Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 3/1 pp. 3-4
  • Me Ya Sa Ake Tsananta wa Mutane Domin Addininsu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Ake Tsananta wa Mutane Domin Addininsu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ba na Duniya Ba”
  • Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Shiga Harkokin Siyasa?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Za Ka Iya Jimre Tsanantawa
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ku Nisanta Kanku Daga Harkokin Wannan Duniyar da Babu Hadin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Shan Tsanani Domin Adalci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 3/1 pp. 3-4

Me Ya Sa Ake Tsananta wa Mutane Domin Addininsu?

KA YARDA a tsananta wa mutane domin addininsu? Ƙila a’a—musamman ma idan ba su fitini mutane da shi ba. Duk da haka, tsanantawa domin addini ya daɗe kuma har yanzu ana yinsa. Alal misali, a Turai da wasu ɓangarorin duniya an hana Shaidun Jehovah da yawa ’yancinsu kuma an zalunce su duk cikin shekaru na ƙarni na 20.

A waɗannan lokatan an gana wa Shaidun Jehovah azaba, waɗanda aka tsara, kuma na lokaci mai tsawo a ƙarƙashin mulkin kama karya biyu a Turai. Menene abin da ya faru da su ya koya mana game da tsanantawa da ake yi domin addini? Kuma me za mu iya koya daga yadda suka ɗauki wahala?

“Ba na Duniya Ba”

Shaidun Jehovah suna fama domin su kasance masu-bin doka, masu zaman lafiya, kuma mutane masu ɗabi’a. Ba sa hamayya da gwamnatoci ko kuma su nemi arangama da su, ba sa kuwa tsokana domin kawai suna son a kashe su. Waɗannan Kiristoci ba sa saka hannu a siyasa. Wannan daidai yake da kalmomin Yesu: “[Mabiyana] ba na duniya suke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yohanna 17:16) Yawancin gwamnatoci sun san matsayin Shaidu na tsaka-tsaki. Amma masu iko a mulkin kama karya ba sa daraja farillan Littafi Mai Tsarki na kada Kiristoci su zama na duniya.

An bayyana dalilin wannan a wani taro a Jami’ar Heidelberg ta Jamus, a Nuwamba ta 2000. Taron yana da jigo Danne Hakki da Neman Hakki: Shaidun Jehovah a Ƙarƙashin Mulkin Kama Karya da na Kwaminis. Dokta Clemens Vollnhals na ƙungiyar Hannah-Arendt-Institute na Binciken Mulkin Kama Karya, ya ce: “Iko na Mulkin kama karya ba a kan siyasa ba kawai ya ƙare. Suna son mutum ya miƙa kansa ne sukutum.”

Kiristoci na gaskiya ba za su iya ba da “kansu sukutum” ga gwamnatin ’yan Adam ba, domin sun riga sun ba da kansu gaba ɗaya ga Jehovah Allah. Shaidu da suke ƙarƙashin mulkin kama karya sun fahimci cewa abin da Gwamnati take bukata a wasu lokatai sun saɓa wa imaninsu. Menene suka yi sa’ad da suka fuskanci irin wannan saɓani? A cikin tarihi, Shaidun Jehovah sun yi amfani da ƙa’ida da mabiyan Yesu Kristi suka furta: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:29.

Shaidu dubbai sun riƙe amincinsu kuma sun kasance a tsaka-tsaki game da harkokin siyasa duk da tsanani mafi muni. Ta yaya za su iya jimrewa? Daga ina suka sami ƙarfi suka yi haka? Bari su amsa da kansu. Bari kuma mu ga abin da kowa zai koya daga abin da ya faru da su, duk da Shaidu da waɗanda ba Shaidu ba.

[Bayanin da ke shafi na 4]

Shaidun Jehovah a Jamus sun sha tsanani ƙwarai, kuma na dogon lokaci a ƙarƙashin mulkoki biyu na kama karya

[Bayanin da ke shafi na 4]

“Iko na Mulkin kama karya ba a kan siyasa ba kawai ya ƙare. Suna son mutum ya miƙa kansa ne sukutum.”

Dokta Clemens Vollnhals

[Hoto a shafi na 4]

An hana iyalin Kusserow ’yancinsu kuma an sa su a kurkuku domin sun ƙi su karya ƙa’idar imaninsu

[Hoto a shafi na 4]

An kashe Johannes Harms a kurkuku na Nazi domin imaninsa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba