Masu Kula Da Kuma Bayi Masu Hidima Allah Ne Ya Naɗa Su
“Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula.”—AYYUKAN MANZANNI 20:28.
1, 2. Ta yaya Ishaya 60:22 yake samun cika?
TUN da daɗewa Jehovah ya annabta cewa abu na musamman zai faru a zamanin ƙarshe. Ta annabi Ishaya, an faɗa: “Har ma da iyalin da suka fi ƙanƙanta da ƙasƙanci, Za su zama babbar al’umma, Kamar al’umma mai iko. Zan sa wannan ya faru nan da nan sa’ad da lokacin da ya dace ya yi. Ni ne Ubangiji!”—Ishaya 60:22.
2 Akwai tabbaci ne cewa wannan annabci yana samun cika a yau? Hakika kuwa! Cikin shekarun 1870, an kafa ikilisiya ta mutanen Jehovah guda a Allegheny, Pennsylvania, U.S.A. Daga wannan ƙaramin somawar, dubban ikilisiyoyi sun fito kuma suna cin gaba a duniya duka. Dubban masu shelar Mulki—babbar al’umma—yanzu tana tarayya cikin fiye da ikilisiyoyi 91,000 a sama da ƙasashe 235 a dukan duniya. Babu shakka, wannan ya nuna cewa Jehovah yana hanzarta tattara masu bauta ta gaskiya kafin ɓarkewan “matsananciyar wahala,” da ta kusa yanzu sosai.—Matiyu 24:21; Wahayin Yahaya 7:9-14.
3. Menene yake nufi a yi baftisma ‘a sunan Uba, da Ɗa, da ruhu mai tsarki’?
3 Bayan sun keɓe kansu ga Jehovah, cikin jituwa da umurnin Yesu, waɗannan miliyoyi sun yi baftisma “da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki.” (Matiyu 28:19) Baftisma “da sunan Uba” na nufin waɗannan mutane da suka keɓe kansu sun amince Jehovah shi ne Ubansu na samaniya, Mai Ba da Rai kuma suna biyayya da ikonsa na mallaka. Baftisma cikin ‘sunan Ɗa’ na nuna cewa sun amince Yesu Kristi ne Mai Fansarsu, Shugaba, da kuma Sarki. Sun kuma yarda da matsayin ruhu mai tsarki na Allah, ko kuma ikon aiki ya ja-goranci rayuwarsu. Wannan ya nuna cewa sun yi baftisma ‘cikin sunan ruhu mai tsarki.’
4. Yaya ake naɗa masu hidima Kirista?
4 Lokacin baftismarsu, sababbin almajirai an naɗa su masu hidima na Jehovah Allah. Wanene ke naɗa su? Cikin ƙa’ida, kalmomi da ke rubuce a 2 Korantiyawa 3:5 suna faruwa kansu: “Iyawarmu [na masu hidima] daga Allah take.” Babu ɗaukaka mafi girma da za su iya samu fiye da Jehovah Allah kansa ya naɗa su! Bayan baftismarsu, za su ci gaba da girma a ruhaniya, su masu hidima na “bisharan” muddin sun amince da ja-gorar ruhun Allah kuma sun ci gaba da amfani da Kalmarsa.—Matiyu 24:14; Ayyukan Manzanni 9:31.
Naɗi—Na Tsarin Allah—Ba na Dimokuraɗiyya Ba
5. Ta tsarin dimokuraɗiyya ne ake zaɓan masu lura Kirista da kuma bayi masu hidima? Ka ba da bayani.
5 Ana bukatar kula mai kyau na ƙwararrun masu kula da kuma taimakon bayi masu hidima don a kula da bukatu na ruhaniyar adadin masu hidima da ƙwazo da ke ƙaruwa. (Filibiyawa 1:1) Yaya ake naɗa irin waɗannan maza masu ruhaniya? Ba yadda Kiristendam suke yi ba. Alal misali, ba a zaɓan masu kula Kirista ta tsari na dimokuraɗiyya, wato, ta cin zaɓe da yawancin mutane da suke ikilisiya suka jefa wa ƙuri’a. Maimako, ana yin waɗannan naɗi daidai da tsari na Allah. Menene wannan ke nufi?
6. (a) Menene tsarin gaske na Allah? (b) Me ya sa ake bin tsarin Allah wajen naɗa masu kula da kuma bayi masu hidima?
6 A sauƙance, tsari na gaske na Allah, sarautar Allah ce. Shaidun Jehovah da yardan rai suke biyayya ga sarautarsa kuma suke ba da haɗin kai don su yi nufin Allah. (Zabura 143:10; Matiyu 6:9, 10) Naɗa masu kula Kirista, da kuma bayi masu hidima ta tsarin Allah ne domin yadda ake yabawa kuma a naɗa irin waɗannan maza daidai yake da yadda Allah ya tsara cikin Nassosi Masu Tsarki. Da yake shi ne “Maɗaukaki duka,” Jehovah yana da iko ya tsai da ƙa’idar yadda ƙungiyarsa da ake gani za ta yi aiki.—1 Tarihi 29:11; Zabura 97:9.
7. Ta yaya ake ja-gorancin Shaidun Jehovah?
7 Dabam da rukunin addinai da yawa na Kiristendam, Shaidun Jehovah ba sa tsai da shawarar kansu game da irin tsari na ruhaniya da za su yi aiki a ƙarƙashinsa. Waɗannan sahihan Kiristoci suna ƙoƙari su manne wa mizanan Jehovah. Ba a saka masu kula cikinsu a matsayi na wasu ikilisiya, tsarin gado, ko kuma irin na presbyteria ta gwamnatin cocin. Idan halin duniya yana neman shiga waɗannan naɗi, mutanen Jehovah suna ƙin karya ƙa’ida. Da aminci, suna riƙe matsayin da manzanni suka furta a ƙarni na farko yayin da suka ce: “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.” (Ayyukan Manzanni 5:29) Saboda haka, Shaidu suna miƙa kansu ga Allah a dukan abu. (Ibraniyawa 12:9; Yakubu 4:7) Bin tsarin Allah yana kawo amincewa na Allah.
8. Ta yaya matakai na dimokuraɗiyya da na tsarin Allah suka bambanta?
8 Da yake mu bayin Mai Sarauta Mai Girma, Jehovah ne, yana da kyau mu tuna bambanci tsakanin dimokuraɗiyya da ƙa’idodi na tsarin Allah. Dimokuraɗiyya tana bukatar mutane da za su tsaya a madadin mutumin, kuma sau da yawa ana kamfen don matsayi da samun zaɓe wajen yawanci da suka jefa ƙuri’ar. Ba a bin irin waɗannan matakai a naɗi na tsarin Allah. Waɗannan ba sa zuwa daga mutane; ko kuwa daga wasu mutane na doka. Hakika yana nuni ga naɗa shi da Yesu da kuma Jehovah suka yi ya zama “manzo ne ga al’ummai,” Bulus ya gaya wa Galatiyawa cewa an naɗa shi “ba kuwa manzon mutum ba, ba kuma ta wurin wani mutum ba, sai dai ta wurin Yesu Almasihu, da Allah Uba, wanda ya tashe shi daga matattu.”—Romawa 11:13; Galatiyawa 1:1.
Naɗi ta Ruhu Mai Tsarki
9. Menene Ayyukan Manzanni 20:28 ya ce game da naɗi na masu kula Kirista?
9 Bulus ya tunasar wa masu kula da suke zama a Afisus cewa Allah ne ya naɗa su ta wurin ruhu mai tsarki. Ya ce: “Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jinin[Ɗansa].” (Ayyukan Manzanni 20:28) Waɗannan masu kula Kirista suna bukatar ruhu mai tsarki ya ci gaba da ja-gorarsu yayin da suke aikinsu na makiyayan garken Allah. Idan wani mutum da aka naɗa ba ya cika mizanan Allah, da shigewar lokaci ruhu mai tsarki zai sa a cire shi daga matsayinsa.
10. Yaya ne ruhu mai tsarki yake da matsayi mai muhimmanci a naɗi na tsarin Allah?
10 Yaya ruhu mai tsarki yake da matsayi da yake da muhimmanci? Na farko, ruhu mai tsarki ne ya hure rubutu da ya tsara farillai na aikin kulawa ta ruhaniya. A wasiƙunsa zuwa ga Timoti da Titus, Bulus ya tsara mizanai da masu kula da bayi masu hidima za su cika. A duka duka, ya ambata farillai 16 dabam dabam. Alal misali, masu kula za su zama marar abin zargi, masu kamunkai, natsattsu, kintsattsu, masu yi wa baƙi alheri, masu gwanin koyarwa, da kuma magidanta da suke abin koyi ne. Ba za su zama mashaya ba, ba kuwa masu son kuɗi ba, kuma za su nuna kamewa. Hakanan ma, an kafa irin waɗannan mizanai masu girma ga maza masu burin aikin bayi masu hidima.—1 Timoti 3:1-10, 12, 13; Titus 1:5-9.
11. Menene wasu farillai da dole maza masu burin nawayar ikilisiya za su cika?
11 Sake bincika waɗannan farillai ya nuna cewa waɗanda suke shugabanci a bautar Jehovah dole ne su zama abin koyi wajen halayen Kirista. Maza da suke burin kula da ikilisiya dole ne su ba da tabbaci cewa ruhu mai tsarki yana aiki cikinsu. (2 Timoti 1:14) Dole ne ya zama a bayyane cewa ruhun Allah yana ba da ’ya’ya “ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci, da tawali’u da kuma kamunkai” a cikin waɗannan maza. (Galatiyawa 5:22, 23) Irin ’ya’yan nan su zama a bayyane a cikin sha’aninsu da ’yan’uwa masu bi da kuma wasu. Hakika, wasu mai yiwuwa sun gwanance a nuna wasu ’ya’yan ruhu, yayin nan kuma wasu za su cika wasu farillai na masu kula a mafificin hanya. Amma, a tafarkinsu na rayuwa, duka waɗanda suke sa rai su zama masu kula ko bayi masu hidima ya kamata su nuna su maza ne masu ruhaniya, suna cika farillai na Kalmar Allah.
12. Su wanene ake iya cewa ruhu mai tsarki ne ya naɗa su?
12 Lokacin da Bulus ya gargaɗi wasu su yi koyi da shi, ya faɗi haka a sake domin shi kansa ya yi koyi da Yesu Kristi, wanda ‘ya bar mana gurbi mu bi hanyarsa a tsanake.’ (1 Bitrus 2:21; 1 Korantiyawa 11:1) Waɗanda suke cika farillai na Nassi a lokacin da aka naɗa su masu kula ko bayi masu hidima ana iya ce ruhu mai tsarki ne ya naɗa su.
13. Yaya ruhu mai tsarki yake taimakon waɗanda suke yin shawarar danƙa wa mutane aiki cikin ikilisiya?
13 Akwai wani abu da ke nuna yadda ruhu mai tsarki yake aiki a yabawa da kuma a naɗa masu kula. Yesu ya ce ‘Uba na sama yana ba da ruhu mai tsarki ga masu roƙonsa.’ (Luka 11:13) Saboda haka, yayin da dattawa cikin ikilisiya suka haɗu su danƙa wa wasu maza hakkin ikilisiya, suna addu’a don ruhun Allah ya ja-gorance su. Suna danƙa aikin bisa abin da aka faɗa cikin hurarren Kalmar Allah, kuma ruhu mai tsarki yana taimakonsu su gane ko mutumin da ake so a naɗa ya cika farillai na Nassi. Bai kamata yadda mutum yake a waje, iliminsa na makaranta, ko iyawarsa su rinjayi waɗanda suke danƙa wa wani aiki ba. Za su mai da hankali musamman ga ko mutumin mai ruhaniya ne, wanda waɗanda suke cikin ikilisiya za su iya zuwa wurinsa da sauƙi don shawara ta ruhaniya.
14. Menene muka koya daga Ayyukan Manzanni 6:1-3?
14 Gaskiya ne cewa rukunin dattawa tare da masu kula masu ziyara suke danƙa wa ’yan’uwa da za su yi hidima na dattawa da bayi masu hidima, ana yin naɗi na ainihi yadda aka kafa a ƙarni na farko. A wani lokaci, ana bukatar maza masu ruhaniya da sun ƙware su kula da wata muhimmiyar aiki. Hukumar mulki ta ba da bayani na biye: “Ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku, waɗanda ake yabawa, cike da Ruhu da kuma hikima, waɗanda za mu danƙa wa wannan aiki.” (Ayyukan Manzanni 6:1-3) Yayin da mutane da suke wurin ne suke yabo, maza da aka ba su hakki a Urushalima ne suke naɗin. Ana bin wannan tafarkin ma a yau.
15. Ta yaya Hukumar Mulki take cikin batun naɗa mutane?
15 Hukumar Mulki ta Shaidun Jehovah ne suke naɗa dukan waɗanda suke cikin Kwamiti na Rassa. Yayin da ake tsai da shawarar wanda za a ba irin wannan hakki mai girma, Hukumar Mulki tana tuna furcin Yesu: “Wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.” (Luka 12:48) Ƙari ga naɗa Kwamiti na Reshe, Hukumar Mulki tana naɗa dattawan Bethel da masu kula masu ziyara. Amma, suna ba ’yan’uwa da aka amince da su su yi wasu naɗin. Akwai misali a Nassi game da wannan ma.
‘Ka Yi Naɗi, Kamar Yadda na Nushe Ka’
16. Me ya sa Bulus ya bar Titus a Karita, kuma menene wannan ya nuna game da naɗi na tsarin Allah a yau?
16 Bulus ya gaya wa abokin aikinsa Titus: “Wannan shi ya sa na bar ka a Karita, musamman domin ka ƙarasa daidaita al’amuran da suka saura, ka kuma kafa dattawan ikilisiya a kowane gari, kamar yadda na nushe ka.” (Titus 1:5) Sa’an nan Bulus ya tsara farillai da Titus zai duba wajen maza da za su inganta don irin wannan naɗi. Saboda haka, a yau, Hukumar Mulki ta danƙa wa ’yan’uwa da suka inganta a rassa su zama wakilinta su naɗa dattawa da bayi masu hidima. Ana tabbatar da cewa waɗanda suke aiki a madadin Hukumar Mulki sun fahimci sarai kuma suna bin ƙa’idodi na Nassi don irin waɗannan naɗi. Saboda haka, ta ja-gorancin Hukumar Mulki ne ake naɗa maza da suka inganta su yi hidima cikin ikilisiyoyi na Shaidun Jehovah a duniya duka.
17. Yaya ake tsai da shawara don naɗa masu kula da kuma bayi masu hidima a ofishin reshe?
17 Yayin da aka aika wa ofishin reshe na Watch Tower Society takarda na waɗanda aka shawarta a naɗa su dattawa da kuma bayi masu hidima, maza da suka ƙware suna dogara ga ruhun Allah don ja-gora a yin naɗin. Waɗannan maza sun san za su ba da lissafi, sun fahimci cewa bai kamata su yi garajen ɗora wa kowane mutum hannu ba, in ba haka ba zunubansa za su shafe su.—1 Timoti 5:22.
18, 19. (a) Yaya ake aika wasu naɗi? (b) Yaya ake tafiyar da duk shiri na yabawa da kuma naɗi?
18 Za a iya aika wasu naɗin ta wajen wasiƙa da aka buga mata tambari daga hukuma ta ƙasa. Za a iya yin amfani da irin wannan wasiƙar a naɗa fiye da ɗan’uwa guda cikin ikilisiyar.
19 Naɗi na tsarin Allah yana zuwa daga Jehovah ta Ɗansa da kuma hanyar sadarwa na Allah da ake gani a duniya, “amintaccen bawan nan mai hikima” da Hukumar Mulkinta. (Matiyu 24:45-47) Hanyar yabawa da kuma naɗi, ruhu mai tsarki ne ke ja-gorarta. Haka yake saboda farillan a cikin Kalmar Allah suke, wadda ruhu mai tsarki ya hure, kuma mutumin da aka naɗa ya ba da tabbacin yana da ruhu mai tsarki ta wajen nuna ’ya’yan ruhun. Saboda haka, ake ɗauka cewa naɗin ruhu mai tsarki ne ya yi. Yadda ake naɗa masu kula da kuma bayi masu hidima ta tsarin Allah a ƙarni na farko, haka ake yi a yau.
Yi Godiya ga Ja-gorancin Jehovah
20. Me ya sa muke irin farin zuciyar Dauda da ke rubuce a Zabura 133:1?
20 A wannan lokaci na ni’ima a ruhaniya da ƙaruwar tsarin Allah a aikin wa’azin Mulki, muna godiya cewa Jehovah yana da hannu wajen naɗa masu kula da kuma bayi masu hidima. Tsari na Nassi yana taimakawa wajen riƙe mizanan adalci na Allah masu girma tsakaninmu Shaidun Jehovah. Ƙari ga haka, hali na Kirista da ƙoƙarce-ƙoƙarce na ƙwarai na waɗannan maza suna sa mu kasance da salama da kuma haɗin kai mu bayin Jehovah. Kamar mai Zabura Dauda, mun motsa mu furta: “Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, ga jama’ar Allah su zauna tare kamar ’yan’uwa!”—Zabura 133:1.
21. Yaya Ishaya 60:17 yake cika a yau?
21 Muna godiya don ja-gorar Jehovah ta Kalmarsa da kuma ruhunsa mai tsarki! Hakika, kalmomi da ke rubuce a Ishaya 60:17 suna da ma’ana sosai: “Zan kawo miki zinariya maimakon tagulla, Azurfa maimakon baƙin ƙarfe, Tagulla kuma maimakon itace. Za ki sami baƙin ƙarfe maimakon dutse. Masu mulkinki ba za su ƙara zaluntarki ba, Zan sa su yi mulki da gaskiya da salama.” Yayin da ake cin gaba da amfani sosai da ƙa’idodi na tsarin Allah tsakanin Shaidun Jehovah, mun ga wannan yanayin albarka a duk cikin ƙungiyar Allah ta duniya.
22. Menene muke farin cikinsa, kuma me ya kamata mu ƙudura aniyyar yi?
22 Muna godiya sosai ga tsarin Allah da akwai tsakaninmu. Kuma muna farin ciki a aiki mai wuya da mai gamsarwa da masu kula da bayi masu hidima da aka naɗa ta tsarin Allah suke yi. Da dukan zuciyarmu muna ɗaukaka Ubanmu na samaniya mai ƙauna, wanda ya ba mu ni’ima ta ruhaniya kuma ya albarkace mu sosai. (Karin Magana 10:22) Saboda haka, bari mu ƙuduri aniyyar ci gaba da bin ƙungiyar Jehovah. Fiye da kome, bari mu ci gaba da bauta tare da haɗin kai ga ɗaukaka, yabo, da kuma darajar sunan Jehovah mai girma kuma mai tsarki.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa za mu faɗi cewa naɗi na masu kula da kuma bayi masu hidima na tsarin Allah ne, ba na dimokuraɗiyya ba?
• Ta yaya ruhu mai tsarki yake naɗa maza Kirista da suka inganta?
• Ta yaya Hukumar Mulki take cikin batun naɗi na masu kula da kuma bayi masu hidima?
• Game da naɗi na tsarin Allah, me ya sa ya kamata mu yi godiya ga Jehovah?
[Hotuna a shafi na 6]
Dattawa da bayi masu hidima suna da gatar yin hidima ta naɗi na tsarin Allah