“Ga Shi, Wannan Allahnmu Ne”
Abin da aka tattauna cikin waɗannan talifofin nazari biyu daga littafin nan Ka Kusaci Jehovah ne, wanda aka fito da shi a taron gunduma da aka yi a dukan duniya a shekara ta 2002/2003.
“Ga shi, wannan Allahnmu ne; mun jirace shi, za ya cece mu: Ubangiji ne wannan.”—ISHAYA 25:9.
1, 2. (a) Menene Jehovah ya kira uban iyali Ibrahim, kuma me wannan zai iya sa mu yi mamakinsa? (b) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da mu cewa ana iya yin dangantaka ta kurkusa da Allah?
“AMININA.” Yadda Jehovah, Mahaliccin sama da ƙasa ya kira uban iyali, Ibrahim ke nan. (Ishaya 41:8) Ka yi tunani—bil adama na more abuta da Ubangiji Mamallakin sararin halitta! Kana iya mamaki, ‘Zai yiwu kuwa gare ni na matsa kusa da Allah?’
2 Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da mu cewa samun dangantaka ta kurkusa da Allah zai yiwu. Ibrahim ya sami zarafin irin wannan matsa kurkusa domin ya “gaskata Allah.” (Yaƙub 2:23) A yau ma, “asirin [Jehovah] yana tare da masu-adalci.” (Misalai 3:32) A Yaƙub 4:8, Littafi Mai Tsarki ya aririce mu: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.” A bayyane yake, idan muka ɗauki mataki mu matsa kusa da Jehovah, shi ma zai kusace mu. Hakika, za ya matso kusa da mu. Amma shin waɗannan hurarrun kalmomi na nufin cewa—mu masu zunubi, mutane ajizai ne—za mu fara ɗaukan mataki? Sam. Dangantaka da Jehovah yana yiwuwa kawai domin Allahnmu mai ƙauna ya ɗauki muhimman matakai biyu.—Zabura 25:14.
3. Waɗanne matakai biyu Jehovah ya ɗauka domin mu more abuta da shi?
3 Da farko, Jehovah ya shirya Yesu ya “bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Matta 20:28) Wannan hadayar fansa ya sa ya yiwu mu kasance kusa da Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Muna ƙauna, domin ya fara ƙaunace mu.” (1 Yohanna 4:19) Hakika, tun da Allah ne “ya fara ƙaunace mu,” shi ne ya kafa mana tushen abokantaka da shi. Na biyu, Jehovah ya bayyana mana kansa. A kowanne abokantaka da muka kafa, gamin yana bisa sanin mutumin ne da gaske, mu so shi kuma daraja halayensa na musamman. Ka yi la’akari da abin da wannan ke nufi. Da a ce Jehovah Allah a ɓoye yake, da ba a iya saninsa ba, da ba za mu taɓa zuwa kusa da shi ba. Amma, bai ɓoye kansa ba, Jehovah yana so mu san shi. (Ishaya 45:19) Ya bayyana kansa cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki a furci da za mu fahimta—tabbaci ke nan cewa ba kawai yana son mu ba amma cewa yana son mu san shi kuma mu ƙaunace shi Ubanmu na samaniya.
4. Yaya za mu ji game da Jehovah yayin da mun zo ga sanin halayensa sosai?
4 Ka taɓa ganin ɗan yaro yana nuna wa abokansa ubansa da farin ciki da kuma alfahari, “Ga babana”? Masu bauta wa Jehovah suna da dalilan jin haka game da Jehovah. Littafi Mai Tsarki ya annabta lokaci da amintattun mutane za su yi ihu: “Ga shi, wannan Allahnmu ne.” (Ishaya 25:8, 9) Da zarar ka ƙara fahimi game da halayen Jehovah, haka nan za ka ji kana da Uba mafi kyau, da kuma Aboki mafi kusa da za ka iya tunaninsa. Hakika, fahimta halayen Jehovah na ba mu dalilai na matsa kusa da shi. Saboda haka, bari mu bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana halayen Jehovah na musamman—iko, shari’a, hikima, da kuma ƙauna. Za mu tattauna guda uku cikin halayen a wannan talifin.
“Mafifici ne . . . Cikin Iko”
5. Me ya sa ya dace da Jehovah ne kaɗai aka kira “Mai-iko duka,” kuma a waɗanne hanyoyi yake amfani da ikonsa mai ban mamaki?
5 Jehovah “mafifici ne . . . cikin iko.” (Ayuba 37:23) Irmiya 10:6 ta ce: “Babu mai-kāma da kai, Ya Ubangiji: mai-girma ne kai, sunanka kuma da girma cikin iko.” Ba kamar wata halitta ba, ikon Jehovah marar iyaka ne. Domin haka ne, shi kaɗai ne ake kira “Mai-iko duka.” (Ru’ya ta Yohanna 15:3) Jehovah ya yi amfani da ikonsa mai ban mamaki ya yi halitta, ya halakar, ya kāre, kuma ya maido. Ka yi la’akari da misalai biyu kawai—ikon halitta da ikonsa na kāriya.
6, 7. Yaya ƙarfin rana yake, kuma wace muhimmiyar gaskiya ce ta tabbatar?
6 Yayin da ka tsaya a waje a cikin rana lokacin rani, yaya kake ji a jikinka? Zafin rana. To, hakika kana jin sakamakon ikon halitta na Jehovah ne. Yaya ƙarfin rana yake? A tsakiyarta, rana tana da zafin da ya kai kusan awo miliyan 27. Idan za ka iya ɗaukan ɗan mitsitsi kamar kan allura na rana ka ajiye a nan duniya, ba za ka iya tsayawa ba daga nisan mil 90 ba tare da ka yi rauni ba don wannan ɗan ƙanƙanin tushen zafi! Kowacce daƙiƙa, rana tana fid da zafi da ya yi daidai da ɗarurruwan miliyoyin bom na nukiliya. Duk da haka, duniya tana zagaya wannan tanderu a daidai inda ya dace. Idan duniya tana kusa da rana, ruwa na duniya zai zama tiriri; idan kuma duniya tana nesa zai daskare ya zama ƙanƙara. Kowanne cikin yanayi biyun ba zai sa rayuwa ta yiwu a duniya ba.
7 Ko da yake rayuwarsu ta dangana a kan rana ne, mutane da yawa ba sa ɗaukarta da muhimmanci. Saboda haka, suna banza da abin da rana za ta iya koya mana. Zabura 74:16 ta ce game da Jehovah: “Kai ne ka shirya haske da rana.” Hakika, rana tana girmama Jehovah, “mai-halittan sama da ƙasa.” (Zabura 146:6) Duk da haka, guda ce kawai cikin halittu da yawa da ke koya mana game da ikon Jehovah mai girma. Yayin da muke ƙara koyo game da ikon halitta na Jehovah, za mu ƙara jin tsoronsa.
8, 9. (a) Wace kalmar kwatanci ta nuna mana sarai yadda Jehovah yake a shirye ya kāre kuma kula da masu bauta masa? (b) Yaya makiyayi na lokatan Littafi Mai Tsarki yake kula da tumakinsa, kuma menene wannan ya koya mana game da Makiyayinmu Mai Girma?
8 Jehovah kuma yana amfani da ikonsa mai yawa domin ya kāre bayinsa kuma ya kula da su. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da wasu misalai don ya kwatanta alkawarin Jehovah na kulawa. Alal misali, ka lura da Ishaya 40:11. A wurin Jehovah ya kamanta kansa da makiyayi kuma mutanensa da tumaki. Mu karanta: “Za ya yi kiwon garkensa kamar makiyayi, za ya tattara ’ya’yan tumaki a hannunsa, ya ɗauke su a cikin ƙirjinsa, a hankali kuma za ya bida masu-bada mama.” Za ka iya ƙaga abin da aka kwatanta a ayar?
9 Dabbobi kalilan ne ba sa kāre kansu kamar tunkiya. Makiyayi a lokatan Littafi Mai Tsarki yana bukatar ya kasance da gaba gaɗi don ya kāre tumakinsa daga karnukan daji, da kuma zakuna. (1 Samu’ila 17:34-36; Yohanna 10:10-13) Amma akwai lokatai da kārewa da kuma kula da tumakin yake bukatar juyayi. Alal misali, lokacin da tunkiya ta haihu da nisa da garken, ta yaya makiyayin zai kāre ɗan rago sabon haihuwa daga haɗari? Zai ɗauke shi, ƙila ma na kwanaki, a “ƙirjinsa”—kalmasa da ke kasancewa a saman rigarsa. Ta yaya ɗan rago zai kasance a ƙirjin makiyayi? Ɗan rago zai iya zuwa wajen makiyayin har ma ya ɗan ture ƙafarsa. Amma, makiyayin ne zai durƙusa, ya kai wurin ɗan ragon, kuma ya sa shi inda zai samu kwanciyar rai a ƙirjinsa. Dubi misalin juyayi na Makiyayinmu Mai Girma da ke a shirye ya kāre kuma kula da bayinsa!
10. Wace kāriya ce Jehovah yake tanadinsa a yau, kuma me ya sa irin kāriyar nan take da muhimmanci?
10 Jehovah ya yi fiye da yin alkawarin kāriya kawai. A lokatan Littafi Mai Tsarki, ya nuna a hanyoyi na mu’ujiza cewa yana iya “ceci masu-ibada daga cikin jaraba.” (2 Bitrus 2:9) Yau kuma fa? Mun sani cewa ba ya yin amfani da ikonsa domin ya kāre mu daga dukan masifa ba a yanzu. Hakika, yana tanadin wani abu mafi muhimmanci—kāriya ta ruhaniya. Allahnmu mai ƙauna yana kāre mu daga haɗari na ruhaniya ta shirya mu da abubuwan da muke bukata don mu jimre wa gwaji kuma kāre dangantakarmu da shi. Alal misali, Luka 11:13 ta ce: “Idan ku fa da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?” Ikon nan na iya sa mu iya jimre da dukan gwaji ko kuma matsala da muke fuskanta. (2 Korinthiyawa 4:7) Saboda haka, Jehovah yana yin abubuwa don ya tsare rayukanmu, ba na shekaru kalilan kawai ba, amma na dawwama. Domin wannan zaton, za mu iya ɗaukan kowane irin wahala cikin zamanin nan na “lokaci kaɗan” ne kawai. (2 Korinthiyawa 4:17) Ba za mu matsa kusa da Allahn da yake amfani da ikonsa cikin ƙauna dominmu ba?
‘Jehovah Mai Son Shari’a Ne’
11, 12. (a) Me ya sa shari’ar Jehovah ke jawo mu kusa da shi? (b) Wace kammalawa ce Dauda ya yi game da shari’ar Jehovah, kuma ta yaya waɗannan hurarrun kalmomi ke mana ta’aziyya?
11 Jehovah yana yin abin da yake daidai kuma yana yin haka ko da yaushe, ba tare da wariya ba. Shari’a ta Allah, ba halin son kai da ke korarmu ba, amma wanda ke jawo mu ga Jehovah. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta kyan wannan hali sosai. To, bari mu yi la’akari da hanyoyi uku da Jehovah yake nuna shari’a.
12 Na farko, shari’ar Jehovah tana motsa shi ya nuna gaskiya da aminci ga bayinsa. Mai Zabura Dauda ya zo ga fahimtar wannan fannin shari’ar Jehovah. Daga abin da ya faru masa da kuma daga nazarin hanyoyin Allah, wace kammalawa Dauda ya yi? Ya sanar cewa: “Ubangiji yana son shari’a, kuma ba ya yarda tsarkakansa ba; ana kiyaye su har abada.” (Zabura 37:28) Dubi tabbaci mai ban ƙarfafa! Ko na ɗan lokaci Allahnmu ba zai yi banza da waɗanda suke aminci gare shi ba. Saboda haka, za mu iya dangana ga abokantakarsa da kuma kulawarsa ta ƙauna. Shari’arsa ta ba da tabbacin wannan!—Misalai 2:7, 8.
13. Yaya yadda Jehovah yake damuwa da tsiyayyu take bayyane cikin Dokar da ya ba wa Isra’ila?
13 Na biyu, shari’a ta Allah ba ta banza da bukatar tsiyayyu. Ana ganin tabbacin kulawar Jehovah don tsiyayyu cikin Doka da ya ba Isra’ila. Alal misali, Dokar ta yi tanadin kula da marayu da gwauraye. (Kubawar Shari’a 24:17-21) Domin ya fahimci yadda rayuwa za ta kasance da wuya ga irin iyalan nan, Jehovah kansa ya zama ubansu Alƙali da kuma Mai Kāriya. (Kubawar Shari’a 10:17, 18) Ya faɗakar da Isra’ilawa cewa idan suka wahalar da mata da yara da ba su da mai taimako, zai ji kukansu. “Fushina kuma za ya ƙuna da zafi,” yadda ya faɗa ke nan, da aka rubuta a Fitowa 22:22-24. Ko da yake fushi ba ya cikin halin Allah na musamman ba, ana sa ya yi fushi na adalci ta wajen ayyuka marasa adalci da gangan, musamman ma idan waɗanda ake zalunta musu tsiyayyu ne.—Zabura 103:6.
14. Menene ya nuna da gaske cewa Jehovah ba ya tara?
14 Na uku, a Kubawar Shari’a 10:17, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da mu cewa Jehovah “ba ya tara, ba ya kuwa karɓan rishuwa ba.” Jehovah ba kamar wasu mutane masu iko da tasiri ba, ba ya yarda wadata ko kuma ganin ido ya rinjaye shi. Ba ya wariya ko kuma nuna son kai ba. Ga tabbaci mai girma na rashin wariyarsa: Zarafi na zama masu bauta masa, da samun rai marar matuƙa a nan gaba, ba domin manya kalilan kawai ba. Maimako, Ayukan Manzanni 10:34, 35 ta ce: “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowacce al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” Wannan begen domin kowa ne ko da ina suka fito, launin jikinsu, ko kuma ƙasar da suke zama. Wannan ba shari’a ce ta gaske ba? Hakika, fahimtar shari’ar Jehovah da kyau na jawo mu kusa da shi!
“Ya Zurfin . . . Hikimar Allah”!
15. Mecece hikima, kuma ta yaya Jehovah yake nuna ta?
15 Manzo Bulus ya motsa ya ce, kamar yadda yake a Romawa 11:33: “Ya zurfin . . . hikimar Allah duk da na saninsa!” Hakika, yayin da muke tunanin fannoni dabam dabam na hikimar Jehovah mai girma, babu shakka sai mu cika da mamaki kawai. To, yaya za mu iya ba da ma’anar wannan hali? Hikima tana haɗa ilimi, basira, da kuma fahimi kuma su fito da sakamakon aikinsu. Domin fāɗin sani da zurfin fahiminsa, kullum Jehovah yana tsai da shawara mafi dacewa, yana cika su ta ayyuka da ake iya fahimtawa.
16, 17. Ta yaya halittun Jehovah suka tabbatar da hikimarsa mai yawa? Ka ba da misali.
16 Ina wasu tabbaci na musamman na girman hikimar Jehovah? Zabura 104:24 ta ce: “Ya Ubangiji, ayyukanka ina misalin yawansu! Da hikima ka yi su duka: duniya cike ta ke da wadatarka.” Babu shakka, idan muka ƙara koyo game da abubuwan da Jehovah ya halitta, haka za mu iske muna mamaki game da hikimarsa. ’Yan kimiyya sun koyi abubuwa da yawa daga nazarin halittar Jehovah! Har ma da sashen injiniyoyi da ake kira kimiyyar kwaikwayo, da take neman ta yi kwaikwayon dukan abin da suke gani a halitta.
17 Alal misali, wataƙila za ka zuba wa saƙar gizo-gizo idanu kana mamakin kyanta. Hakika abin mamaki ne na zane-zane. Wasu zare da kamar ba su da ƙarfi sun fi ƙarfe ƙarfi, sun fi ma zaren da ake rigar kāre harsashi da shi. Menene wannan yake nufi da gaske? Ka yi tunanin an faɗaɗa saƙar gizo har sai da ta kai girman taru. Irin wannan tarun yana da ƙarfi da zai iya tsayar da jirgin sama na fasinja da yake cikin gudu! Hakika, Jehovah ya yi dukan waɗannan abubuwa ‘cikin hikima.’
18. Ta yaya aka ga hikimar Jehovah a yadda ya yi amfani da mutane su rubuta Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki?
18 Tabbaci mafi girma ta hikimar Jehovah ana iya samunsa ne cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Gargaɗi na hikima da ke cikin shafofinsa sun nuna mana da gaske hanya mafi kyau ta rayuwa. (Ishaya 48:17) Amma ana ganin hikimar Jehovah da babu na biyunta a hanyar da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. Ta yaya? Cikin hikimarsa, Jehovah ya zaɓi mutane su rubuta Kalmarsa. Da ya yi amfani da mala’iku su rubuta hurarriyar Kalmarsa, da Littafi Mai Tsarki zai kasance da armashi daidai haka kuwa? Hakika, da mala’iku sun bayyana Jehovah daga iliminsu mai girma kuma ta yadda su za su yi masa ibada. Amma da mun iya fahimtar yadda halittu kamiltattu na ruhu suke, waɗanda saninsu, fasaharsu, da ƙarfinsu ya fi gaban namu?—Ibraniyawa 2:6, 7.
19. Wane misali ya nuna cewa yin amfani da marubuta mutane ya ba Littafi Mai Tsarki daɗaɗa da kuma armashi?
19 Yadda aka yi amfani da mutane su yi rubutun ya ba Littafi Mai Tsarki daɗaɗa da armashi. Marubutan, mutane ne da tabi’a kamarmu. Domin ajizai ne, sun fuskanci gwaji da matsi irin namu. A wasu yanayi, sun rubuta game da kansu, jiye-jiyensu da kuma fama. (2 Korinthiyawa 12:7-10) Saboda haka, sun rubuta abin da mala’ika ba zai rubuta ba. Alal misali, kalmomin Dauda da ke rubuce a Zabura 51. Bisa jigon, Dauda ya rubuta wannan zaburar bayan ya yi zunubi mai tsanani ne. Ya furta zuciyarsa, yana furta baƙin ciki kuma yana roƙon gafarar Allah. Ayoyi na 2 da 3 suka ce: “Ka wanke ni sarai daga kuskurena, ka tsarkake ni daga zunubina. Gama ina sane da laifofina: zunubina yana gabana tuttur.” Ka lura da aya ta 5: “Ga shi, cikin mugunta aka sifanta ni; cikin zunubi kuma uwata ta ɗauki cikina.” Aya 17 ta daɗa: “Hadayu na Allah karyayyen ruhu ne: karyayyar zuciya mai-tuba ba za ka rena ta ba, ya Allah.” Ka lura da yadda marubucin yake baƙin ciki? Wa zai iya furta wannan idan ba mutum ajizi ba?
20, 21. (a) Me ya sa za a ce ko da an yi amfani da marubuta mutane, Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi hikimar Jehovah? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
20 Ta wurin amfani da mutane ajizai, Jehovah ya yi tanadin daidai abin da ake bukata—abin da ke rubuce “hurarre daga wurin Allah” da yake ɗauke da abin da mutane za su fahimta. (2 Timothawus 3:16) Hakika, ruhu mai tsarki ne ya yi wa waɗannan marubutan ja-gora. Saboda haka, sun rubuta hikimar Jehovah, ba tasu ba. Hikimar nan matabbaciya ce kamiltacciya. Wannan ta wuce tamu hikima da Allah ya aririce mu: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” (Misalai 3:5, 6) Ta wurin bin wannan shawara mai kyau, za mu jawo kusa da Allah mai dukan hikima.
21 Hali mafi jawo mutum kuma mafi kyau cikin dukan halayen Jehovah shi ne ƙauna. Za a tattauna yadda Jehovah ya nuna ƙauna cikin talifi na gaba.
Za Ka Iya Tunawa?
• Waɗanne matakai Jehovah ya ɗauka domin ya sa abutarmu da shi ta yiwu?
• Ina wasu misalan ikon halitta na Jehovah da kuma na ikonsa na kāriya?
• A waɗanne hanyoyi ne Jehovah yake nuna shari’a?
• Ta yaya ake ganin hikimar Jehovah cikin halittunsa, da kuma cikin Littafi Mai Tsarki?
[Hoto a shafi na 22]
Kamar makiyayi da yake ɗaukan ɗan rago a ƙirjinsa, Jehovah yana kula da Tumakinsa
[Hoto a shafi na 25]
An ga hikimar Jehovah a hanyar da aka rubuta Littafi Mai Tsarki