Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 10/1 p. 30
  • “Wannan Abin Wayar da Kai Ne!”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Wannan Abin Wayar da Kai Ne!”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Makamantan Littattafai
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Iyaye Ku Kāre Kyautarku Mai Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Tabbatacciyar Shawara Domin Renon Yara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 10/1 p. 30

Rahoto Daga Masu Shelar Mulki

“Wannan Abin Wayar da Kai Ne!”

DOROTA, mai hidima ce ta cikakken lokaci, Mashaidiyar Jehovah a ƙasar Poland, ta bi ɗanta ɗan shekara 14 zuwa bincike a asibiti da ke makarantarsu. Da ake bincika yaron, likitar Janinaa ta tambayi Dorota game da irin aikin da ɗanta yake yi a gida.

“Sa’ad da na gaji, ɗana yakan dafa abinci wa dukanmu shida a iyalin,” in ji Dorota. “Yana kuma sharan gida ya yi wasu gyare-gyare kewaye da gidan. Yana son yin karatu. Ɗalibi ne mai ƙwazo.”

“Tabɗi,” in ji Janina. “Na yi aiki a nan yanzu na shekara 12, amma ban taɓa jin wani abu haka ba.”

Da ta fahimta wannan zarafi ne na yin wa’azi, Dorota ta yi bayani: “Iyaye da yawa a yau ba sa yin renon yara yadda ya dace. Shi ya sa yaransu ba su da mutuncin kansu.”

“Yaya kika san dukan wannan?” in ji Janina. “Yawancin iyaye ba su san waɗannan abubuwa ba.”

“Littafi Mai Tsarki tushe mai tamani ne da za a samu irin wannan bayanin,” in ji amsar Dorota. “Alal misali, abin da ke a Kubawar Shari’a 6:6-9 ta nuna cewa koyar da yaranmu tana soma da koyar da kanmu ne. Bai kamata mu sahinta a zuciyarmu da azancinmu abubuwa masu kyau masu daraja da muke son mu koya wa yaranmu ba ne?”

“Tabɗi, tabɗi!” in ji Janina. Sai ta tambayi Dorota yadda Littafi Mai Tsarki ya taimake ta a reno da kuma koyar da yaranta.

“Muna nazarin Littafi Mai Tsarki kowanne mako da yaranmu,” in ji Dorota. “Muna amfani da littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work.”b Sai ta kwatanta littafin kuma ta ambata wasu darussa da ke ciki.

“Wannan abin wayar da kai ne!” in ji Janina. “Zan iya ganin littafin?”

Bayan awa guda, Dorota ta kawo littafin.

“Wane addini kike bi?” Janina tana tambaya sa’ad da take dudduba littafin.

“Ni Mashaidiyar Jehovah ce.”

“Yaya Shaidun Jehovah suke bi da waɗanda ba sa bin imaninsu?”

“Kamar yadda nike bi da ke da daraja,” in ji Dorota, ta daɗa cewa: “Hakika, muna fatan za su san gaskiyar Littafi Mai Tsarki.”

“Na soma farin ciki yanzu ma,” in ji Janina.

A ƙarshen ziyararta, Dorota ta aririci Janina ta karanta Littafi Mai Tsarki. “Zai sa rayuwarki ta kasance da ma’ana kuma ya taimake ki a aikinki.”

“Hakika, kin motsa ni na yi haka nan,” in ji Janina.

Tare da kissa da ƙuduri, Dorota ta yi amfani da ziyararta ta yi wa likita wa’azi.—1 Bitrus 3:15.

[Hasiya]

a Ba ainihin sunanta ba ne.

b Shaidun Jehovah ne suka buga.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba