Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 12/1 pp. 30-31
  • Ƙungiya ta Dukan Duniya Tana Kula da Juna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙungiya ta Dukan Duniya Tana Kula da Juna
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • ’Yan’uwa Sun Taimaki Waɗanda Suke da Bukata
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 12/1 pp. 30-31

Ƙungiya ta Dukan Duniya Tana Kula da Juna

HAR iyar inda ido ya kai, da mutane. Da yawa tsofaffi ne, wasu naƙasassu ne da da ƙyar ma su yi tafiya. Akwai mata masu juna biyu da sababbin ma’aurata da suke da ƙananan yara. Dukansu ’yan gudun hijira ne—maza, mata, da yara—da yaƙin basasa, tsarar bala’i, ko kuma wasu yanayi suka tilasta su su gudu daga gidajensu su nemi mafaka a ƙasashe da suke maƙwabtaka da su. Wasu a kai a kai an tilasta su su bar mazauninsu. Da sun ga alamar hargitsi ko kuma tsarar bala’i, suka ɗauki wasu kayayyaki, suka tara yaransu, suka nufa wuri mai salama. Lokacin da yanayi ya koma yadda yake dā, ’yan gudun hijira da yawa suka koma su gina gidajensu su soma kuma.

Cikin shekaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta buɗe ƙofofinta ga ’yan gudun hijira daga ƙasashe da yawa. A baya bayan nan, dubban mutane, haɗe da Shaidun Jehovah da yawa, ya zame musu dole su gudu daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyya ta Congo inda ake yaƙi zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda ake da ɗan kwanciyar hankali.

’Yan’uwa Sun Taimaki Waɗanda Suke da Bukata

Shaidu da suke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka ga gata ce su shirya gudummawar su tallafa wa jama’a. An shirya wa ’yan’uwa Kirista da suke isowa masaukai. A farko, an samu ɗakuna a gidajen mutane, amma adadin ’yan gudun hijira ya ƙaru, ya bayyana cewa ana bukatar ƙarin shiri. An juya wasu Majami’ar Mulki zuwa manyan ɗakuna. ’Yan’uwa na yankin suka soma aiki suna ƙara wutar lantarki, suna saka bututun ruwa, kuma suna simintin daɓen don waɗanda za su zauna a wurin su ji daɗin zama. ’Yan gudun hijiran sun yi aiki tare da ’yan’uwan don su kafa waɗannan ɗakuna. An shirya cikakken tsarin taro na Kirista a yaren Lingala don a ba masu isowa abinci na ruhaniya mai rayarwa. Haɗin kai na kurkusa da ke tsakanin Shaidu na yankin da baƙinsu ya nuna cewa ’yan’uwantaka na dukan duniya gaskiya ne.

Iyalan ’yan gudun hijiran ba koyaushe ba ne suke zuwa tare. Wasu lokatai, waɗanda suke cikin iyali da suka rabu suna sake haɗuwa ne a masaukinsu. Sunayen waɗanda suka isa lafiya ana ajiyewa a kowacce Majami’ar Mulki. An shirya a nemi waɗanda har ila ba a gansu ba. Ofishin reshe da ke ja-gorar aikin Shaidun Jehovah a ƙasar suna aika da motoci uku kowacce rana don su taimaki Shaidu da suke kan hanya kuma su nemi waɗanda suka ɓata. Ana gane waɗannan motoci da babbar alama, da aka rubuta “WATCH TOWER—Jehovah’s Witnesses.”

Ka yi tunanin farin cikin wasu yara bakwai ’yan gudun hijira da suka rabu da iyayensu sa’ad da suka ga motar Shaidun Jehovah. Suka gudu nan da nan zuwa wajen motar kuma suka gabatar da kansu su Shaidu ne. ’Yan’uwan suka taimake su shiga motar kuma aka kai su Majami’ar Mulki, inda suka sake haɗuwa da iyalansu.

Menene ya taimake waɗannan sahihan Kiristoci su jimre wa irin wannan yanayi, ba sau ɗaya ba, amma a kai a kai? Sun tabbata cewa muna cikin kwanaki na ƙarshe yadda aka annabta cikin Nassosi Masu Tsarki.—2 Timothawus 3:1-5; Ru’ya ta Yohanna 6:3-8.

Saboda haka, sun san cewa ba da daɗewa ba Jehovah Allah zai kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe, ƙiyayya, mugunta, da jayayya. Matsalar gudun hijira za ta zama aba da ta shige. A yanzu dai, cikin jituwa da gargaɗin manzo Bulus a 1 Korinthiyawa 12:14-26, Shaidun Jehovah suna ƙoƙari su kula da juna. Ko da koguna, iyaka, yare, sun raba su kuma tsakaninsu da nisa, suna damuwa da juna, saboda haka suke saurin tallafawa yayin da wani yake da bukata.—Yaƙub 1:22-27.

[Taswira a shafi na 30]

AFIRKA

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Jamhuriyar Dimokuraɗiyya ta Congo

[Inda aka Dauko]

Mountain High Maps® Hakkin Wallafawa © 1997 Digital Wisdom, Inc.

[Hotuna a shafi na 30]

An juya Majami’un Mulki uku zuwa inda ake marabtar mutane

[Hoto a shafi na 31]

An gina madafa nan da nan

[Hoto a shafi na 31]

’Yan gudun hijira da yawa sun iso

[Hoto a shafi na 31]

Sababbin haihuwa amma sun riga sun zama ’yan gudun hijira

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba