Ka Yi Farin Ciki Ka Sami Kuma Kana Samun Sanin Jehovah
“[Masu farin ciki ne] waɗannan da suna jin maganar Allah, suna kiyaye ta kuma.”—LUKA 11:28.
1. Yaushe ne Jehovah ya soma magana da mutane?
JEHOVAH yana ƙaunar mutane kuma yana damuwa da yanayinsu. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne da yake magana da su. Wannan maganar ta soma ne a gonar Adnin. Farawa 3:8, ta ce a wani lokaci “da sanyin yamma,” Adamu da Hauwa’u “suka ji muryar Ubangiji Allah.” Wasu sun ce wai wannan ya nuna cewa al’adar Jehovah ne ya yi magana da Adamu a lokacin, mai-yiwuwa kowacce rana. Ko yaya yake dai, Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa Allah ba kawai yana ba da gargaɗi ga mutum na farko ba amma kuma ya koya masa abin da yake bukata ya sani don ya cika hakkinsa.—Farawa 1:28-30.
2. Ta yaya mata da miji na farko suka ware kansu daga ja-gorar Jehovah, kuma menene sakamakon haka?
2 Jehovah ya ba Adamu da Hauwa’u rai, su mallaki dabobbi, da kuma iko bisa duniya duka. Amma da akwai abu ɗaya da aka haramta—ba za su ci daga itace na sanin nagarta da mugunta ba. Adamu da Hauwa’u suka yi rashin biyayya ga umurnin Allah domin rinjayar Shaiɗan. (Farawa 2:16, 17; 3:1-6) Sun zaɓi su yi abin kansu, suka zaɓi abin da ke nagarta da mugunta wa kansu. Ta haka, suka yi wautar ware kansu daga ja-gorar Mahaliccinsu mai ƙauna. Sakamakon haka bala’i ne a gare su da kuma ’ya’yan da ba su haifa ba tukuna. Daga baya Adamu da Hauwa’u suka tsufa kuma suka mutu, ba su da begen tashi daga matattu. Zuriyarsu suka gaji zunubi da sakamakonsa, mutuwa.—Romawa 5:12.
3. Me ya sa Jehovah ya yi magana da Kayinu, kuma me Kayinu ya yi?
3 Duk da tawayen a Adnin, Jehovah ya ci gaba da magana da halittunsa mutane. Kayinu, ɗan fari na Adamu da Hauwa’u, ya shiga yanayi da zunubi zai yi nasara da shi. Jehovah ya yi masa gargaɗi cewa zai shiga masifa idan “ba ya kyauta ba.” Kayinu ya ƙi wannan gargaɗi mai kyau kuma ya kashe ɗan’uwansa. (Farawa 4:3-8) Ta haka mutane uku na farko a duniya suka yi banza da ja-gora daga wanda ya ba su rai, Allah wanda yake ba da gargaɗi ga mutanensa don su amfani kansu. (Ishaya 48:17) Lalle wannan abin baƙin ciki ne ga Jehovah!
Jehovah Ya Bayyana Kansa ga Mutanen Dā
4. Menene Jehovah ya tabbata game da zuriyar Adamu, kuma domin wannan wane saƙon bege ne ya sanar?
4 Ko da yake yana da ikon ya daina magana da mutane, Jehovah bai yi hakanan ba. Ya tabbata cewa wasu daga cikin zuriyar Adamu za su yi hikima su bi Ja-gorarsa. Alal misali, yayin da yake yanke wa Adamu da Hauwa’u hukunci, Jehovah ya annabta zuwan ‘ɗa’ da zai yi adawa da Macijin, Shaiɗan Iblis. A kwana a tashi, za a yi wa Shaiɗan ƙujewar kisa a kai. (Farawa 3:15) Wannan annabcin saƙon farin ciki ne na bege ga “waɗannan da suna jin maganar Allah, suna kiyaye ta kuma.”—Luka 11:28.
5, 6. A waɗanne hanyoyi ne Jehovah ya yi magana da mutanensa kafin ƙarni na farko A.Z., ta yaya wannan ya amfane su?
5 Jehovah ya sanar da nufinsa ga ubannin iyalai na dā, kamar su Nuhu, Ibrahim, Ishaƙu, Yakubu, da kuma Ayuba. (Farawa 6:13; Fitowa 33:1; Ayuba 38:1-3) Daga baya, ta wurin Musa, ya kafa tsarin doka domin al’ummar Isra’ila. Dokar Musa ta taimake su a hanyoyi da yawa. Ta yin biyayya da ita, Isra’ila ta kasance a ware daga sauran al’ummai, da yake su mutanen Allah ne na musamman. Allah ya tabbatar da Isra’ilawa cewa idan suka yi biyayya ga Dokar, zai yi musu albarka ba a abin duniya kawai ba amma a ruhaniya ma, yana sa su zama mulki na firistoci, al’umma mai tsarki. Dokar ta yi tanadin abubuwan da za a ci da na tsabta da ke kawo lafiyar jiki. Amma, Jehovah ya yi gargaɗi game da bala’in da za ta auku saboda rashin biyayya.—Fitowa 19:5, 6; Kubawar Shari’a 28:1-68.
6 A kwana a tashi, an daɗa wasu littattafai cikin Littafi Mai Tsarki. Tarihi ya faɗi game da yadda Jehovah yake bi da al’ummai da kuma mutane. Littattafan waƙa sun ambata halayensa da kyau. Littattafan annabci kuma sun annabta game da nufin Jehovah a nan gaba. Mutane masu aminci na dā sun yi nazari kuma sun yi amfani da waɗannan hurarun rubuce-rubuce. Wani ya rubuta: “Maganarka fitila ce ga sawayena, haske ne kuma a tafarkina.” (Zabura 119:105) Ga waɗanda suke so su saurara, Jehovah ya yi musu tanadin ilimi da kuma wayewa.
Hasken Yana Ƙara Haskakawa
7. Ko da yake Yesu ya yi mu’ujizai, da me aka fi saninsa, kuma me ya sa?
7 A ƙarni na farko, rukunin addinin Yahudawa sun daɗa al’adun mutane ga Dokar. An ɓata amfanin Dokar, maimakon ta zama abin wayarwa, ta zama kaya domin waɗannan al’adu. (Matta 23:2-4) Amma a shekara ta 29 A.Z., Yesu ya bayyana shi Almasihu. Aikinsa ba kawai domin ya ba da ransa domin mutane ba amma kuma domin ya “bada shaida ga gaskiya.” Ko da yake ya yi mu’ujizai, an fi saninsa da “Malami.” Koyarwarsa tana kama da haske da ya haskaka cikin duhu da ya ƙware azantan mutane. Daidai kuwa Yesu kansa ya ce: “Ni ne hasken duniya.”—Yohanna 8:12; 11:28; 18:37.
8. Waɗanne hurarun littattafai ne aka rubuta a ƙarni na farko A.Z., kuma ta yaya waɗannan suka amfani Kiristoci na farko?
8 Daga baya kuma aka daɗa Lingila, labarai kashi huɗu na rayuwar Yesu, da kuma littafin Ayukan Manzanni, tarihin yaɗuwar Kiristanci bayan mutuwar Yesu. Da akwai kuma hurarun wasiƙu da almajiran Yesu suka rubuta, har da littafin annabci na Ru’ya ta Yohanna. Waɗannan rubuce-rubuce, haɗe da Nassosin Ibrananci suka cika littattafan Littafi Mai Tsarki. Ta wajen taimakon wannan huraren laburare, Kiristoci sun iya sanin “ko menene fāɗin da ratar da tsawon da zurfin” gaskiya. (Afisawa 3:18) Suna iya kasance da “nufin Kristi.” (1 Korinthiyawa 2:16) Duk da haka, waɗancan Kiristoci na farko ba su fahimci sosai dukan fanni na ƙudurin Jehovah ba. Manzo Bulus ya rubuta zuwa ga ’yan’uwa masu bi: “Yanzu cikin madubi mu ke gani a zaurance.” (1 Korinthiyawa 13:12) Irin madubin nan zai nuna abu, amma ba fasalolinsa gabaki ɗaya ba. Kafin a fahimci Kalmar Allah sarai, sai a nan gaba ne.
9. Wane wayewar kai aka samu cikin “kwanaki na ƙarshe”?
9 A yau, muna zama a zamanin da ake kira “kwanaki na ƙarshe,” zamani da “miyagun zamanu” ne ƙwarai masu wuya. (2 Timothawus 3:1) Annabi Daniel ya annabta cewa a wannan lokaci “ilimi za ya ƙaru.” (Daniel 12:4) Shi ya sa, Jehovah, Mai Magana Mai Girma, ya taimake masu zukatan kirki su fahimci ma’anar Kalmarsa. Jama’a mai yawa yanzu suna fahimtar cewa Kristi Yesu ya hau sarauta a sammai da ba a gani a shekara ta 1914. Sun kuma sani cewa ba da daɗewa ba zai kawo ƙarshen dukan mugunta da ke duniya kuma ya mai da duniya ta zama aljanna duka. Wannan muhimmiyar fanni na bisharar Mulkin yanzu ana wa’azinta a dukan duniya.—Matta 24:14.
10. Duk cikin ƙarnuka, yaya ne mutane suka yi game da gargaɗin Jehovah?
10 Hakika, duk cikin tarihi Jehovah ya sanar da nufinsa da ƙudurinsa ga mutane a duniya. Labarin Littafi Mai Tsarki ya ambata mutane da yawa da suka saurara, suka yi amfani da hikima ta Allah, kuma suka sami albarka. Ya faɗa game da wasu da suka ƙi gargaɗi mai kyau na Allah, suka bi tafarkin halaka na Adamu da Hauwa’u. Yesu ya yi misalin yanayin nan yayin da ya yi maganar hanyoyi biyu na alama. Ɗaya tana kai zuwa halaka. Mai fāɗin, wanda mutane da yawa da suka ƙi Kalmar Allah ne suke bi. Ɗayan hanyar kuma tana kai zuwa madawwamiyar rai. Ko da yake matsatsiya ce, ita ce tafarkin kalilan da suka amince da Littafi Mai Tsarki yadda yake, Kalmar Allah, kuma suka yi rayuwa daidai da shi.—Matta 7:13, 14.
Godiya Domin Abin da Muke da Shi
11. Saninmu na Littafi Mai Tsarki da gaskata da shi tabbacin menene ne?
11 Kana cikin waɗanda suka zaɓi hanyar rai? Idan haka ne, lalle za ka so ka ci gaba a hanyar. Ta yaya za ka iya yin haka? Ka yi bimbini a kai a kai a yin godiya domin albarkar da sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki ya kawo cikin rayuwarka. Gaskiyar cewa ka karɓi bishara, tabbacin albarkar Allah ce. Yesu ya nuna wannan yayin da yake addu’a ga Ubansa da kalmomin nan: “Ina yabonka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.” (Matta 11:25) Masunta da masu karɓan haraji suka fahimci koyarwar Yesu, amma masu ilimi sosai shugabannan addini ba su fahimta ba. Yesu ya sake cewa: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yohanna 6:44) Idan ka samu sanin Littafi Mai Tsarki ka gaskata kuma kana bin koyarwarsa, tabbaci ne cewa Jehovah ya jawo ka. Dalili ne na farin ciki.
12. A waɗanne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki yake wayarwa?
12 Kalmar Allah tana ƙunshe da gaskiya mai ’yantarwa mai wayarwa. Waɗanda suke rayuwa daidai da sanin Littafi Mai Tsarki sun ’yantu daga camfi, koyarwar ƙarya, da jahilci da ke mallakar rayuwar miliyoyin mutane. Alal misali, sanin gaskiya game da kurwa tana ɗauke mana tsoron cewa matattu za su iya yin mana lahani ko cewa waɗanda muke ƙauna da suka mutu suna shan wahala. (Ezekiel 18:4) Sanin gaskiya game da miyagun mala’iku ta taimake mu mu guje wa haɗarin sihiri. Koyarwar tashin matattu ta’aziyya ce ga waɗanda suka yi rashin waɗanda suke ƙauna. (Yohanna 11:25) Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki na nuna mana kiɗayar lokaci kuma na ba mu tabbaci game da alkawuran Allah a nan gaba. Suna sake ƙarfafa begenmu na rayuwa har abada.
13. Ta yaya yin biyayya da Kalmar Allah ke amfane mu a jiki?
13 Ƙa’idodin ibada cikin Littafi Mai Tsarki suna koya mana mu yi rayuwa a hanyar da zai kawo mana amfani na jiki. Alal misali, mun koyi mu guji ayyuka da suke ƙazantar da jikunanmu, irinsu shan taba da kuma wasu miyagun ƙwayoyi. Muna guje wa yin maye. (2 Korinthiyawa 7:1) Yin biyayya da dokokin Allah na ɗabi’a kāriya ce daga cututtuka da ake ɗauka daga lalata. (1 Korinthiyawa 6:18) Ta kiyaye gargaɗin Allah cewa mu guje wa son kuɗi, ba ma halaka kwanciyar ranmu yadda mutane da yawa sun yi garin neman arziki. (1 Timothawus 6:10) A waɗanne hanyoyi ne kai ka amfana a jiki domin yin amfani da Kalmar Allah a rayuwanka?
14. Wane tasiri ne ruhu mai tsarki yake da shi cikin rayuwarmu?
14 Idan muka rayu daidai da Kalmar Allah, za mu samu ruhu mai tsarki na Jehovah. Muna koyan halayen Kristi, wanda halaye masu kyau na jinƙai da juyayi suke ciki. (Afisawa 4:24, 32) Ruhun Allah kuma yana sa mu samu ’ya’yansa—ƙauna, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa. (Galatiyawa 5:22, 23) Waɗannan halaye suna kawo dangantaka ta farin ciki kuma mai albarka da wasu, har da kuma waɗanda ke cikin iyali. Muna da kwanciyar rai da ke taimake mu fuskanci wahala tare da gaba gaɗi. Ka fahimci yadda ruhu mai tsarki ya taɓa rayuwanka da kyau?
15. Yayin da muka sa rayuwarmu ta jitu da nufin Allah, yaya muke amfana?
15 Yayin da muka sa rayuwarmu ta jitu da nufin Allah, ƙarfafa dangantakarmu da Jehovah. Sai mu daɗa tabbata cewa yana gane kuma yana ƙaunarmu. Ta abubuwan da suka faru, mun koyi cewa yana toƙara mana a lokatai masu wuya. (Zabura 18:18) Mun fahimci cewa da gaske yana saurarar addu’o’inmu. (Zabura 65:2) Muna dogara ga tsarewarsa, da gaba gaɗin zai amfane mu. Kuma muna da bege mai girma cewa a lokaci na Allah zai kai amintattu zuwa kamilcewa kuma ya ba su kyautar rai na har abada. (Romawa 6:23) “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku,” in ji almajiri Yaƙub. (Yaƙub 4:8) Kana jin cewa dangantakarka da Jehovah ya yi ƙarfi tun da ka matsa kusa da shi?
Dukiya da Babu ta Biyunta
16. Waɗanne canje-canje Kiristoci na ƙarni na farko suka yi?
16 Bulus ya tunasar da Kiristoci shafaffu da ruhu na ƙarni na farko cewa wasu cikinsu dā masu fasikanci ne, mazinata, masu luwaɗi, ɓarayi, masu ƙyashi, masu maye, masu alfasha, da kuma masu ƙwace. (1 Korinthiyawa 6:9-11) Littafi Mai Tsarki ya sa suka yi canje-canje ƙwarai; aka “wanke” su. Ka yi ƙoƙarin ƙaga yadda rayuwarka za ta zama idan babu gaskiyar Littafi Mai Tsarki mai ’yantarwa. Hakika, gaskiya dukiya ce da babu ta biyunta. Dubi yadda muke farin ciki kuwa cewa Jehovah yana magana da mu!
17. Ta yaya ne aka ciyar da Shaidun Jehovah a ruhaniya a taron Kirista?
17 Ban da haka, ka yi tunanin albarka da muke da ita cikin ’yan’uwancinmu na harsuna dabam dabam. “Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” suna tanadin abinci na ruhaniya a kan lokaci, haɗe da Littafi Mai Tsarki, jaridu, da wasu littattafai a harsuna da yawa. (Matta 24:45-47) A taron ikilisiya a shekara ta 2000, Shaidun Jehovah a ƙasashe da yawa sun maimaita muhimman darussa daga littattafai takwas na Nassosin Ibrananci. Sun yi bimbini a kan rayuwar wasu mutane 40 na cikin Littafi Mai Tsarki da aka tattauna daga Insight on the Scriptures. Sun bincika fiye da rabin littafin nan The Greatest Man Who Ever Lived kuma suka yi nazarin Pay Attention to Daniel’s Prophecy! kusan gabaki ɗayansa. Suka tattauna wasu talifai 36 cikin jaridar Hasumiyar Tsaro ban da talifan nazari 52 da aka yi nazarinsu. Ƙari ga wannan, mutanen Jehovah sun sami wartsakewa ta wurin Our Kingdom Ministry guda 12 da kuma jawabai na kowanne mako a kan jigo dabam dabam na Littafi Mai Tsarki. Lalle an yi tanadin sani na ruhaniya mai yawa kuwa!
18. A waɗanne hanyoyi ne aka taimake mu cikin ikilisiyar Kirista?
18 A duk duniya, fiye da ikilisiyoyi 91,000 sun ba da goyon baya da kuma ƙarfafa ta wurin taro da kuma tarayya. Mun kuma more tallafawa na ’yan’uwa masu bi Kiristoci da suka manyanta da suke niyyar taimaka mana a ruhaniya. (Afisawa 4:11-13) Hakika, mun amfana ƙwarai ta samun sanin gaskiya. Abin farin ciki ne a sani kuma a bauta wa Jehovah. Gaskiya ne kalmomin mai Zabura wanda ya rubuta: “Masu-farin zuciya ne mutane, waɗanda [Jehovah] ne Allahnsu.”—Zabura 144:15.
Ka Tuna?
• Su wanene Jehovah ya yi magana da su kafin lokacin Kiristanci?
• Ta yaya haske na ruhaniya ya ƙara haskakawa a ƙarni na farko? a lokatai na zamani?
• Waɗanne albarka ke zuwa daga yin rayuwa daidai da sanin Jehovah?
• Me ya sa muke farin ciki a saninmu na Allah?
[Hotuna a shafi na 20]
Jehovah ya sadar da nufinsa wa Musa, Nuhu, da kuma Ibrahim
[Hoto a shafi na 21]
A kwananmu, Jehovah ya haskaka haske a kan Kalmarsa
[Hotuna a shafi na 22]
Ka yi tunanin albarka da muke da ita cikin ’yan’uwancinmu na harsuna dabam dabam!