Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 10/1 p. 19
  • Kambin Bangirma ga Majami’ar Mulki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kambin Bangirma ga Majami’ar Mulki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Makamantan Littattafai
  • Majami’un Mulki Suna Buɗe Domin Kowa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Wannan Wurin Ne Muke Bauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Menene Majami’ar Mulki?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Me Ya Sa Ake Gina Majami’un Mulki Kuma Yaya Ake Yin Ginin?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 10/1 p. 19

Rahoto Daga Masu Shelar Mulki

Kambin Bangirma ga Majami’ar Mulki

HUKUMAR Kula da Mahalli a Finland ta yi wa shekara ta 2000 laƙabi da “Shekara ta Ƙawata Mahalli.” Wani da ke cikin masu shirin ya ce “manufar amfani da ƙawata mahalli a jigon shekara domin a tunasar da dukanmu muhimmancin koren mahalli a rayuwarmu ta yau da kullum.”

A 12 ga Janairu, 2001, wasiƙa daga Tarayyar Ma’aikata na Ƙawata Mahalli ta Finland ta iso ofishin reshe na Shaidun Jehovah a Finland. Wasiƙar ta yi bayani cewa Majami’ar Mulki na Shaidun Jehovah a Tikkurila ta ci kambin bangirma na shekara ta ƙawata mahalli domin yadda aka zana mahallinta da fasalin lambunta. Wasiƙar ta daɗa cewa yadda mahallin yake, babu rani babu damina, yana da kyau, yana da kyaun gaske, kuma yana da inganci ƙwarai.”

An ba Shaidun Jehovah kambin bangirma a Otel da ke Rosendahl a Tampere, Finland, a wani biki da ƙwararrun mutane da ’yan kasuwa 400 suka halarta. Tarayyar Ma’aikata na Ƙawata Mahalli ta Finland ta kuma gaya wa manema labarai cewa: “A wurare dabam dabam na ƙasar, Majami’un Mulki na Shaidun Jehovah, kusan kowacce an zana ta da kyau. Yadda ake kula da mahallin na sa masu wucewa su yi sha’awarta sosai. Majami’ar Mulki a Tikkurila misali ce ta lambu mai gwanin kyau. Ginin da filin gidan duka suna nuna lumana da daidaituwa.”

A Finland da akwai Majami’un Mulki 233, lambuna masu kyau suka gewaye yawancinsu. Amma, abin da ya sa waɗannan wurare suke da kyaun gaske ma shi ne cewa cibiyoyi ne na bauta ta gaskiya da kuma koyar da Littafi Mai Tsarki. Ga Shaidun Jehovah miliyan shida da suke ko’ina cikin duniya, Majami’ar Mulki—da aka shirya da kyau ko mai sauƙi—wuri ne da ake so ƙwarai. Shi ya sa suke ɗokin su kula da shi da kyau. Ƙofofin Majami’un Mulki suna buɗe ga duka a yankinku!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba