Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 11/1 pp. 24-29
  • Za Ka Iya Kasancewa Da Ɗabi’a Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Kasancewa Da Ɗabi’a Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gina Gaskatawa ta Ƙwarai
  • Abubuwa da Suke Kai wa ga Lalata
  • Koya Daga Zunuban Dauda
  • Jure wa Sakamakon Zunubi
  • Ana Samun Farin Ciki Daga Bauta wa Jehovah Ne
  • Ka Dogara Ga Ruhun Allah Sa’ad Da Kake Fuskantar Canji A Yanayin Rayuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Zunubin Sarki Dauda
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Za Mu Iya Kasancewa da Dabi’a Mai Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • “Ku Guje Wa Halin Lalata!”
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 11/1 pp. 24-29

Za Ka Iya Kasancewa Da Ɗabi’a Mai Tsarki

“Domin ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa.”—1 YAHAYA 5:3.

1. Wane bambanci ne a ɗabi’a ake gani a tsakanin mutane a yau?

DA DAƊEWA, aka hure annabi Malakai ya annabta lokacin da halayen mutanen Allah za su bambanta ƙwarai daga na mutanen da ba sa bauta wa Allah. Annabin ya rubuta: “Sa’an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da ke bauta mini da wanda ba ya bauta mini.” (Malakai 3:18) Wannan annabcin yana cika a yau. Kiyaye umurnan Allah, har da waɗanda suke bukatar ɗabi’a mai tsarki, hikima ce kuma ita ce daidaicacciyar hanyar rayuwa. Duk da haka, ba hanya ba ce da kullum take da sauƙi. Don kakkauran dalili, Yesu ya ce Kiristoci za su yi fama sosai domin su samu tsira.—Luka 13:23, 24.

2. Wane matsi ne daga waje ya sa yake da wuya wasu su riƙe tarbiyya mara aibi?

2 Me ya sa yake da wuya a riƙe tarbiyya mara aibi? Dalili guda shi ne da akwai matsi daga waje. Kamfanin nishaɗi suna nuna fasikanci abu ne mai kyau, mai daɗi, kuma manyanta ne, yayin da kuma suke ƙyale mummunar abin da yake jawowa. (Afisawa 4:17-19) Yawancin irin waɗannan jima’i da ake nunawa a tsakanin mace da miji ne da ba aure suka yi ba. Sau da yawa a silima da telibijin ana nuna jima’i a yanayi da babu wani abu a tsakanin mutane biyun. Hakika, ba a samun ƙauna da kuma daraja ciki. Mutane da yawa suna ganin irin wannan saƙon tun suna ’yan yara. Bugu da ƙari, da akwai matsi ƙwarai daga wajen tsara don mutum ya daidaita da ɗabi’a irin ta yau, waɗanda ba su yi ba wasu lokatai an yi musu ba’a ko ma a gatse su.—1 Bitrus 4:4.

3. Waɗanne dalilai ne ya sa mutane da yawa a duniya suke lalata?

3 Matsi daga ciki ma yana sa ya yi wuya a riƙe tarbiyya mara aibi. Jehovah ya halicci mutane da sha’awar jima’i, kuma sha’awar takan yi ƙarfi sosai. Sha’awa tana shafan abin da muke tunaninsa, kuma lalata ta haɗa da abin da muke tunani da bai jitu da tunanin Jehovah ba. (Yakubu 1:14, 15) Alal misali, in ji wani bincike da aka yi a baya bayan nan da aka buga a cikin British Medical Journal, da yawa da suka yi jima’insu na farko don kawai wai suna so su san yadda jima’i yake ne. Wasu sun gaskata cewa tsaransu suna yin jima’i, saboda haka su ma suke so su yi. Har ila, wasu suka ce sha’awarsu ce ta kwashe musu hankali ko kuma sun “ɗan bugu ne a lokacin.” Idan muna so mu faranta wa Allah rai, to, dole tunaninmu ya bambanta. Wane irin tunani ne zai taimake mu mu riƙe ɗabi’a mai tsarki?

Gina Gaskatawa ta Ƙwarai

4. Don mu riƙe tarbiyya mara aibi, menene dole mu yi?

4 Don a riƙe tarbiyya mara aibi, dole ne mu fahimci cewa bin irin wannan rayuwar ta cancanta. Wannan ya jitu da abin da manzo Bulus ya rubuta zuwa ga Kiristoci a Roma: “Ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.” (Romawa 12:2) Fahimtar cewa ɗabi’a mai tsarki tana da kyau, ya wuce sanin cewa Allah ya haramta lalata kawai a cikin Kalmarsa. Ya ƙunshi gane dalilan da suka sa aka haramta lalata da kuma yadda muke amfana daga guje mata. Wasu cikin waɗannan dalilan mun bincika su a talifi na baya.

5. Ainihi, me ya sa Kiristoci suke so su riƙe tarbiyya mara aibi?

5 Hakika, ga Kiristoci dalili mafi ƙwari na guje wa lalatar jima’i daga dangantakarmu da Allah ne. Mun koya cewa ya san abin da ya fi kyau dominmu. Ƙaunar da muke masa za ta sa mu ƙi abin da ba shi da kyau. (Zabura 97:10) Allah shi ne mai Bayar da “kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta.” (Yakubu 1:17) Yana ƙaunarmu. Ta wajen yi masa biyayya, muna nuna cewa muna ƙaunarsa kuma muna godiya saboda dukan abin da ya yi mana. (1 Yahaya 5:3) Ba ma so mu ba Jehovah kunya kuma mu sa shi baƙin ciki ta wajen taka umurninsa na adalci. (Zabura 78:41) Ba ma so mu yi abin da zai sa a zagi hanyar bauta masa mai tsarki kuma mai adalci. (Titus 2:5; 2 Bitrus 2:2) Ta wajen riƙe tarbiyya mara aibi mu sa Maɗaukaki Duka farin ciki.—Karin Magana 27:11.

6. Ta yaya yake taimako ka gaya wa wasu ɗabi’ar da ka ke bi?

6 Da zarar mun tsai da shawarar za mu riƙe tarbiyya mara aibi, abin da zai sake kāre mu shi ne mu gaya wa wasu abin da muka gaskata. Ka gaya wa wasu kai bawan Allah Jehovah ne kuma ka ƙuduri aniyyar ka riƙe mizanai masu girma. Rayuwarka ce, jikinka ne, kuma zaɓenka ne. Me ke cikin haɗari? Dangantakarka mai tamani da Ubanka na samaniya. Saboda haka ka fayyace cewa nacewanka ga ɗabi’a mai tsarki ba abin da za a yi jayayyarsa ba ne. Ka yi fahariyar ɗaukaka mizanan Allah. (Zabura 64:10) Kada ka ji kunyar tattauna abin da ka gaskata game da ɗabi’a tare da wasu. Magana da gaba gaɗi zai ƙarfafa ka, zai kāre ka, kuma zai ƙarfafa wasu su yi koyi da kai.—1 Timoti 4:12.

7. Ta yaya za mu ci gaba da ƙudurinmu na riƙe tarbiyya mara aibi?

7 Na gaba, bayan mun ƙuduri aniyyar mu riƙe mizanan ɗabi’a masu kyau kuma muka gaya wa wasu, dole ne mu nace wa ƙudurinmu. Hanya ɗaya da za mu yi haka ita ce ta mayar da hankali yayin da muke zaɓan waɗanda za mu yi abota da su. “Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima,” in ji Littafi Mai Tsarki. Ka yi abota da waɗanda suke da irin naka ɗabi’a; za su ƙarfafa ka. Nassin kuma ya ce: “Yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.” (Karin Magana 13:20) Yadda zai yiwu, ka guje wa mutane da za su raunana ƙudurinka.—1 Korantiyawa 15:33.

8. (a) Me ya sa za mu cika zukatanmu da abubuwa masu kyau? (b) Menene ya kamata mu guje wa?

8 Ƙari ga haka, muna bukatar mu cika zukatanmu da abubuwa da suke na gaskiya, na girmamawa, na daidai, na tsattsarka, abin ƙauna, na daddaɗar magana, abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo. (Filibiyawa 4:8) Za mu yi haka ta zaɓan abin da muke kallo, da kuma karatu da waƙe-waƙe da muke sauraro. A ce littattafai da ba su da kyau ba sa lalatarwa kusa ne da cewa littattafan koyar da ɗabi’a ba sa gyara. Ka tuna, mutane ajizai ba wuya su faɗa cikin lalata. Saboda haka, mujallu, fim, da waƙe-waƙe da suke ƙarfafa sha’awar jima’i za su kai ga muguwar sha’awa, kuma wannan a ƙarshe zai kai ga zunubi. Don mu riƙe ɗabi’a mai kyau, dole ne mu cika zukatanmu da hikima ta Allah.—Yakubu 3:17.

Abubuwa da Suke Kai wa ga Lalata

9-11. Kamar yadda Sulemanu ya ba da labari, waɗanne abubuwa suka kai wani saurayi cikin lalata?

9 Sau da yawa, akwai matakai da suke kai wa ga lalata da za a iya gane su. Kowanne ne da aka ɗauka zai sa koma baya ta yi wuya. Ka lura da yadda aka kwatanta wannan a Karin Magana 7:6-23. Sulemanu ya lura da ‘saurayi da bai gogu da duniya ba,’ ko kuma bai da nufin kirki. Saurayin “yana tafe a kan titi kusa da kusurwar da [karuwa] take a zaune, yana wucewa kusa da gidanta, da magariba cikin duhu.” Wannan shi ne kuskurensa na farko. A cikin duhun magariba ne, ‘zuciyarsa’ ta tura shi, ba kawai kowane titi ba, amma inda ya san cewa za a tarar da karuwa ko yaushe.

10 Mun karanta kuma: “Sai ta tarye shi, ta ci ado kamar karuwa, ta shirya yadda za ta yaudare shi.” Yanzu ya gan ta! Zai iya juyawa ya koma gida, amma hakan ya yi wuya fiye da dā, musamman ma tun da ya raunana a ɗabi’a. Ta rungume shi ta sumbace shi. Bayan ya karɓi sumba, sai ya saurari rinjayarta: “Na miƙa hadayu yau,” in ji ta. ‘Yau na cika alkawarina.’ Hadayu na sama ya haɗa da nama, gari, mai, da kuma giya. (Littafin Firistoci 19:5, 6; 22:21; Littafin Ƙidaya 15:8-10) Da ta faɗi wannan, wataƙila tana nuna cewa tana da ruhaniya, kuma wataƙila tana gaya masa cewa tana da abinci mai yawa na ci da kuma na sha a gidanta. “Ka zo,” ta gayyace shi, “mu sha daɗin ƙauna, mu more dukan dare, mu yi farin ciki rungume da juna.”

11 Abin da zai biyo baya ba shi da wuya a sani. “Sai ya ba da kai ga daɗin bakinta.” Ya bi ta zuwa gida “kamar sā zuwa mayanka” kuma kamar “tsuntsun da yake zuwa cikin tarko.” Sulemanu ya kammala da kalmomin ban tausayi: “Bai kuwa sani ransa yana cikin hatsari ba.” Ransa yana cikin hatsari domin “fasikai da mazinata Allah zai hukunta su.” (Ibraniyawa 13:4) Babban darasi ne ga maza da mata! Ya kamata mu guje wa ɗaukan mataki na farko a kan hanyar da take kai wa ga rashin tagomashin Allah.

12. (a) Me ake nufi da furcin nan ‘bai gogu da duniya ba’? (b) Ta yaya za mu gina ɗabi’a mai ƙarfi?

12 Ka lura cewa saurayin cikin labarin bai “gogu da duniya ba.” Wannan furcin ya gaya mana cewa tunaninsa, sha’awarsa, soyayyarsa, motsin zuciyarsa, da kuma burinsa a rayuwa ba su jitu da abin da Allah ya yarda da shi ba. Raunanarsa a ɗabi’a ta kai ga bala’i. A waɗannan “zamanin ƙarshe,” masu wuya ƙwarai yana bukatar ƙoƙari a gina ɗabi’a mai ƙarfi. (2 Timoti 3:1) Allah ya yi tanadi ya taimake mu. Ya yi tanadin taro na ikilisiyar Kirista don ya ƙarfafa mu a kan hanya da take daidai kuma ya gama mu da mutane da suke da irin burin da muke da shi. (Ibraniyawa 10:24, 25) Da akwai dattawan ikilisiya waɗanda suke kiwonmu suke koyar da mu hanyoyin adalci. (Afisawa 4:11, 12) Muna da Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, don ta yi mana ja-gora. (2 Timoti 3:16) A dukan lokaci, muna da zarafin mu yi addu’a domin ruhun Allah ya taimake mu.—Matiyu 26:41.

Koya Daga Zunuban Dauda

13, 14. Ta yaya Sarki Dauda ya faɗa cikin mummunar zunubi?

13 Abin baƙin ciki, har fitattun bayin Allah sun faɗa cikin lalatar jima’i. Ɗaya cikin waɗannan Sarki Dauda ne, wanda ya bauta wa Jehovah na shekaru da yawa cikin aminci. Babu tantama cewa yana ƙaunar Allah ƙwarai da gaske. Duk da haka, ya faɗa cikin zunubi. Kamar na saurayin da Sulemanu ya kwatanta, da akwai abubuwa da suka kai Dauda ga zunubi da ya cika su.

14 Dauda ya ɗan manyanta, wataƙila a cikin farkon shekararsa ta 50. Daga benensa, ya ga kyakkyawa Bath-sheba tana wanka. Ya yi tambaya game da ita ya san wacece ce. Ya fahimci cewa mijinta, Uriya, yana bakin yaƙi a Rabba, birnin Ammonawa. Dauda ya sa aka kawo ta fadarsa ya kwana da ita. Daga baya, abubuwa suka cakuɗe—ta ga Dauda ya yi mata ciki. Da tsammanin Uriya zai kwana da matarsa, Dauda ya kira shi daga bakin yaƙi. A wannan hanyar, Uriya zai zama kamar shi ne uban ɗan Bath-sheba. Amma Uriya bai je gidansa ba. Da ya dugunzuma don ya rufe zunubinsa, sai Dauda ya sake tura Uriya zuwa Rabba da wasiƙa ga shugaban rundunar sojojin ya ce a saka Uriya a gefen da za a kashe shi. Sai aka kashe Uriya, Dauda kuma ya auri bazawarar kafin jama’a su san tana da ciki.—2 Sama’ila 11:1-27.

15. (a) Ta yaya aka fallasa zunubin Dauda? (b) Yaya Dauda ya ji game da tsawatarwar Natan cikin basira?

15 Kamar dai Dauda ya ci nasara a ƙullin da ya yi ya rufe zunubinsa. Watanni suka shige. Aka haifi yaro. Idan Dauda ya rubuta Zabura ta 32 da wannan abin a zuci, to lamirinsa ya azabtar da shi ne. (Zabura 32:3-5) Duk da haka, ba zai ɓoye zunubin wa Allah ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.” (2 Sama’ila 11:27) Jehovah ya aike annabi Natan, wanda cikin basira ya tuntuɓi Dauda game da abin da ya yi. Nan da nan Dauda ya yi ikirari kuma ya roƙi gafarar Jehovah. Tuba da ya yi da gaske ya kawo sulhu tsakaninsa da Allah. (2 Sama’ila 12:1-13) Dauda bai ƙi tsawatarwa ba. Maimako, ya nuna halin da aka kwatanta a cikin Zabura 141:5: “Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri, zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai.”

16. Wane kashedi da gargaɗi Sulemanu ya yi game da laifuffuka?

16 Sulemanu, wanda shi ne ɗan Dauda na biyu wajen Bath-sheba, wataƙila ya yi bimbini a kan wannan mummunar fanni na rayuwar ubansa. Daga baya ya rubuta: “Ba za ka taɓa cin nasara a zamanka ba muddin kana ɓoye laifofinka. Ka hurta zunubanka ka tuba, sa’an nan Allah zai yi maka jinƙai.” (Karin Magana 28:13) Idan muka faɗa cikin mummunar zunubi, ya kamata mu bi wannan hurarren gargaɗi, wanda kashedi ne kuma shawara ce. Ya kamata mu yi ikirari ga Jehovah kuma mu je wajen dattawan ikilisiya don taimako. Hakkin dattawa mafi muhimmanci shi ne su taimaka su karkato da waɗanda suka yi laifuffuka.—Yakubu 5:14, 15.

Jure wa Sakamakon Zunubi

17. Ko da yake Jehovah yana gafarta zunubai, daga menene ba ya kāre mu?

17 Jehovah ya gafarta wa Dauda. Me ya sa? Domin Dauda mutum ne mai aminci, domin yana da jinƙai ga wasu, kuma domin tubarsa ta gaskiya ce. Duk da haka, ba a kāre Dauda daga bala’i da ya biyo baya ba. (2 Sama’ila 12:9-14) Haka yake a yau. Ko da yake Jehovah ba ya yin mugunta ga waɗanda suka tuba, ba ya kāre su daga sakamakon mummunar abin da suka yi. (Galatiyawa 6:7) Sakamakon fasikanci zai iya zama kisan aure, cikin shege, cutar da ake ɗauka wajen jima’i, da rashin yarda da kuma daraja.

18. (a) Yaya Bulus ya ce ikilisiyar Korantiyawa su bi da batun mummunar lalatar jima’i? (b) Ta yaya Jehovah ya nuna ƙauna da kuma jinƙai ga masu zunubi?

18 Idan muka yi mummunan kuskure, ba shi da wuya mu karaya lokacin da muke shan wahalar sakamakon kuskuren da muka yi. Duk da haka, kada mu bar kome ya hana mu tuba kuma mu sulhunta da Allah. A ƙarni na farko, Bulus ya rubuta wa Korantiyawa cewa ya kamata su cire daga cikin ikilisiya wani mutum wanda yake yin fasikanci da danginsa. (1 Korantiyawa 5:1, 13) Da mutumin ya tuba da gaske, Bulus ya umurci ikilisiyar: “Ku yafe masa, ku kuma ƙarfafa masa zuciya, ku tabbatar masa da ƙaunarku.” (2 Korantiyawa 2:7, 8) A wannan hurarren gargaɗi, mun ga ƙaunar Jehovah da kuma jinƙansa ga masu zunubi waɗanda suka tuba. Mala’iku a sama suna farin ciki idan mai zunubi guda ya tuba.—Luka 15:10.

19. Yin baƙin ciki da ya dace saboda kuskure zai kai ga wane amfani?

19 Ko da yake laifi yana baƙanta mana rai, nadama da muke yi tana taimaka mana ‘mu mai da hankali don kada mu koma ga yin mugun abu.’ (Ayuba 36:21) Hakika, bala’in da yake biyo bayan zunubi ya kamata ya hana mu sake yin mugun abu. Ƙari ga haka, Dauda ya yi amfani da baƙin ciki da ya fuskanta daga zunubinsa ya yi wa wasu gargaɗi. Ya ce: “Zan koya wa masu zunubi umarnanka, za su kuwa komo wurinka.”—Zabura 51:13.

Ana Samun Farin Ciki Daga Bauta wa Jehovah Ne

20. Wane amfani ake samu daga yin biyayya ga umurnan Allah na adalci?

20 Yesu ya ce: “Albarka tā fi tabbata ga waɗanda ke jin Maganar Allah suke kuma kiyaye ta.” (Luka 11:28) Biyayya ga umurnan Allah tana kawo farin ciki yanzu da kuma har abada. Idan muka riƙe tarbiyya mara aibi, za mu iya ci gaba a kan hanyar ta yin amfani da tanadi da Jehovah ya yi don ya tallafa mana. Idan mun faɗa cikin lalata, bari mu samu ƙarfafa cikin sanin cewa a shirye Jehovah yake ya gafarta wa waɗanda suka tuba da gaske, bari kuma mu ƙuduri aniyyar kada mu sake yin zunubin.—Ishaya 55:7.

21. Bin wane gargaɗi da manzo Bitrus ya yi ne zai taimake mu riƙe ɗabi’a mai tsarki?

21 Ba da daɗewa ba wannan duniyar marar adalci za ta shuɗe, tare da dukan rashin ɗabi’arta. Ta wajen riƙe tarbiyya mara aibi, za mu amfana yanzu da kuma har abada. Manzo Bitrus ya rubuta: “Ya ƙaunatattuna, tun da kuke jiran waɗannan abubuwa, ku himmantu ya same ku marasa tabo, marasa aibu, masu zaman salama. . . . Da ya ke kun riga kun san haka, ku kula kada bauɗewar kangararru ta tafi da ku, har ku fāɗi daga matsayinku.”—2 Bitrus 3:14, 17.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Me ya sa yake da wuya a riƙe tarbiyya mara aibi?

• Waɗanne hanyoyi ne za mu iya tallafa wa ƙudurinmu na riƙe ɗabi’a mai tsarki?

• Waɗanne darussa za mu koya daga zunubin saurayi da Sulemanu ya yi maganarsa?

• Menene misalin Dauda ya koya mana game da tuba?

[Hoto a shafi na 25]

Kāriya ce a gaya wa wasu tsayawarka a batun tarbiyya

[Hotuna a shafuffuka na 248 29]

Domin Dauda ya tuba da gaske, Jehovah ya gafarta masa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba