Jehovah Yana Kyawanta Mutanensa Da Haske
“Tashi, ki bada haske; gama haskenki ya zo, darajar Ubangiji kuma ya hau bisa kanki.”—ISHAYA 60:1.
1, 2. (a) Yaya yanayin ’yan Adam yake? (b) Wanene ya haddasa duhun da ’yan Adam suke ciki?
“WAIYO, da muna da Ishaya ko kuma Waliyi Bulus!” Wannan ita ce kukar Shugaban ƙasar Amirka Harry Truman a shekaru na 1940. Me ya sa ya furta irin waɗannan kalmomin? Domin ya fahimci ana bukatar shugabanni masu ɗabi’a a zamaninsa. Duniya ta shige lokaci na bala’i a ƙarni na 20, yaƙin duniya na biyu. Ko da yake yaƙin ya ƙare, duniya ba ta da zaman lafiya. Duhu ya ci gaba. Shekara 57 bayan ƙarewar yaƙin, duniya har ila tana cikin duhu. Da Shugaban Ƙasa Truman yana raye a yau, babu shakka zai sake ganin bukatar a samu shugabanni masu ɗabi’a irin na Ishaya da manzo Bulus.
2 Ko Shugaba Truman ya sani ko bai sani ba, manzo Bulus ya yi magana game da duhu da yake rufe mutane, kuma ya yi gargaɗi a kan shi a rubuce-rubucensa. Alal misali, Bulus ya gargaɗi ’yan’uwansa masu bi: “Kokawarmu ba da nama da jini ta ke ba, amma da mulkoki, da ikoki, da mahukuntan wannan zamani mai-duhu, da rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Afisawa 6:12) Da waɗannan kalmomi Bulus ya nuna cewa ba kawai yana da sani game da duhu na ruhaniya da ya rufe duniya ba amma kuma ya san ainihin tushensa—aljanu masu ƙarfi da aka kwatanta da “mahukuntan wannan zamani.” Tun da ruhohi ne suke haddasa wannan duhu, menene mutane suka isa su yi su haskaka shi?
3. Duk da yanayi mai duhu na ’yan Adam, menene Ishaya ya annabta ga mutane masu aminci?
3 Ishaya ma ya yi magana game da duhu da ya rufe mutane. (Ishaya 8:22; 59:9) Duk da haka, da ya hangi zamaninmu, ya annabta cikin hurewa cewa har a cikin waɗannan lokatai masu duhu, Jehovah zai haskaka ra’ayin waɗanda suke ƙaunar haske. Ko da yake, ba mu da Bulus ko Ishaya tare da mu, muna da hurarrun rubuce-rubucensu da za su yi mana ja-gora. Don su nuna yadda wannan zai zama ga waɗanda suke bauta wa Jehovah, ka yi la’akari da kalmomin annabci na Ishaya da suke sura ta 60 na littafinsa.
Mace ta Annabci ta Haska Haske
4, 5. (a) Menene Jehovah ya umurci macen ta yi, kuma wane alkawari ne ya yi? (b) Wane bayani ne mai ban sha’awa Ishaya sura 60 ta ƙunsa?
4 Kalmomin farko na Ishaya sura 60 an furta su ga mace ce da take cikin hali na baƙin ciki—tana kwance a ƙasa cikin duhu. Farat ɗaya, sai haske ya haskaka cikin duhun, Jehovah ya yi kira: “Tashi, ki bada haske; gama haskenki ya zo, darajar Ubangiji kuma ya hau bisa kanki.” (Ishaya 60:1) Lokaci ya zo ga macen ta tashi ta ba da haske na Allah, watau, darajarsa. Me ya sa? Za mu ga amsa a aya ta gaba: “Duba, duhu za ya rufe duniya, baƙin duhu kuma za ya rufe al’ummai: amma Ubangiji za ya tashi a bisa kanki, za a ga darajarsa kuma a bisa kanki.” (Ishaya 60:2) Sa’ad da macen ta yi biyayya ga umurnin Jehovah, an tabbatar mata da sakamako mai ban sha’awa. Jehovah ya ce: “Al’ummai za su zo wurin haskenki, sarakuna kuma wurin hasken tāshinki.”—Ishaya 60:3.
5 Waɗannan kalmomi masu ban sha’awa na waɗannan ayoyi uku suna gabatarwa kuma suna taƙaice ainihin labarin saurar raguwar abin da sura ta 60 ta Ishaya ta ƙunsa. Ta annabta abin da mace ta annabcin ta fuskanta kuma ta yi bayanin yadda mu za mu iya kasancewa cikin hasken Jehovah duk da duhu da ya rufe ’yan Adam. Menene waɗannan alamu cikin waɗannan ayoyi uku na farko suke nufi?
6. Wace ce mace ta Ishaya sura 60, kuma wace ce wakiliyarta a duniya?
6 Macen Ishaya 60:1-3 Sihiyona ce, ƙungiyar Jehovah ta halittun ruhohi. A yau, raguwar “Isra’ila na Allah,” ce take wakiltar Sihiyona a duniya, ikilisiyar Kiristoci shafaffu na dukan duniya, waɗanda suke da begen sarauta da Kristi a sama. (Galatiyawa 6:16) Wannan al’umma ta ruhaniya adadinta ya kai 144,000, kuma cikar Ishaya sura 60 ta dangana ne a kan waɗanda suke raye a duniya a lokacin “kwanaki na ƙarshe.” (2 Timothawus 3:1; Ru’ya ta Yohanna 14:1) Annabcin kuma ya faɗi abubuwa da yawa game da abokanan waɗannan Kiristoci shafaffu, “taro mai girma” na “waɗansu tumaki.”—Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16.
7. Yaya yanayin Sihiyona yake a shekara ta 1918, kuma yaya aka annabta wannan?
7 Da akwai lokaci ne da “Isra’ila na Allah” take kwanciya cikin duhu, kamar yadda mace ta annabci ta alamta? Hakika, wannan ya faru fiye da shekara 80 da ta gabata. A lokacin yaƙin duniya na farko, Kiristoci shafaffu sun yi ƙoƙari su ci gaba da aikin wa’azi. Amma a shekara ta 1918, shekarar ƙarshe ta yaƙin, tsararren aikin wa’azi kusan ya tsaya cak. Joseph. F. Rutherford, wanda yake kula da aikin wa’azi a dukan duniya, da kuma wasu fitattun Kiristoci an ɗaure su na shekaru masu yawa a kan tuhuma ta ƙarya. A Ru’ya ta Yohanna, Kiristoci shafaffu da suke duniya an kwatanta su da gawawwaki a annabce, suna “kwanciya cikin karabkar babban birni, wanda a ke ce da shi a ruhaniya Saduma da Masar.” (Ru’ya ta Yohanna 11:8) Wannan hakika lokaci ne mai duhu ga Sihiyona, kamar yadda ’ya’yanta shafaffu na duniya suka wakilce ta!
8. Wane canji ne mai ban mamaki ya faru a shekara ta 1919, kuma menene sakamakon haka?
8 Duk da haka, shekara ta 1919 ta ga canji mai ban mamaki. Jehovah ya haskaka Sihiyona! Waɗanda suka tsira na Isra’ila ta Allah suka tashi tsaye domin su haskaka hasken Allah, da zuciya ɗaya suka sake fara shelar bishara. (Matta 5:14-16) Godiya ta tabbata ga sabon ƙwazo na waɗannan Kiristoci, ya jawo wasu zuwa wajen hasken Jehovah. Da farko, sababbin zuwa an naɗa su su kasance cikin Isra’ila ta Allah. An kira su sarakuna a Ishaya 60:3, tun da za su zama magāda tare da Kristi a Mulkin Allah na sama. (Ru’ya ta Yohanna 20:6) Daga baya aka fara jawo taro mai girma na waɗansu tumaki zuwa ga hasken Jehovah. Waɗannan sune “al’ummai” da aka ambata a cikin annabcin.
’Ya’yan Macen Sun Zo Gida!
9, 10. (a) Menene macen ta gani, kuma menene wannan yake alamtawa? (b) Wane dalili Sihiyona take da shi na farin ciki?
9 Yanzu, Jehovah ya fara ba da bayani dalla-dalla da ke a Ishaya 60:1-3. Ya ba wa macen wani umurni. Ka saurari abin da ya ce: “Tada idanunki ki duba ko’ina, ki gani.” Macen ta yi biyayya, kuma ta ga abin mamaki! ’Ya’yanta suna zuwa gida. Nassin ya ci gaba da cewa: “Dukansu suna tattaruwa, suna zuwa wurinki: ’ya’yanki maza daga nesa za su taho, ’ya’yanki mata kuma za a zo da su a goye.” (Ishaya 60:4) Aikin wa’azi na dukan duniya da aka fara a shekara ta 1919 ya jawo sababbin mutane dubbai zuwa hidima ta Jehovah. Waɗannan ma sun zama “ ’ya’ya” maza da mata na Sihiyona, shafaffu na Isra’ila ta Allah. Saboda haka, Jehovah ya kyawanta Sihiyona ta wajen kawo mutane na ƙarshe na 144,000 zuwa wajen haske.
10 Za ka iya tunanin irin farin cikin Sihiyona da ’ya’yanta suka zo wajenta? Duk da haka, Jehovah ya ba Sihiyona ƙarin dalilin farin ciki. Mu karanta: “Sa’annan za ki gani ki sami haske, zuciyarki kuma ta motsu ta buɗe; domin albarkar teku za ta juya ta nufa wajenki, wadatar al’ummai kuma za ta zo gareki.” (Ishaya 60:5) Cikin jituwa da waɗannan kalmomin annabci, tun a shekaru na 1930, taro mai girma na Kiristoci waɗanda begensu su zauna a duniya ne har abada sun ruga zuwa Sihiyona. Sun fito daga cikin “teku” na mutane da suke a ware daga Allah kuma suna wakiltan arzikin al’ummai. Su ne “muradin dukan dangogi.” (Haggai 2:7; Ishaya 57:20) Ka lura kuma cewa waɗannan “muradin” ba su je su bauta wa Jehovah kowanne a tasa hanyar ba. A’a, sun ƙara kyawanta Sihiyona ta wajen zuwa su yi bauta cikin haɗin kai da ’yan’uwansu shafaffu, suka zama “garke ɗaya” da su a ƙarƙashin “makiyayi ɗaya.”—Yohanna 10:16.
’Yan Kasuwa, Makiyaya, da Kuma ’Yan Tireda Sun Zo Wajen Sihiyona
11, 12. Ka kwatanta taro da aka gani yana dumfarar Sihiyona.
11 Sakamakon wannan tattarawa da aka annabta shi ne ƙari mai ban mamaki na adadin masu yabon Jehovah. An annabta wannan a cikin waɗannan kalmomi na annabci da ke gaba. Ka yi tunanin kana tsaye da wannan macen ta annabci a Dutsen Sihiyona. Ka kalli gabas, kuma me ka gani? “Yawan raƙuma kuma za su rufe ki, ’yan raƙuma ke nan na Midian da na Ephah; daga Sheba dukansu za su zo: za su kawo zinariya da lubban, za su kawo bisharar yabon Ubangiji.” (Ishaya 60:6) Taron ’yan kasuwa suna jan ayarorinsu a kan hanyar da take zuwa Urushalima. Raƙuman kamar ambaliya ce da ta rufe ƙasa! ’Yan tireda suna ɗauke da kyauta mai tamani, “zinariya da lubban.” Kuma waɗannan ’yan kasuwa sun zo wajen hasken Allah domin su yaba masa a fili, su yi ‘bisharar yabon Jehovah.’
12 Ba ’yan kasuwa ba ne kawai suke zuwa. Makiyaya su ma suna rugawa zuwa Sihiyona. Annabcin ya ci gaba da cewa: “Za a tattara dukan garkuna na Kedar zuwa gareki, raguna na Nebaioth za su yi miki hidima.” (Ishaya 60:7a) Ƙabilar makiyaya suna zuwa cikin birni mai tsarki su ba da kyawawan dabbobinsu ga Jehovah. Sun ma ba da kansu su yi wa Sihiyona hidima! Yaya Jehovah ya marabci waɗannan bare? Allah da kansa ya amsa: “Za su kawo abin karɓa bisa kan bagadina; ni kuwa zan girmama gidana na daraja.” (Ishaya 60:7b) Jehovah ya karɓi kyauta da kuma hadayun waɗannan bare da karimanci. Kasancewarsu a nan ya kyawanta haikalinsa.
13, 14. Me aka gani suna zuwa daga yamma?
13 Yanzu, ka juya ka dubi yamma. Me ka gani? A can nesa, da wani abin da ya yi kama da farin gajimare da ya rufe dukan teku. Jehovah ya yi tambayar da take zuciyarka: “Su wanene waɗannan masu-tashi kamar cincirindo, kamar tantabaru kuma zuwa sakatansu?” (Ishaya 60:8) Jehovah ya amsa tambayarsa: “Tsibirai za su saurara mini, jiragen Tarshish kuma su ne gaba, domin a ɗauki ’ya’yanki daga nesa a kawo su, azurfarsu da zinariyarsu kuma tare da su, saboda sunan Ubangiji Allahnki, sabili da Mai-tsarki na Isra’ila, domin ya ɗaukaka ki.”—Ishaya 60:9.
14 Za ka iya zana yanayin? Farin gajimare ya zo kusa kuma yanzu ya yi kama da ƙananan abubuwa suna zuwa daga yamma. Ya yi kama da tsuntsaye suna firiya a saman ruwa. Da suka ƙara yin kusa, sai ka ga cewa jiragen ruwa ne da iska ke ɗaukan zannuwansu. Jiragen da suke zuwa Urushalima suna da yawa da suka yi kama da tantabarai. Daga nesa, jiragen suna zuwa da gudu, suna kawo masu bi zuwa Urushalima su bauta wa Jehovah.
Ƙungiyar Jehovah ta Bunƙasa
15. (a) Wace bunƙasa ce kalmomin Ishaya 60:4-9 suka annabta? (b) Kiristoci na gaskiya suna nuna wane hali?
15 Lallai wannan zane ne mai kyau na ayoyi 4 zuwa 9 da suka zana bunƙasa ta dukan duniya da ta faru a shekara ta 1919! Me ya sa Jehovah ya albarkaci Sihiyona da irin wannan ƙaruwa? Domin daga shekara ta 1919, Isra’ila ta Allah cikin biyayya ta nace wajen haskaka haske daga Jehovah. Amma ka lura cewa, kamar yadda aya 7 ta ce, sababbin zuwan suna zuwa har “bisa kan bagadi [na Allah]”? Bagadi wajen da ake yin hadaya ne, kuma wannan ɓangare na annabci ya tuna mana cewa hidimar Jehovah ta ƙunshi hadaya. Manzo Bulus ya rubuta: “Ina roƙonku fa, . . . ku miƙa jikunanku hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karɓa ga Allah, bautarku mai-ruhaniya ke nan.” (Romawa 12:1) Cikin jituwa da kalmomin Bulus, Kiristoci na gaskiya ba sa gamsuwa da halartar hidima na addini sau ɗaya kawai a mako. Suna ba da lokacinsu, da ƙarfinsu, da kuma dukiyarsu, domin yaɗa bauta ta gaskiya. Shin bayyanar irin waɗannan masu bauta ba ta kyawanta gidan Jehovah ne? Annabcin Ishaya ya ce zai yi. Kuma za mu ga cewa irin wannan masu bauta da himma, kyawawa ne a idanun Jehovah.
16. Su waye suka tallafa wajen sake gine-gine a zamanin dā, kuma su waye suka yi haka a zamanin yau?
16 Sababbin zuwan suna so su yi aiki. Annabcin ya ci gaba da cewa: “Baƙi kuma za su gina ganuwarki, sarakunansu kuma za su hidimce ki.” (Ishaya 60:10) A cikar farko na waɗannan kalmomi a zamanin komowa daga hijira daga Babila, sarakuna da kuma wasu daga al’ummai suka taimaka aka sake gina haikali da kuma birnin Urushalima. (Ezra 3:7; Nehemiah 3:26) A cikar su ta zamani, taro mai girma sun tallafa wa raguwar shafaffu wajen gina bauta ta gaskiya. Sun taimaka wajen gina ikilisiyoyi ta haka kuma suna ƙarfafa “garu” na ƙungiyar Jehovah. Kuma sun saka hannu cikin aikin gine-gine na zahiri—gine-gine na Majami’ar Mulki, Majami’ar Babban Taro, da kuma gine-gine na Bethel. A dukan waɗannan hanyoyi, suna tallafa wa waɗannan ’yan’uwansu shafaffu wajen kula da bukatun ƙungiyar Jehovah da take bunƙasa!
17. A wace hanya ce Jehovah ya kyawanta mutanensa?
17 Kalmomin ƙarshe na Ishaya 60:10 suna da ban ƙarfafa! Jehovah ya ce: “Cikin hasalata na buge ki, amma cikin alherina na yi miki jinƙai.” Hakika, a shekara ta 1918 zuwa ta 1919, Jehovah ya hori mutanensa. Amma wannan ya shige. Yanzu lokaci ne da Jehovah yake nuna jinƙai ga bayinsa shafaffu da kuma abokanansu waɗansu tumaki. Tabbacin cewa wannan haka ne shi ne ƙari mai yawa da ya albarkace su da shi, ‘yana kyawanta su.’
18, 19. (a) Wane alkawari Jehovah ya yi wa sababbin zuwa cikin ƙungiyarsa? (b) Menene raguwar ayoyi na Ishaya 60 suka gaya mana?
18 Kowacce shekara, “baƙi” dubbai suna tarayya da ƙungiyar Jehovah, kuma za ta kasance a buɗe ga mutane da yawa da za su biyo su. Jehovah ya ce wa Sihiyona: “Ƙofofinki kuma za su kasance a buɗe tuttur: ko da dare, ko da rana ba za a rufe su ba; domin mutane su kawo miki wadatar al’ummai, sarakunansu kuma a gaba.” (Ishaya 60:11) Wasu ’yan hamayya sun yi ƙoƙari su rufe waɗannan “ƙofofin,” amma mun sani cewa ba za su yi nasara ba. Jehovah da kansa ya ce ta kowacce hanya, ƙofar za ta kasance a buɗe. Ƙaruwa za ta ci gaba.
19 Har yanzu da akwai wasu hanyoyi da Jehovah ya albarkaci mutanensa, ya kyawanta su, a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Raguwar ayoyi na Ishaya 60 sun bayyana waɗannan hanyoyi a annabce.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Wacce ce “mace” ta Allah, kuma waye ke wakiltarta a duniya?
• Yaushe ne ’ya’yan Sihiyona suka kwanta, yaushe kuma ta yaya suka “tashi”?
• Ta wajen amfani da alamu dabam dabam, ta yaya Jehovah ya annabta ƙari na masu wa’azin Mulki a yau?
• A wace hanya ce Jehovah ya sa haskensa ya haskaka a kan mutanensa?
[Hoto a shafi na 22]
“Macen” Jehovah an umurce ta ta tashi
[Hoto a shafi na 24]
Jiragen ruwa kamar cincirindo daga nesa