Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 12/1 p. 19
  • “Kin Buga Lambar da ba Daidai Ba”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Kin Buga Lambar da ba Daidai Ba”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Makamantan Littattafai
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Jehobah Yana wa Wadanda Suka Koma Kasarsu Albarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 12/1 p. 19

Rahoto Daga Masu Shelar Mulki

“Kin Buga Lambar da ba Daidai Ba”

A JOHANNESBURG, Afirka ta Kudu, Leslie da Caroline suna canji-canji wajen yin wa’azi da tarho ga mutanen da suka yi murabus da suke zama a wani ƙauye. Mutane kalilan suka samu a lokacin da suke bi gida gida kuma kaɗan suka nuna suna son saƙon Kirista, saboda haka, Caroline ta ji daɗi da wata mata ta amsa.

“Matar B— ce?” Caroline ta yi tambaya.

Murya ta abokanta ta ce, “ayya, a’a, matar G—ce. Kin buga lambar da ba daidai ba.”

Da ta lura da abokantaka da ya fito a muryar, sai Caroline ta ce: “To, bari in yi miki bayanin abin da nake so na gaya wa matar B—.” Sai ta soma magana game da albarkar Mulkin Allah da yake zuwa. Bayan sun shirya ta aiko mata da mujallar nan Minene Allah ke Bukata Daga Garemu?, sai Matar G— ta yi tambaya: “Tsaya tukuna, wane addini kike yi?”

“Mashaidiyar Jehovah ce ni,” in ji Caroline.

“A’a, ba na son wannan addinin! Ban tsammani zan so mu sadu ba.”

“Amma matar G—,” in ji Caroline, “a minti 20 da ya shige, na gaya miki game da bege mai ban mamaki, na nuna miki daga cikin Littafi Mai Tsarki abin da Mulkin Allah zai yi wa ’yan Adam ba da daɗewa ba . Kuma kin yi farin cikin jin waɗannan abubuwa—har da murna—kuma kin so ƙarin bayani. Menene ki ka sani da gaske game da Shaidun Jehovah? Idan ba ki da lafiya, za ki je wajen makanike ne? Me ya sa ba za ki ƙyale ni na gaya miki abin da Shaidun Jehovah suka gaskata ba?”

Bayan ta yi shiru na ɗan lokaci sai ta amsa: “Da gaskiyar ki. Ki zo. Amma fa ki sani, ba za ki iya canja ni ba!”

“Matar G—, ba zan iya canja ki ba ko idan ina son in yi haka,” Caroline ta amsa. “Jehovah ne kaɗai zai iya hakan.”

Ziyarar a ba ta mujalla kome ya je daidai, kuma matar G— (Betty) ta yarda a sake ziyartar ta. Sa’ad da Caroline ta koma, Betty ta ce, ta gaya wa matan da suke cin abinci tare cewa tana tattaunawa tare da Shaidun Jehovah. “Me ya sa?” suka yi tambaya, suka riƙe kwankwasonsu. “Waɗannan mutanen da ba su gaskata ma da Yesu ba!”

Caroline ta tuna wa Betty abin da suka tattauna game da Mulkin Allah babu ɓata lokaci.

“Waye zai zama Sarkin?” Caroline ta yi tambaya.

“A’a, Yesu mana,” Betty ta amsa.

“Hakika,” in ji Caroline. Sai ta ci gaba da bayani cewa Shaidun Jehovah sun gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne, amma ba daidai yake da Allah ba a sashen Allah Uku Cikin Ɗaya.—Markus 13:32; Luka 22:42; Yohanna 14:28.

Bayan ’yan ziyara, ya bayyana sarai cewa ko da yake tana da tabbaci da kuma farin ciki, Betty ba ta da lafiya. Tana da ciwon daji kuma tana tsoron mutuwa. “Da na san waɗannan abubuwa shekaru da yawa da suka shige da kuma bangaskiyarku mana,” in ji ta. Caroline ta ƙarfafa ta ta wajen nuna mata nassosi da suka kwatanta mutuwa da barci mai zurfi da mutum zai iya tashi a lokacin tashin matattu. (Yohanna 11:11, 25) Wannan ya ƙarfafa Betty, wadda yanzu tana nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai. Rashin lafiyarta ne da yake tsanani yake hana ta zuwa taro a Majami’ar Mulki.

Caroline ta ce: “Ya bayyana sarai a gare ni cewa mala’iku suna ja-gorar wannan aikin. Betty ‘lamba ce aka buga da ba daidai ba,’ kuma ka ji, shekararta 89 yanzu!”—Ru’ya ta Yohanna 14:6.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba