Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 8/1 p. 30
  • Sakamako na Farin Ciki na Haƙuri da Naciya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sakamako na Farin Ciki na Haƙuri da Naciya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 8/1 p. 30

Rahoto Daga Masu Shelar Mulki

Sakamako na Farin Ciki na Haƙuri da Naciya

YESU KRISTI ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe “ƙaunar yawancin mutane za ta yi sanyi.” Domin haka, a ɓangarorin duniya da yawa a yau, mutane galibi ba sa son bisharar Mulki. Har ma wasu suna ƙyamar addini.—Matta 24:12, 14.

Duk da haka, tare da bangaskiya da haƙuri, masu shelar Mulki suna nasara a ƙalubalen, yadda labari na gaba daga Jamhuriyar Czech ya nuna.

Shaidu biyu suna magana da wata mata da take bayan ƙofa a ƙulle. Bayan ɗan lokaci, matar ta ɗan buɗe ƙofar, ta fito da hannunta ta karɓi jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! da Shaidun suke rarrabawa. Daga ciki ta ce “na gode,” sai ta rufe ƙofa. Shaidun suka yi tunani, “Mu komo ne?” Ɗaya cikinsu da majagaba ce, ko kuma mai hidima ta cikakken lokaci, ta shawarta ta koma, amma irin wannan abu ya sake faruwa, kuma haka wannan ya ci gaba na shekara guda.

Bayan da ta yi tunani ta canja yadda take magana, majagabar ta yi addu’a ga Jehovah domin taimako. A wani lokaci kuma da ta ba wa matar jaridu ta yi wa matar tambayoyi irin ta abokai: “Kina lafiya? Kin ji daɗin jaridun kuwa?” Da farko, ba ta amsa ba, amma bayan Mashaidiyar ta yi ta ziyararta, sai matar ta ɗan fara magana. Wani lokaci ta buɗe ƙofa da faɗi, amma gajeren taɗi suka yi.

Domin yadda matar ba ta magana a ƙofa, majagaban ta rubuta mata wasiƙa ta bayyana dalilin ziyarar kuma yi mata gayyar nazarin Littafi Mai Tsarki a gida. A ƙarshe, bayan shekara guda da rabi na haƙuri, majagaban ta yi nasarar soma nazarin Littafi Mai Tsarki da matar. Ta yi mamaki amma ta samu ƙarfafa da matar daga baya ta gaya mata cewa: “Na yi imani da Allah tun lokacin da kika soma kawo mini jaridu.”

Hakika kuwa, haƙuri da naciya na kawo sakamako na farin ciki a aikin wa’azin Mulki da kuma na almajirantarwa.—Matta 28:19, 20.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba