Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 8/1 p. 32
  • “Mutane Biyu Suka Ƙwanƙwasa Ƙofarmu”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Mutane Biyu Suka Ƙwanƙwasa Ƙofarmu”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 8/1 p. 32

“Mutane Biyu Suka Ƙwanƙwasa Ƙofarmu”

“SHEKARA biyu ke nan tun da muke baƙin ciki domin rashin ’yarmu.” Yadda wata wasiƙa ta soma ke nan da aka buga cikin wata jaridar Le Progrès, a Saint-Étienne, Faransa.

“Mélissa wata uku ce kawai kuma ta wahala daga ciwon da ake kira trisomy 18. Ba a iya samun warkewa ta sarai daga irin wannan bala’in ciwon. Ko da yake an yi renonmu cikin imanin Katolikawa, kullum muna ta damuwa cewa ‘Allah, idan ka wanzu, me ya sa ka ƙyale irin abubuwan nan su faru?’ ” A bayyane yake cewa uwar da ta rubuta wannan wasiƙar tana baƙin ciki kuma ba ta samun taimako. Wasiƙarta ta ci gaba:

“Bai daɗe ba da wannan abin ya auku, mutane biyu suka ƙwanƙwasa ƙofarmu. Nan da nan na gane su Shaidun Jehovah ne. Na shirya cewa da wayo zan kore su, amma sai na lura da wata mujallar da suke rarrabawa. Game da dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala ne. Sai na shawarta na yarda su shiga domin in ƙaryata abin da za su ce. Ra’ayina shi ne cewa a batun wahala, iyalita ta sha isashen wahala, kuma mun gaji da jin ‘Allah ya ba mu ita, kuma Allah ya ɗauke ta.’ Shaidun suka zauna har fiye da awa guda. Suka saurare ni da juyayi mai yawa, kuma sa’ad da suke tafiya, na sami wartsakewa ƙwarai da na yarda su sake ziyara na. Shekara biyu ke nan ta shige. Ban zama Mashaidiya ba, amma na soma nazarin Littafi Mai Tsarki tare da su, kuma ina halartan taronsu yadda na iya.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba