Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 10/1 p. 32
  • Kana ‘Tsayayya da Ƙaimi’ Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana ‘Tsayayya da Ƙaimi’ Ne?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 10/1 p. 32

Kana ‘Tsayayya da Ƙaimi’ Ne?

ALOKATAN Littafi Mai Tsarki, ana amfani da ƙaimi—doguwar sanda da take da tsini a kai—domin korar dabbobin noma. Idan dabbar ta yi tsayayya da ja-gorar ƙaimin tana turawa, me zai faru? Maimakon ta sami sakewa, za ta jawo rauni ne wa kanta.

Yesu Kristi da aka ta da daga matattu ya yi zancen ƙaimi sa’ad da ya bayyana ga mutumin da ake kira Shawulu da yake hanyar zuwa ya tsare wasu cikin almajiran Yesu. Daga cikin haske mai haskakawar, Shawulu ya ji Yesu ya ce: “Shawulu, Shawulu, don me ka ke tsanantata? Da wuya ne gareka ka yi harbi a [ƙaimi].” Ta tsananta wa Kiristoci, Shawulu yana faɗā ne da Allah, yana bin tafarki da zai jawo masa rauni.—Ayukan Manzanni 26:14.

Mu ma ba tare da saninmu ba muna ‘harba ƙaimi’ ne? Littafi Mai Tsarki ya kamanta “kalmomi masu-hikima” da ƙaimi na ja-gora. (Mai-Wa’azi 12:11) Huraren gargaɗi na Kalmar Allah na motsa mu kuma na yi mana ja-gora daidai—idan mun yarda masa. (2 Timothawus 3:16) Idan muka ƙi ta, za mu sha rauni ne kawai.

Shawulu ya saurari kalmomin Yesu ya canja tafarkinsa, ya zama ƙaunataccen Kirista manzo Bulus. Idan mun bi gargaɗin Allah ma zai kawo mana madawwamin albarka.—Misalai 3:1-6.

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 32]

L. Chapons/Illustrirte Familien-Bibel nach der deutschen Uebersetzung Dr. Martin Luthers

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba