Ka “Nuna Iyakacin Tawali’u Ga Dukan Mutane”
“Ka tuna musu su . . . kasance . . . masu-laushin hali, suna nuna iyakacin tawali’u ga dukan mutane.”—TITUS 3:1, 2.
1. Me ya sa ba shi da sauƙi a nuna tawali’u?
“KU ZAMA masu-koyi da ni” in ji manzo Bulus, “kamar yadda ni kuma na Kristi ne.” (1 Korinthiyawa 11:1) Dukan bayin Allah yau suna ƙoƙari su bi wannan gargaɗin. Hakika, yana da wuya, domin mun gāji son kai daga iyayenmu na farko da hali da bai jitu da misalin Kristi ba. (Romawa 3:23; 7:21-25) Duk da haka, idan ya kai ga nuna tawali’u, dukanmu za mu iya yin nasara idan muka yi ƙoƙari. Amma ƙoƙarin kanmu kawai ba zai isa ba. Ana bukatar fiye da haka. Me kuma ake bukata?
2. Ta yaya za mu nuna “iyakacin tawali’u ga dukan mutane”?
2 Tawali’u na Allah ɓangare ne na ’yar ruhu mai tsarki na Allah. Da zarar mun bi ja-gorar ruhun Allah, haka nan ’yar ruhun ta bayyana. Sa’an nan ne kawai za mu iya nuna “iyakacin tawali’u” ga kowa. (Titus 3:2) Bari mu bincika yadda za mu iya bin misalin Yesu domin mu sa wasu da suka sadu da mu su “sami hutawa.”—Matta 11:29; Galatiyawa 5:22, 23.
A Cikin Iyali
3. Wane yanayi na iyali ne ke nuna ruhun duniya?
3 Wajen da tawali’u ya wajaba a cikin iyali ne. Ƙungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya ta kimanta cewa nuna ƙarfi a iyali yakan sa lafiyar mata cikin haɗari fiye da haɗarin mota da kuma zazzabin cizon sauro gaba ɗayansu in an haɗa. Alal misali, a London ta Ingila, kashi ɗaya cikin huɗu na dukan ƙara da ake yi na nuna ƙarfi cikin iyali ne. ’Yan sanda sau da yawa suna haɗuwa da mutane da suke bayyana zuciyarsu ta wajen “hargowa, da zage-zage.” Mafi muni, wasu ma’aurata sun ƙyale “ɓacin rai” ya shafi nasabarsu. Wannan abin baƙin ciki ne da ke nuna “ruhun duniya” domin haka ba shi da wuri a cikin iyalin Kirista.—Afisawa 4:31; 1 Korinthiyawa 2:12.
4. Yaya tawali’u zai iya shafan iyali?
4 Domin mu tsayayya wa ra’ayoyi irin na duniya, muna bukatar ruhun Allah. “Inda Ruhun Ubangiji ya ke, nan akwai ’yanci.” (2 Korinthiyawa 3:17) Ƙauna, kirki, kame kai, da kuma tsawon jimrewa suna ƙarfafa haɗin kan maza ajizai da matansu. (Afisawa 5:33) Tawali’u yana canja yanayi na faɗa na iyalai da yawa zuwa na farin ciki. Abin da mutum ya ce yana da muhimmanci, amma yadda ya faɗe shi ne yake nuna abin da yake nufi. Damuwa da aka furta cikin tawali’u yana rage ɓacin rai. Sulemanu Sarki mai hikima ya rubuta: “Mayarda magana da taushi ya kan juyadda hasala: amma magana mai-zafi ta kan tone fushi.”—Misalai 15:1.
5. Ta yaya tawali’u zai yi taimako a iyalai da addininsu ya bambanta?
5 Tawali’u yana da muhimmanci musamman a iyalai da addininsu ya bambanta. Tare da ayyukan kirki, zai iya rinjayar waɗanda ba su da zuciyar kirki ga Jehovah. Bitrus ya yi wa mata Kirista gargaɗi: “Ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu banda magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta tare da tsoro. Kada adonku ya zama ado na waje, watau su kitson gashi, da sa ado na zinariya, ko yafa tufafi masu ƙawa; amma ya zama ɓoyayyen mutum na zuciya, cikin tufafi waɗanda ba su lalacewa, na ruhu mai-ladabi mai-lafiya, abin da ke da tamani mai-girma a gaban Allah.”—1 Bitrus 3:1-4.
6. Ta yaya nuna tawali’u zai ƙarfafa dangantaka tsakanin iyaye da ’ya’yansu?
6 Nasaba tsakanin iyaye da ’ya’yansu zai iya lalacewa, musamman ma idan babu ƙaunar Jehovah. Amma a dukan gidajen Kiristoci da bukatar a nuna tawali’u. Bulus ya yi gargaɗi ga Ubanni: “Ku ubanni kuma, kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:4) Sa’ad da tawali’u ya kasance a iyali, dangantaka tsakanin iyaye da yara sai ya ƙarfafa. Dean, ɗaya cikin yara biyar, ya tuna da babansa: “Baba yana da tawali’u. Ban taɓa musu ba ko sau ɗaya da shi—har a lokacin da nake saurayi. Yana da tawali’u ko da yaushe har a lokacin da ya yi fushi ma. Wani lokaci sai ya kore ni in koma ɗakina ko kuma ya hana wasu abubuwa, amma ba mu taɓa yin musu ba. Ba baba ba ne kawai a gare mu. Abokinmu ne, kuma ba ma so mu ba shi kunya.” Tawali’u yana taimakawa wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin iyaye da ’ya’yansu.
A Hidimarmu
7, 8. Me ya sa nuna tawali’u a hidimar fage yake da muhimmanci?
7 Wani wuri kuma da tawali’u yake da muhimmanci a hidimar fage ne. Sa’ad da muke sanar da wasu bisharar Mulki, muna saduwa da mutane da suke da zuciya iri dabam dabam. Wasu suna sauraron saƙon bege da muke kawo musu. Wasu, domin wasu dalilai za su ƙi. A nan ne halin tawali’u yake da taimako ƙwarai a gare mu mu cika wajibinmu na yin shaida har iyakan duniya.—Ayukan Manzanni 1:8; 2 Timothawus 4:5.
8 Manzo Bitrus ya rubuta: “Cikin zukatanku ku tsarkake Kristi kamar Ubangiji: kullum a shirye ku ke ku amsa ma kowane mai-tambayanku dalilin begen da ke cikinku, amma dai da ladabi da tsoro.” (1 Bitrus 3:15) Domin mun riƙe Kristi a zuciyarmu abin koyi, muna ƙoƙari mu nuna tawali’u da daraja sa’ad da muke yi wa waɗanda suke tankiya wa’azi. Wannan halin sau da yawa yana kawo sakamako mai kyau.
9, 10. Ka ba da labari da ya nuna muhimmancin tawali’u a hidimar fage.
9 Sa’ad da matarsa ta buɗe ƙofa sa’in da aka ƙwanƙwasa ƙofar, Keith yana cikin gida. Da ta gano cewa baƙonsu Mashaidin Jehovah ne, matar Keith cikin fushi ta zargi Shaidun da yi wa yara ƙeta. Ɗan’uwan ya kame kansa. Cikin tawali’u ya yi bayani: “Kai, abin bai mini daɗi ba da kike jin haka. Bari in nuna miki abubuwan da Shaidun Jehovah suka yi imani da su!” Keith yana sauraran maganarsu sai ya matso domin ya sallami ɗan’uwan.
10 Daga baya, ma’auratan suka yi nadama cewa ba su kyauta wa baƙonsu ba. Tawali’unsa ya taɓa zuciyarsu. Abin mamaki, bayan sati ɗaya ɗan’uwan ya sake dawowa, Keith da matar suka yarda ya yi bayani daga Nassosi dalilin imaninsa. Daga baya suka ce: “Cikin shekara biyu, mun saurari wasu abubuwa da yawa da wasu Shaidu suka ce. Suka yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su, kuma a ƙarshe dukansu biyu suka yi baftisma alamar keɓe kansu ga Jehovah. Wannan albarka ce ga wannan Mashaidin da ya fara zuwa wurin Keith da matarsa! Mashaidin ya sadu da ma’auratan bayan shekaru da yawa kuma ya ga cewa sun zama ’yan’uwansa a ruhaniya. Tawali’u ya yi nasara.
11. Wace hanya ce tawali’u zai iya buɗewa domin wani ya karɓi gaskiyar Kiristanci?
11 Abin da Harold ya gani a aikin soja ya sa ya yi fushi kuma yake shakkar wanzuwar Allah. Matsalar ta ƙaru, sa’ad da haɗarin mota da wani bugeggen direba ya haddasa ya sa Harold ya naƙasa. Sa’ad da Shaidun Jehovah suka ziyarci gidansa, Harold ya ce ba ya so su riƙa ziyartarsa. Amma wata rana, wani Mashaidi mai suna Bill ya shirya zai ziyarci wani mutum da yake kusa da gidan Harold. Bill ya yi kuskure ya ƙwanƙwasa ƙofar Harold. Sa’ad da Harold da yake tafiya da sanduna biyu ya buɗe ƙofa, babu ɓata lokaci Bill ya ba shi haƙuri, ya yi bayanin cewa yana so ya ziyarci wani gida ne na kusa. Menene Harold ya yi? Bill bai sani ba cewa Harold ya ga Shaidun a telibijin suna aiki tare domin su gina sabuwar Majami’ar Mulki a cikin ɗan ƙaramin lokaci. Ganin mutane da yawa suna aiki tare cikin haɗin kai ya burge shi ƙwarai, kuma wannan ya sa ya canja halinsa game da Shaidu. Haƙuri da Bill ya ba shi da kuma halinsa na tawali’u ya faranta masa rai, Harold ya yarda Shaidu su riƙa ziyartar sa. Ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki, ya sami ci gaba, ya zama bawan Jehovah wanda ya yi baftisma.
A Cikin Ikilisiya
12. Waɗanne halaye ne na duniya mutanen ikilisiya ya kamata su yi tsayayya da shi?
12 Wuri na uku da tawali’u yake da muhimmanci shi ne a ikilisiyar Kirista. Husuma aba ce ta kullum a duniya ta yau. Musu da jayayya abubuwa ne na kullum tsakanin waɗanda suke ɗaukan rayuwa a hanya ta jiki. A wani lokaci, irin waɗannan halaye suna shigowa cikin ikilisiyar Kirista kuma su bayyana cikin tashin hankali da faɗa a kan kalmomi. Yana baƙanta wa dattawa rai sa’ad da ya kasance dole su magance wannan yanayin. Duk da haka, ƙaunar Jehovah da kuma na ’yan’uwansu take motsa su su yi ƙoƙari su maido da waɗanda suka yi kuskure.—Galatiyawa 5:25, 26.
13, 14. Menene zai kasance sakamakon ‘horon masu-jayayya cikin tawali’u?’
13 A ƙarni na farko, Bulus da kuma abokinsa Timothawus sun fuskanci matsaloli daga cikin ikilisiya. Bulus ya yi wa Timothawus gargaɗi game da ’yan’uwa waɗanda suka yi kama da tukwane na ‘marasa daraja.’ “Kada bawan Ubangiji kuwa ya yi husuma,” in ji Bulus, “amma shi yi nasiha ga duka, mai-sauƙin koyarwa, mai-haƙuri cikin tawali’u yana horon masu-jayayya.” Sa’ad da muka kasance da tawali’u sa’ad da aka sa muka fusata, masu jayayya za su motsu su sake bincika sūkarsu. Jehovah kuma kamar yadda Bulus ya ci gaba da rubuta zai “ba su tuba zuwa sanin gaskiya.” (2 Timothawus 2:20, 21, 24, 25) Ka lura cewa Bulus ya haɗa nasiha da haƙuri tare da tawali’u.
14 Bulus ya yi abin da yake wa’azinsa. Sa’ad da yake bi da “mafifitan manzanni” a ikilisiya ta Koranti, ya aririci ’yan’uwan: “Ni Bulus da kaina dai bisa ga tawali’u da nasiha na Kristi ina roƙonku, ni da ni ke mai-tawali’u a cikinku sa’anda ina wurinku, amma sa’anda ina rabe da ku gaba gaɗi ni ke zuwa gareku.” (2 Korinthiyawa 10:1; 11:5) Bulus da gaske ya yi koyi da Kristi. Ka lura cewa ya roƙi waɗannan ’yan’uwa “bisa ga tawali’u” na Kristi. Saboda haka, ya guji halin fahariya, da nuna iko. Gargaɗinsa babu shakka ya faranta wa waɗanda suke da zuciyar kirki a cikin ikilisiya. Ya gyara dangantaka kuma ya shirya hanyar salama da haɗin kai a cikin ikilisiya. Wannan ba hanyar da duka ya kamata mu yi ƙoƙari mu bi ba ne? Dattawa musamman suna bukatar su bi hanyar Kristi da ta Bulus.
15. Me ya sa tawali’u yake da muhimmanci sa’ad da ake ba da gargaɗi?
15 Hakkin a taimaki wasu ba kawai sa’ad da salama da haɗin kan ikilisiya take fuskantar barazana ba ne. Kafin dangantaka ta yi tsami, ’yan’uwa suna bukatar ja-gora cikin ƙauna. “ ’Yan’uwa, ko an iske mutum a cikin kowane laifi, ku da ku ke masu-ruhaniya, . . . ku komo da irin wannan,” in ji Bulus. Ta wace hanya? “Cikin ruhun tawali’u . . . kana lura da kanka, kada ya zama kai kuma ka jarabtu.” (Galatiyawa 6:1) Kasancewa da ruhun “tawali’u” ba koyaushe ba ne yake da sauƙi, musamman ma domin dukan Kiristoci, har da maza da aka naɗa, suna fuskantar yanayi na zunubi. Duk da haka, tawali’u ne zai sa komo da wannan mai laifi da sauƙi.
16, 17. Menene zai taimaka wajen gyara wani jinkiri a bin gargaɗi?
16 A Helenanci na ainihi, kalmar da aka fassara “komo” za ta iya nufi miƙawa ko kuma haɗa ƙashi, abu ne mai zafi. Likita da zai haɗa ƙashin zai yi maganar amfanin maganin. A hanya mai ƙarfafawa. Kalmomi masu daɗi da fari za su taimaka wajen rage zafi mai tsanani. Haka nan, gyara ta ruhaniya za ta kasance da zafi. Amma tawali’u zai sa ya zama da abin karɓa, ta haka a mai da dangantaka mai kyau kuma a gyara hanya domin mai laifi ya canja hanyarsa. Ko da da farko an ƙi gargaɗi da aka bayar, tawali’u daga wurin wanda yake ba da taimako zai taimaka a gyara dukan wani jinkiri wajen bin shawara ta Nassosi.—Misalai 25:15.
17 Sa’ad da ake taimakon wasu su yi gyara, da akwai haɗarin cewa za a ɗauki gargaɗin kamar sūka ce. Wani marubuci ya ce: “Sa’ad da muke yi wa wasu gargaɗi akwai haɗarin mu kasance da iko, saboda haka, muna bukatar tawali’u.” Koyon tawali’u da ya fito daga ƙasƙantar zuciya zai taimaki Kirista mai ba da gargaɗi ya guje wa wannan haɗarin.
“Ga Dukan Mutane”
18, 19. (a) Me ya sa zai yi wa Kiristoci wuya su nuna tawali’u wajen hulɗa da masu iko na duniya? (b) Menene zai taimaki Kiristoci su kasance da tawali’u ga masu iko, kuma me ƙila zai zama sakamakon haka?
18 Inda yake yi wa mutane da yawa wuya su nuna tawali’u shi ne wajen bi da masu iko. Hakika, abin da wasu masu iko suke yi yana nuna tankiya da rashin juyayi. (Mai-Wa’azi 4:1; 8:9) Duk da haka, ƙaunarmu ga Jehovah za ta taimaka mana mu fahimci ikonsa, da kuma miƙa kai da ake bukata a wurinmu ga gwamnati. (Romawa 13:1, 4; 1 Timothawus 2:1, 2) Har a lokacin da waɗanda suke da matsayi suka nemi hanyar da za su matse hanyar furta bautarmu ga Jehovah, da farin cikin muna neman wasu hanyoyi da za mu miƙa hadayarmu ta yabo.—Ibraniyawa 13:15.
19 Babu yanayi da zai sa mu zama masu tankiya. Muna ƙoƙari mu kasance masu hankali duk da haka ba za mu yi shirka ba ga mizanan adalci. A wannan hanyar, ’yan’uwanmu sun ci gaba da yin hidimarsu a ƙasashe 234 na duniya. Muna bin gargaɗin Bulus mu “yi biyayya ga mahukunta, ga masu-iko; su ji magana, su zama shiryayyu ga kowane kyakkyawan aiki, kada su ambaci kowa da mugunta, su kasance marasa-faɗa, masu-laushin hali, suna nuna iyakacin tawali’u ga dukan mutane.”—Titus 3:1, 2.
20. Wace lada waɗanda suka nuna tawali’u za su samu?
20 Albarka mai yawa tana jiran waɗanda suke nuna tawali’u. “Masu-albarka ne masu-tawali’u,” in ji Yesu, “gama su za su gāji duniya.” (Matta 5:5) Ga ’yan’uwan Kristi shafaffu, kasancewa da tawali’u zai tabbatar musu da farin ciki da kuma gatar sarauta bisa duniya a Mulkin. “Taro mai-girma” kuma na “waɗansu tumaki,” sun ci gaba da nuna tawali’u kuma suna ci gaba da sauraron rayuwa cikin aljanna a nan duniya. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16; Zabura 37:11) Lalle bege mai ban sha’awa yana nan gaba! Saboda haka, kada mu manta gargaɗi da Bulus ya yi wa Kiristoci a Afisus: “Ni fa, ɗaurarre cikin Ubangiji, ina roƙonku ku yi tafiya irin da ta cancanci kira da aka kiraye ku da ita, da dukan tawali’u da ladabi.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; Afisawa 4:1, 2.
Domin Maimaitawa
• Wace albarka ce take zuwa daga nuna tawali’u
• a iyali?
• a hidimar fage?
• a cikin ikilisiya?
• Wace lada aka yi alkawarinta ga waɗanda suke da tawali’u?
[Hoto a shafi na 27]
Tawali’u musamman yana da muhimmanci a iyalin da addininsu ya bambanta
[Hoto a shafi na 27]
Tawali’u na ƙarfafa dangantaka ta iyali
[Hoto a shafi na 29]
Ka yi kāriya da tawali’u da kuma ladabi mai zurfi
[Hoto a shafi na 30]
Tawali’un mai ba da gargaɗi zai taimaki mai laifi