Suna da Tasu Irin Hikima
“MANYA suna da hikima, amma yara ma suna da tasu irin hikima,” in ji wani karin magana na Nijeriya. Edwin, dattijo na Kirista a Nijeriya, ya ga hakan gaskiya ne.
Wata rana, Edwin ya samu asusun ƙarfe a ƙarƙashin teburinsa a gida.
“Na waye wannan?” Edwin ya tambayi ’ya’yansa uku.
“Nawa ne,” Emmanuel ɗan shekara takwas ya amsa. Ya yi hanzari ya daɗa cewa wannan asusu mai tsatsa na ƙarfe mai faɗin inci biyar da yake da baki a sama domin ba da kyauta ne na aikin dukan duniya na Shaidun Jehovah. “Tun da ba na zuwa Majami’ar Mulki kowacce rana,” ya yi bayani, “shi ya sa na yi asusu saboda idan ban kashe kuɗin abinci na ba, in saka a cikin asusun.”
Uban Emmanuel yana da asusu a gida domin tara kuɗi don halartar taron gunduma. Amma domin wasu matsaloli na iyali, sun yi amfani da kuɗin. Domin ya tabbata cewa ba a yi amfani da kyautarsa ba domin wani abu dabam, Emmanuel ya ɗauki tsohon gwangwani ya kai wa mai walda ya rufe masa. Mai waldan da ya fahimci dalilin gwangwanin, ya yi wa Emmanuel asusu da raguwar ƙarfensa. Michael, ƙanin Emmanuel, ɗan shekara biyar ma ya nemi asusu.
Da ya yi mamakin abin da yaran suka yi, Edwin ya tambaye su dalilin da ya sa suka yi asusu. Michael ya amsa: “Ina so in ba da kyauta!”
Emmanuel, Michael, da kuma Uchei, ’yarsu ’yar shekara tara, ashe suna tara kuɗi daga cikin kuɗin abincinsu na rana ta wajen saka su cikin asusu. A ina suka samu wannan hikima? Da zarar yaran sun yi girma su riƙe kuɗi a hannunsu, iyayensu sun koya musu saka kuɗi a cikin asusu na ba da kyauta a Majami’ar Mulki. Hakika, yaran suna amfani da abin da suka koya.
Sa’ad da asusun suka cika, sai aka buɗe su. Abin da suka tare ya kai misalin ₦349. 62 ($3.13 U.S.)—ba ƙaramin kuɗi ba ne a ƙasar da matsakaicin abin da mutane suke samu a shekara ’yan ɗarurruwan daloli ne. Irin wannan ba da kyauta da son rai don tallafa wa aikin wa’azi na Shaidun Jehovah da yanzu ana yi a ƙasashe 235 a dukan duniya.