafiyar da manufarsa. Bayan Joshuwa ya ja-goranci Isra’ilawa zuwa ƙetaren Kogin Urdun har cikin ƙasar da Allah ya yi wa iyalan Ibrahim alkawari, lokaci ya yi da za a kori Kan’aniyawa. (Maimaitawar Shari’a 7:1-3) Wannan ya haɗa da Gibeyonawa. Isra’ilawa sun ci Yariko da Ai kuma suka kafa sansani a kusa da Gilgal. Gibeyonawa ba sa son su mutu a matsayin la’anannun Kan’aniyawa, saboda haka, sai suka aika wakilai ga Joshuwa a Gilgal. Sun yi ƙarya cewa su ba daga yankin Kan’ana suke ba domin su ƙulla kawance da Ibraniyawa.
14 Wakilan suka ce: ‘Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka.’ (Joshuwa 9:3-9) Tufafinsu da kayan abincinsu sun nuna cewa daga nesa suke, amma Gibeyon mil 20 ne kawai daga Gilgal. [19] Domin sun gamsu, sai Joshuwa da shugabannin jama’a suka yi yarjejeniya na abuta da Gibeyon da garuruwa da ke kusa da ita. Gibeyonawa sun yi wayo ne domin su kauce wa hallaka? Akasin haka, sun nuna sha’awarsu ne na samun tagomashin Allahn Isra’ilawa. Jehovah ya amince wa Gibeyonawa su “zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin jama’a da bagaden Ubangiji,” suna kawo itace wajen bagaden hadaya. (Joshuwa 9:11-27) Gibeyonawa sun ci gaba da yin ayyuka na bayi a hidimar Jehovah da son rai. Wataƙila, wasu cikinsu suna cikin ma’aikatan haikali da suka komo daga Babila waɗanda suke hidima a cikin haikalin da aka sake ginawa. (Ezra 2:1, 2, 43-54; 8:20) Muna iya koyi da halinsu wajen ƙoƙarin kasancewa da salama da Allah mu kuma kasance a shirye mu yi ayyuka na bayi a hidimarmu.
Mu Sadaukar da Kanmu
15. Me ya sa yanayin ƙasa game da Nassosin Kirista na Helenanci yake da ban sha’awa?
15 Yanayin ƙasashen Littafi Mai Tsarki da ke cikin labaran da ke Nassosin Kirista na Helenanci, sun lissafta tafiya da hidimar Yesu da manzo Bulus. (Markus 1:38; 7:24, 31; 10:1; Luka 8:1; 13:22; 2 Korantiyawa 11:25, 26) Ka yi tunanin irin wannan tafiyar a cikin labarin da ke gaba.
16. Ta yaya ne Kiristocin da suke a Biriya suka nuna godiya wa Bulus?
16 A lokacin tafiyarsa ta biyu ta hidima (shunayyar layi da ke cikin taswira), Bulus ya iso Filibi, da ke Girka na yanzu. [33] Ya yi wa’azi a wurin, an saka shi a cikin kurkuku bayan haka aka sake shi, daga nan ya tafi Tasalonika. (Ayyukan Manzanni 16:6–17:1) Sa’ad da Yahudawa suka ta da rigima, ’yan’uwa da ke Tasalonika suka shawarci Bulus ya tafi Biriya, wadda tafiyar mil 40 ce. Bulus ya sami nasara a hidimarsa a Biriya, amma Yahudawa suka zo suka zuga jama’ar. Saboda haka, “nan da nan kuwa ’yan’uwa suka tura Bulus bakin bahar,” kuma “waɗanda suka rako Bulus kuwa, sai da suka kai shi har Atina.” (Ayyukan Manzanni 17:5-15) Saboda haka, wasu sababbin da suka tuba suka yi tafiyar mil 25 zuwa Tekun Aegean da yardan rai, suka biya kuɗin jirgin ruwa, kuma suka yi tafiyar kusan mil 300. Ko da yake irin wannan tafiyar tana da haɗari, amma ’yan’uwan suka yi kasada, da haka suka ƙara ɓad da lokaci da wannan wakilin Allah mai ziyara.
17. Me za mu gane sa’ad da muka fahimci nisar da ke tsakanin Militas da Afisus?
17 A tafiyarsa ta uku (koriyar layi a taswira), Bulus ya iso tashar jirgin ruwa da ke Militas. Ya aika wa dattawan ikilisiyar Afisus da ke da nisar mil 30, cewa su zo. Ka yi tunanin yadda dattawan suka bar wasu ayyuka domin su je wurin Bulus. Yayin da suke tafiya, wataƙila suna ta magana cikin farin ciki game da taron da za su. Bayan sun sadu da Bulus kuma suka yi addu’a tare, “sai duk suka fashe da kuka, suka rungume Bulus, suna ta sumbantarsa.” Bayan haka, “suka rako shi har bakin jirgi” domin ya tafi Urushalima. (Ayyukan Manzanni 20:14-38) Suna da abubuwa da yawa da za su tattauna yayin da suke komawa Afisus. Ƙauna da daraja da suka nuna na tafiya mai nisa da suka yi domin su kasance da mai hidima mai ziyara wanda zai iya koyar da su ya kuma ƙarfafa su, bai burge ka ba? Akwai abubuwan da ka gani a cikin wannan labarin da za ka iya amfani da su a cikin rayuwarka da tunaninka?
Ka Koya Game da Wannan Ƙasar da Kuma Abin da ke Gaba
18. Menene ya kamata mu ƙuduri aniyyar yi game da wuraren ƙasashen da ke cikin Littafi Mai Tsarki?
18 Misalai da aka ambata a baya sun nuna amfanin da ya sa ya kamata a san ƙasashen da Allah ya ba Isra’ilawa kuma wannan abu ne mai muhimmanci a cikin labaran Littafi Mai Tsarki. (Kuma muna iya faɗaɗa fahimtarmu ta haɗa da koya game da ƙasashen da aka ambata a cikin labaran Littafi Mai Tsarki.) Yayin da muka daɗa koyo da fahimtar musamman Ƙasar Alkawari, za mu tuna abin da ake bukata daga Isra’ilawa domin su shiga kuma su more ƙasa “mai yalwar abinci.” Wadda ita ce su ji tsoron Jehovah su kuma kiyaye dokokinsa.—Maimaitawar Shari’a 6:1, 2; 27:3.
19. Waɗanne aljanna guda biyu ne ya kamata mu mai da hankali a kansu?
19 Haka nan ma a yau, muna bukatar mu yi iyakacin ƙoƙarinmu, mu ji tsoron Jehovah kuma mu manne wa hanyoyinsa. Ta haka, za mu daɗa kyautatawa kuma mu kyawanta aljanna ta ruhaniya da ta kasance yanzu a ikilisiyar Kirista. Za mu ƙara ilimi na fannoninta da albarkatunta. Kuma mun san cewa akwai ƙarin albarka. Joshuwa ya ja-goranci Isra’ilawa suka ƙetare Urdun zuwa ƙasa mai kyau. Yanzu muna da dalili mai kyau mu saurari Aljanna ta zahiri da tabbaci da ke nan gaba da mu.
Ka Tuna?
• Me ya sa ya kamata mu yi sha’awar faɗaɗa koyo da fahimtarmu game da ƙasashen Littafi Mai Tsarki?
• Wane wurin zama na zahiri da aka tattauna cikin wannan talifin ne ya wayar maka da kai?
• Wane darasi ne ka koya game da yanayin ƙasa na wasu wurare?
[Box/Hoto a shafi na 14]
“Ga Wannan Kyakkyawar Ƙasa”
A taron guduma ta shekarar 2003 da 2004, da farin ciki Shaidun Jehovah sun karɓi mujallar nan “See the Good Land.” Wannan sabuwar mujallar da akwai ta a kusan harsuna 80, tana cike da taswirori da jadawali masu kala da suka nuna yankunan duniya da aka tattauna a cikin Littafi Mai Tsarki, musamman ma Ƙasar Alkawari.
Talifin da ke baya ya yi nuni ga wasu taswirori ta wajen sa lambar shafofi da ke cikin manyan baƙaƙe, kamar [15]. Idan kana da wannan sabuwar mujallar, ka ba da lokaci sosai domin ka saba da fannoninta da za su taimaka maka ka ƙara saninka da fahimtar Kalmar Allah.
(1) Yawancin taswirorin suna da rubutu da ke ƙarƙashin hotuna ko akwati da suke bayyana alamun da ke cikin taswirar [18]. (2) Yawancin taswirorin suna da jadawali da aka zana miloli da kilomitoci da za su taimaka maka ka fahimci girma da nisar wuraren [26]. (3) Akwai kibiya da ta fuskanci arewa, wadda za ta taimaka maka ka fahimci inda take juyawa [19]. (4) Sau da yawa taswirorin suna da kala da za ta kwatanta duka tuddan [12]. (5) Wataƙila taswirar tana da baƙaƙe ko lambobi a gefe da za su taimaka maka ka ga hanyoyin da za ka yi amfani da su ka gane biranen ko sunayen [23]. (6) A fihirisa mai shafi biyu na sunayen wurare [34-35], za ka iya ganin lambar shafuffuka a cikin manyan baƙaƙe, sau da yawa tana nuna inda hanya take, kamar E2. Bayan ka yi amfani da waɗannan fannonin na ɗan lokaci, za ka yi mamakin ganin cewa suna taimakawa wajen faɗaɗa saninka da zurfafa fahimtarka na Littafi Mai Tsarki.
[Chart.Taswira a shafi nas 16, 17]
JADAWALIN YANKUNA
A. Gaɓar Bahar Rum
B. Filayen Yammacin Urdun
1. Filin Ashiru
2. Gaɓar Zirin Dor
3. Wuraren Kiwo na Sharon
4. Filin Filistiya
5. Kwarin Tsakiya na Gabas Maso Yamma
a. Filin Magiddo
b. Kwarin Yezreyel
C. Duwatsun Yammacin Urdun
1. Tuddan Galili
2. Tuddan Kamel
3. Tuddan Samariya
4. Shefela (Ƙananan Tuddai)
5. Ƙasar da Take Tudu na Yahuza
6. Jejin Yahuza
7. Negeb
8. Jejin Faran
D. Arabah (Kwari)
1. Tafkin Hula
2. Wuraren Tekun Galili
3. Kwarin Urdun
4. Tekun Gishiri
5. Arabah (kudancin Tekun Gishiri)
E. Duwatsun/Filin Gabashin Urdun
1. Bashan
2. Gileyad
3. Ammon da Mowab
4. Filayen Dutsen Edom
F. Duwatsun Lebanon
[Map]
Dutsen Harmon
Moriya
Abel-mehola
Sukkot
Yogbeha
Betel
Gilgal
Gibeyon
Urushalima
Hebron
Gaza
Biyer-sheba
Saduma?
Kadesh
[Map/Hoto a shafi na 15]
KA’ANAN
Magiddo
GILEYAD
Dothan
Shekem
Betel (Luz)
Ai
Urushalima (Salem)
Bai’talahmi (Efrata)
Mamre
Hebron (Macfela)
Gerar
Biyar-sheba
Saduma?
NEGEB
Rehobot
[Mountains]
Moriya
[Bodies of water]
Tekun Gishiri
[Rivers]
Urdun
[Picture]
Ibrahim ya kewaye ƙasar
[Taswira a shafi na 18]
Taruwasa
SAMUTARAKI
Niyabolis
Filibi
Amfibolis
Tasalonika
Biriya
Atina
Koranti
Afisus
Militas
RODUSA