Fa’idodin Bishara
“Ubangiji ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga matalauta; ya aike ni domin in warkadda masu-karyayyen zuciya . . . in yi ma dukan masu-makoki ta’aziyya.”—ISHAYA 61:1, 2.
1, 2. (a) Wanene Yesu ya bayyana kansa, kuma ta yaya? (b) Waɗanne fa’idodi ne bisharar da Yesu ya yi shelarta ta kawo?
DA FARKO a hidimarsa a wata ranar Asabarci, Yesu yana cikin majami’a a Nazarat. Yadda labarin ya ce, “aka miƙa masa littafin annabi Ishaya. Ya buɗe littafi, ya iske wurin da aka rubuta, Ruhun Ubangiji yana bisa gareni, gama ya shafe ni da zan yi shelar bishara.” Yesu ya ci gaba da karatun wasu wurare na annabci. Sai ya zauna kuma ya ce: “Yau an cika wannan nassi a cikin kunnuwanku.”—Luka 4:16-21.
2 A wannan hanya, Yesu ya nuna kansa mai wa’azin bishara da aka annabta, mai faɗar bishara kuma mai ɗauke da ta’aziyya. (Matta 4:23) Hakika bishara ce da Yesu yake da ita ya faɗa! Ya gaya wa waɗanda ke jinsa: “Ni ne hasken duniya: wanda yana biyona ba za shi yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai.” (Yohanna 8:12) Ya kuma ce: “Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske; ku a san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantadda ku.” (Yohanna 8:31, 32) Hakika Yesu yana “da maganar rai na har abada.” (Yohanna 6:68, 69) Haske, rai, ’yanci—hakika waɗannan fa’idodi ne da za a daraja!
3. Wace bishara ce almajiran Yesu suka yi wa’azinta?
3 Bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., almajiran suka ci gaba da aikin bishara da Yesu ya yi. Sun yi wa’azin “bishara kuwa ta mulki” ga Isra’ilawa da kuma mutane na al’ummai. (Matta 24:14; Ayukan Manzanni 15:7; Romawa 1:16) Waɗanda suka yi na’am suka zo ga sanin Jehovah Allah. An ’yantar da su daga bauta ta addini kuma sun zama sashen sabuwar al’umma ta ruhaniya, “Isra’ila na Allah,” wanda waɗanda suke ciki suke da begen yin sarauta ta har abada a sama tare da Ubangijinsu, Yesu Kristi. (Galatiyawa 5:1; 6:16; Afisawa 3:5-7; Kolossiyawa 1:4, 5; Ru’ya ta Yohanna 22:5) Lallai waɗannan fa’idodi ne masu tamani!
Bishara a Yau
4. A wace hanya ce ake cika aikin wa’azin bishara a yau?
4 A yau, Kiristoci shafaffu waɗanda “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki” da suke girma suke goya musu baya, suna ci gaba da cika aikin nan da aka ba Yesu cikin annabci. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) Sakamakon haka, ana wa’azin bisharar da girma yadda ba a taɓa yinta ba. A cikin ƙasashe da yankuna 235, Shaidun Jehovah sun fita su “yi shelar bishara ga matalauta . . . [su] warkadda masu-karyayyen zuciya, [su] yi ma ɗaurarru shela ta sāki, da buɗewar kurkuku ga waɗanda su ke a sarƙa; [su] yi shelar shekara ta alherin Ubangiji, da ranar sakaiya ta Allahnmu: [su] yi ma dukan masu-makoki ta’aziyya.” (Ishaya 61:1, 2) Saboda haka, aikin bishara na Kirista ya ci gaba da kawo fa’idodi ga mutane da yawa da kuma ta’aziyya ta gaske ga “waɗanda ke cikin kowane irin ƙunci.”—2 Korinthiyawa 1:3, 4.
5. Game da yin wa’azin bisharar, ta yaya Shaidun Jehovah suke dabam da coci na Kiristendam?
5 Hakika, cocin Kiristendam suna da bishara iri-iri. Da yawa suna aikawa da masu wa’azi na ƙasashen waje don su nemi ’yan tuba a wasu ƙasashe. Alal misali, The Orthodox Christian Mission Center Magazine ya ba da rahoto a kan aikin masu wa’azi na ƙasashen waje na ’yan Orthodox a Madagascar, a kudancin Afirka, Tanzania, da kuma Zimbabwe. Amma, a coci na ’yan Orthodox, yadda yake cikin wasu coci na Kiristendam, yawancinsu ba sa sa hannu cikin irin aikin nan. Akasin haka, dukan Shaidun Jehovah da suka keɓe kansu suna ƙoƙari su sa hannu cikin bishara. Sun fahimci cewa yin shelar bishara tabbaci ne na nuna tabbacaccen bangaskiyarsu. Bulus ya ce: “Da zuciya mutum yake bada gaskiya zuwa adalci; da baki kuma a ke shaida zuwa ceto.” Bangaskiya da ba ta motsa mutum ya aikata wani abu, lallai macacciya ce.—Romawa 10:10; Yaƙub 2:17.
Bishara da Take Kawo Fa’idodi Masu Dawwama
6. Wace bishara ce ake wa’azinta a yau?
6 Shaidun Jehovah ne suke wa’azin labari mafi kyau da ke akwai. Suna buɗe Littafi Mai Tsarki nasu su nuna wa waɗanda suke sauraro cewa Yesu ya ba da hadayar ransa ya buɗe wa mutane hanya da za su kusanci Allah, su samu gafarar zunubai, da kuma begen rai na har abada. (Yohanna 3:16; 2 Korinthiyawa 5:18, 19) Suna shelar cewa an kafa Mulkin Allah a sama a ƙarƙashin Sarki shafaffe, Yesu Kristi, kuma ba da daɗewa ba zai kawar da mugunta daga duniya kuma ya lura da maido da Aljanna. (Ru’ya ta Yohanna 11:15; 21:3, 4) A cikar annabcin Ishaya, suna gaya wa maƙwabtansu cewa yanzu ne “shekara ta alherin Ubangiji” lokaci da mutane har ila za su iya saurara ga bisharar. Suna kuma faɗakar da cewa ba da daɗewa ba “ranar sakaiya ta Ubangijinmu” lokaci da Jehovah zai kawo ƙarshen masu mugunta da suka ƙi tuba zai zo.—Zabura 37:9-11.
7. Wane labari ne ya nuna haɗin kan Shaidun Jehovah, kuma me ya sa suke morar irin wannan haɗin kai?
7 A cikin duniyar da take cike da masifa da bala’i, wannan ne bishara kawai da take da fa’idodi masu dawwama. Waɗanda suka yi na’am da ita suna zama sashe na haɗaɗiyar ’yan’uwanci na Kirista na dukan duniya da ba sa yarda wa wariyar ƙasa, ƙabilanci, ko kuma yanayin tattalin arziki ya raba su. Sun riga sun ‘yafa wa kansu ƙauna, wadda magami ne kamiltacce.’ (Kolossiyawa 3:14; Yohanna 15:12) An ga wannan a shekarar da ta shige a wata ƙasar Afirka. Wata rana da safiya aka ta da babban birnin da ƙarar harba bindigogi. Ana ƙoƙarin ƙwace mulki. Yayin da aukuwar ta zama na wariyar dangi, sai aka tuhumi wata iyali da Shaidu ne da cewa suna ɓoye ’yan’uwansu Shaidu na wani dangi dabam. Iyalin ta ce: “Shaidun Jehovah ne kawai suke zama a gidanmu.” A gare su, wariyar dangi ba ta da wani muhimmanci; ƙaunar Kirista ce—yin ta’aziyya wa wasu da ke bukatar haka—ne ke da muhimmanci. Wata cikin dangin da ba Mashaidiya ba, ta ce: “Waɗanda suke cikin dukan addinai suna cin amanar waɗanda suke sujjada tare. Shaidun Jehovah ne kaɗai ba sa haka.” Aukuwa da yawa makamanci da aka rahoto daga ƙasashe da suke yaƙin basasa sun nuna cewa Shaidun Jehovah da gaske sun “ƙaunaci ’yan’uwanci.”—1 Bitrus 2:17.
Bisharar Tana Canja Mutane
8, 9. (a) Waɗanne gyare-gyare waɗanda suka amince da bisharar suka yi? (b) Waɗanne labarai ya nuna ikon bisharar?
8 Bisharar tana game da abin da Bulus ya kira ne “rai na yanzu, da na mai-zuwa.” (1 Timothawus 4:8) Ba kawai yana ba da bege mai girma don nan gaba ba amma kuma yana kawo gyara don “rai na yanzu.” Mutane ɗai-ɗai, Kalmar Allah ce, Littafi Mai Tsarki, ke ja-gorar Shaidun Jehovah, su sa rayuwarsu ta jitu da nufin Allah. (Zabura 119:101) Mutuntakarsu tana sabonta yayin da suke gina halaye na adalci da aminci.—Afisawa 4:24.
9 Ka yi la’akari da misalin Franco. Yana da matsalar yin fushi. Duk lokacin da ransa ya ɓace, yakan hasala ƙwarai kuma ya farfashe abubuwa. Matarsa ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehovah, kuma misalinsu na Kirista ya taimake Franco ya ga ya kamata ya yi gyara. Ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare da su kuma a ƙarshe ya iya bayyana ’ya’yan ruhu mai tsarki na salama da kamewa. (Galatiyawa 5:22, 23) Yana ɗaya daga cikin 492 da suka yi baftisma a Belgium a shekarar hidima ta 2001. Ka kuma yi la’akari da Alejandro. Wannan matashin ya lazamtu da mugun ƙwaya ya dulmuya ciki har yana kwasan kaya a bola, ya sayar da su don ya sayi miyagun ƙwayoyi. Lokacin da yake ɗan shekara 22, Shaidun Jehovah suka gayyace Alejandro ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma ya yarda. Yana karanta Littafi Mai Tsarki kowacce rana kuma yana halartar taron Kirista. Ya tsarkake rayuwarsa da sauri da kafin wata shida, ya iya sa hannu a aikin bishara—yana ɗaya daga cikin 10,115 da suka yi hakanan a shekarar da ta shige a Panama.
Bishara—Albarka ga Masu Tawali’u
10. Su wa ke yin na’am da bisharar, kuma ta yaya ra’ayinsu ya canja?
10 Ishaya ya annabta cewa za a yi wa’azin bisharar ga masu tawali’u. Su wanene masu tawali’un nan? Sune aka kwatanta cikin littafin Ayukan Manzanni cewa “waɗanda aka ƙaddara su ga rai na har abada.” (Ayukan Manzanni 13:48) Masu sauƙin kai ne daga kowane matsayi cikin jam’iyya da suka ba da zukatansu ga saƙon gaskiya. Irin waɗannan sun koyi cewa yin nufin Allah yana kawo fa’idodi da suka fi duk wani abin da duniya za ta iya bayarwa. (1 Yohanna 2:15-17) Amma fa, yaya Shaidun Jehovah suke kai zukatan mutane a aikinsu na bishara?
11. In ji Bulus, yaya ya kamata a yi wa’azin bisharar?
11 To, ka yi la’akari da misalin manzo Bulus, wanda ya rubuta ga Korinthiyawa: “ ’Yan’uwa, sa’anda na zo wurinku, ba da gwanintar zance na zo ba ko da hikima, ina yi muku shelar asirin Allah. Gama na ƙudurta ba ni sane da komi a cikinku ba, sai Yesu Kristi kaɗai, shi kuwa [ratayyaye].” (1 Korinthiyawa 2:1, 2) Bulus bai yi ƙoƙari ya burge waɗanda suke sauraronsa ba ta wurin iliminsa. Ba abin da ya koyar sai tabbacaccen gaskiya ta Allah, gaskiyar da ke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki a yau. Ka kuma lura da ƙarfafa da Bulus ya yi wa ɗan’uwansa, Timothawus, mai wa’azin bishara: “Ka yi wa’azin kalma; ka yi naciya.” (2 Timothawus 4:2) Ya kamata Timothawus ya yi wa’azin “kalma,” saƙon Allah. Bulus kuma ya rubuta zuwa ga Timothawus: “Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gareshi, kana rarrabe kalmar gaskiya sosai.”—2 Timothawus 2:15.
12. Ta yaya Shaidun Jehovah a yau suke bin kalmomin Bulus da kuma misalinsa?
12 Shaidun Jehovah suna bin misalin Bulus, da kuma kalmominsa ga Timothawus. Sun fahimci ikon Kalmar Allah kuma suna yin amfani mai kyau da shi yayin da suke biɗan maƙwabtansu da kalmomin bege da suka dace da kuma ta’aziyya. (Zabura 119:52; 2 Timothawus 3:16, 17; Ibraniyawa 4:12) Hakika, suna amfani mai kyau da littattafan Littafi Mai Tsarki don waɗanda suke so su samu ƙarin sani na Littafi Mai Tsarki a nasu lokaci. Amma kullum suna neman su nuna wa mutane kalmomi daga Nassi. Sun sani cewa hurariyar Kalmar Allah za ta motsa zukatan masu tawali’u. Kuma idan sun yi amfani da shi a wannan hanyar tana ƙarfafa tasu bangaskiya ma.
‘Ta’aziyya ga Masu Baƙin Ciki’
13. A shekara ta 2001, wace aukuwa ta jawo bukatar ta’aziyya ga waɗanda suke baƙin ciki?
13 Shekara ta 2001 ta samu nata rabon bala’i, domin haka, mutane da yawa suna bukatar ta’aziyya. Satumba da ta shige ta ga misali na musamman a Amirka, da ’yan ta’ada suka kai wa Cibiyar Kasuwanci na Duniya (World Trade Center) a New York da kuma Pentagon kusa da Washington, D.C., farmaki. Farmakin ya firgita ƙasar gabaki ɗaya! A waɗannan aukuwa, Shaidun Jehovah suka yi ƙoƙarin su cika aikinsu na yin ‘ta’aziyya ga masu baƙin ciki.’ Labarai kalilan za su nuna yadda suka yi wannan.
14, 15. Ta yaya a yanayi biyu Shaidu suka yi amfani sosai da nassosi don su wa masu baƙin ciki ta’aziyya?
14 Wata Mashaidiya da mai bishara ce na cikakken lokaci ta kusanci wata mace da take kan titi kuma ta tambaye ta ra’ayinta game da farmakin ’yan ta’ada na baya bayan nan. Matar ta soma kuka. Ta ce ba ta ji daɗinsa ba sam sam kuma ta yi fata ta ba da wani taimako. Mashaidiyar ta gaya mata cewa Allah yana sonmu duka, kuma ta karanta Ishaya 61:1, 2. Wannan hurariyar kalmar Allah ta zama da ma’ana ga matar, wadda ta ce kowa na baƙin ciki. Ta karɓi warƙa kuma ta ce Mashaidiyar ta ziyarce ta a gida.
15 Shaidu biyu da suke aikin wa’azi suka sadu da wani mutum da ke aiki cikin rumfarsa. Suka nuna masa kalmomin ta’aziyya daga Nassosi game da masifa da ta same Cibiyar Kasuwanci na Duniya. Da yardarsa suka karanta 2 Korinthiyawa 1:3-7, wadda kalmomin nan suke ciki: ‘Ta’aziyya tana yawaita ta wurin Kristi.’ Mutumin ya yi godiya yana cewa maƙwabtansa Shaidu suna yi wa wasu ta’aziyya kuma ya ce: “Bari Allah ya albarkaci aiki mai girma da kuke yi.”
16, 17. Waɗanne labarai biyu suka nuna ikon Littafi Mai Tsarki don taimaka wa mutane da suke baƙin ciki ko kuma da sun damu game da masifu?
16 Wani Mashaidi lokacin da yake koma ziyara wajen waɗanda suka nuna suna so ya sadu da ɗan wata mace da ta nuna dā tana son saƙon kuma ya kasance cewa ya damu game da lafiyar maƙwabtansa bayan masifa na baya bayan nan. Mutumin ya yi mamaki cewa Mashaidin ya ɗauki lokaci yana ziyartar mutane kuma yana tambayar lafiyarsu. Ya ce yana aiki ne kusa da Cibiyar Kasuwanci na Duniya yayin da farmakin ya auku kuma ya ga dukan abin da ya faru. Da ya yi tambaya ko me ya sa Allah ya ƙyale mugunta, Mashaidin ya karanta ayoyi daga Littafi Mai Tsarki, har da Zabura 37:39, wadda ta ce: “Ceton masu-adalci daga wurin Ubangiji ne: shi ne marayarsu cikin kwanakin wahala.” Sai mutumin ya tambayi Mashaidin lafiyarsa da na iyalinsa, ya ce ya sake ziyararsa, kuma ya yi godiya don ziyarar da ya yi.
17 Wata kuma cikin dubbai da suke baƙin ciki, da Shaidun Jehovah suke yi musu ta’aziyya bayan farmakin ’yan ta’adan, mace ce da Shaidun suka sadu da ita yayin da suke ziyartar maƙwabtansu. Ta damu ƙwarai da abin da ya faru kuma ta saurara lokacin da suke karatun Zabura 72:12-14: “Za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka: matalauci kuma wanda ba shi da mai-taimako. Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-mayata, za ya kuwa ceci rayukan fakirai. Za ya fanshi ransu daga zalunci da ƙwace; a ganinsa kuma jininsu mai-daraja ne.” Lallai kalmomin nan suna da ma’ana! Matar ta ce Shaidun su sake karanta ayoyin kuma ta gayyace su zuwa gidanta su ci gaba da tattaunawa. A ƙarshen taɗin, aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki.
18. Ta yaya wani Mashaidi ya taimaki maƙwabtansa yayin da aka gayyace shi ya yi musu addu’a?
18 Wani Mashaidi yana aiki a kantin cin abinci a yanki mai arziki inda mutane dā ba sa yawan son bisharar Mulkin. Bayan farmakin ’yan ta’ada, mazaunan wurin suka firgita. Da maraice ranar Jumma’a bayan farmakin, manajar wurin cin abincin ta ce kowa ya fita waje kuma ya riƙe kyandir, lokaci da za su yi bimbini a tunawa da waɗanda abin ya shafa. A daraja juyayinsu, Mashaidin ya fita kuma ya tsaya shuru a kan titin. Manajar ta sani shi Mashaidin Jehovah ne, saboda haka bayan da suka gama bimbini, ta ce masa ya yi musu addu’a. Mashaidin ya yarda. A cikin addu’arsa, ya ambaci baƙin ciki da ke ko’ina amma ya ce masu baƙin cikin suna da bege. Ya yi maganar lokaci da irin aukuwar nan ba za su ƙara faruwa ba kuma ya ce duka za su iya su kusaci Allah na ta’aziyya ta wurin cikakken sani daga Littafi Mai Tsarki. Bayan da suka ce “Amin,” manajar—tare da mutane fiye da 60 da suke a waje da kantin cin abincin—suka je wajen Mashaidin, suka gode masa, suka kuma rungume shi, tana cewa addu’ar ce mafi kyau da ta taɓa ji.
Fa’idodi ga Jama’a
19. Wane labari ya nuna cewa wasu suna godiya ga mizanai masu girma na Shaidun Jehovah?
19 A cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe, yankuna inda Shaidun Jehovah suke aiki suna amfana daga gare su—yadda mutane da yawa sun faɗa ke nan. To, mutane da suke gabatar da salama, kirki, da kuma ɗabi’a mai tsabta ba za su zama haka ba? A wata ƙasa ta Asiya ta Tsakiya, Shaidu suka sadu da wani babban ma’aikaci wajen tsaro na jihar da ya yi murabus. Ya ce an sa shi ya bincika ƙungiyoyin addini dabam dabam. Da ya bincika Shaidun Jehovah, halinsu na gaskiya da kuma na kirki ya burge shi. Ya so yadda suke tsayin daka a bangaskiyarsu da kuma gaskiya a koyarwarsu da ke bisa Nassosi. Wannan mutumin ya amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.
20. (a) Menene rahoton aiki da Shaidun Jehovah suka yi a shekarar da ta shige ya nuna? (b) Menene ya nuna cewa da akwai aiki mai yawa da za a yi, kuma yaya muke ɗaukan gatar bishara?
20 Daga cikin labarai kalilan da aka ambata cikin talifin nan, daga cikin dubbai da an ambata, a bayyane yake cewa Shaidun Jehovah sun shagala sosai a shekarar hidima ta 2001.a Sun yi magana da miliyoyin mutane, sun yi ta’aziyya ga mutane da yawa da suke baƙin ciki, kuma sun sami sakamako mai kyau na aikin bishararsu. An samu mutane 263,431 da suka nuna alamar keɓe kansu ga Allah ta wurin yin baftisma. A duk duniya, adadin masu bishara sun ƙaru da kashi ɗaya da ɗigo bakwai bisa ɗari. Kuma zancen cewa 15,374,986 ne suka halarci Abin Tuni na mutuwar Yesu da ake yi kowace shekara ya nuna cewa akwai aiki mai yawa da za a yi. (1 Korinthiyawa 11:23-26) Bari mu ci gaba da neman masu tawali’u da suke na’am da bishara. Muddin shekara ta alherin Jehovah ta ci gaba, bari mu ci gaba da ba da ta’aziyya ga ‘masu karyayyen zuciya.’ Lallai muna da aiki mai gamsarwa! Hakika dukanmu na maimaita kalmomin Ishaya: “Zan yi farinciki ƙwarai cikin Ubangiji, raina za ya yi murna cikin Allahna.” (Ishaya 61:10) Bari Allah ya ci gaba da yin amfani da mu yayin da yake cika waɗannan kalmomi na annabci: “Ubangiji Yahweh za ya sa adalci da yabo su tsiro a gaban dukan al’ummai.”—Ishaya 61:11.
[Hasiya]
a Taswira a shafuffuka na 29 zuwa 32 ya ba da rahoton aiki na Shaidun Jehovah a shekarar hidima ta 2001.
Ka Tuna?
• Ta yaya ne masu tawali’u suka sami amfani daga bisharar da Yesu ya yi wa’azinsa?
• Waɗanne fa’idodi suka zo ga waɗanda suke na’am da aikin bishara na almajiran Yesu a ƙarni na farko?
• Ta yaya ne waɗanda suke na’am a yau suke samun amfani daga bisharar?
• Ta yaya muke ɗaukan gatarmu na bishara?
[Hoto a shafi na 25]
Ko yaushe Shaidun Jehovah suna tuna da hakkinsu su yi bishara
[Hoto a shafi na 27]
Waɗanda suka yi na’am da bisharar suna zama sashen haɗaɗiyar ’yan’uwanci na dukan duniya