Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 11/1 pp. 8-13
  • Mulkin Allah—Sabuwar Sarauta Ta Duniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mulkin Allah—Sabuwar Sarauta Ta Duniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sabuwar Sarauta ta Duniya
  • Abokan Sarauta
  • Nufin Allah ne a Yi Mulkin?
  • ‘Ba a Hannun Mutum ne Yake Ba’
  • Kyautar ’Yancin Zaɓe
  • Mulkin “da ba Za a Rushe Shi ba Daɗai”
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Menene Mulkin Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Sashe na 8—Nufe-Nufen Allah Na Tafiya Zuwa Cikawa
    Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 11/1 pp. 8-13

Mulkin Allah—Sabuwar Sarauta Ta Duniya

“Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.”—DANIYEL 2:44.

1. Wane gabagaɗi za mu kasance da shi game da Littafi Mai Tsarki?

LITTAFI MAI TSARKI wahayi ne daga Allah zuwa ga ’yan Adam. Manzo Bulus ya rubuta: “Sa’ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, wato Maganar Allah.” (1 Tasalonikawa 2:13) Littafi Mai Tsarki na ɗauke da abin da muke bukatar mu sani game da Allah: game da mutumtakarsa, game da nufe-nufensa, da abin da yake bukata a gare mu. Yana da gargaɗi mafi kyau game da rayuwar iyali da halaye na yau da kullum. Ya faɗa annabce-annabce da sun cika dā dalla-dalla, da waɗanda suke cika yanzu, da waɗanda za su cika nan gaba. Hakika, “kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci, domin bawan Allah ya zama cikakke, shiryayye sosai ga kowane kyakkyawan aiki.”—2 Timoti 3:16, 17.

2. Yaya Yesu ya nanata jigon Littafi Mai Tsarki?

2 Abin da ya fi muhimmanci a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne jigonsa: kunita ikon mallakar Allah (ikonsa na sarauta) ta wajen Mulkinsa na samaniya. Yesu ya sa wannan ya zama abu na musamman a cikin hidimarsa. “Tun daga lokacin nan Yesu ya fara wa’azi, yana cewa: ‘Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.” (Matiyu 4:17) Ya nuna inda ya kamata mu saka shi a rayuwarmu, ya aririta: “Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma adalcinsa.” (Matiyu 6:33) Ya kuma nuna yadda hakan yake da muhimmanci ta koya wa mabiyansa su yi addu’a ga Allah: “Mulkinka ya zo, a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.”—Matiyu 6:10.

Sabuwar Sarauta ta Duniya

3. Me ya sa Mulkin Allah abu ne da yake da muhimmanci na nan da nan a gare mu?

3 Me ya sa Mulkin Allah yake da muhimmanci haka ga bil’adam? Domin ba da daɗewa ba zai yi abu da zai canja sarauta ta wannan duniya har abada. Annabci na Daniyel 2:44 ya ce: “A kwanakin waɗannan sarakuna, [da suke sarautar duniya yanzu] Allah na Sama zai kafa wani mulki [gwamnati a sama] wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki [gwamnatoci na duniya], ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.” Lokacin da Mulkin Allah na samaniya ya soma sarauta gaba ɗaya, mutane ba za su sake sarautar duniya ba. Sarauta ta mutane da ke haddasa rashin haɗin kai kuma da ba ta gamsarwa za ta zama aba da ta wuce.

4, 5. (a) Me ya sa Yesu ne ya dace sosai ya zama Sarkin a sama? (b) Wane aiki ne Yesu zai samu a nan gaba kusa?

4 Babban Masarauci na Mulkin samaniya a ƙarƙashin ja-gorar Jehovah, shi ne wanda ya dace sosai—Kristi Yesu. Kafin ya zo duniya, yana da zama a sama shi ‘gwanin aiki’ ne na Allah da yake shi ne halittar farko na Allah. (Karin Magana 8:22-31) “Shi ne surar Allah marar ganuwa, magaji ne tun ba a halicci kome ba, don ta gare shi ne aka halicci dukkan kome, abubuwan da ke sama da abubuwan da ke ƙasa.” (Kolosiyawa 1:15, 16) Lokacin da Allah ya aiko Yesu zuwa duniya, ya yi nufin Allah a kowane yanayi. Ya jure wa gwaji mafi wuya kuma ya mutu cikin aminci ga Ubansa.—Yahaya 4:34; 15:10.

5 Don amincinsa ga Allah har mutuwa, an saka wa Yesu. Allah ya tashe shi zuwa sama ya kuma ba shi ikon Sarauta a sama. (Ayyukan Manzanni 2:32-36) Da yake shi Sarki ne na Mulkin, Kristi Yesu zai samu aiki na ban mamaki daga Allah ya jagabanci dubban halittun ruhu masu girma wajen kawar da sarautar ’yan Adam daga duniya da kuma cire dukan mugunta a duniyarmu. (Karin Magana 2:21, 22; 2 Tasalonikawa 1:6-9; Wahayin Yahaya 19:11-21; 20:1-3) Sa’an nan Mulkin Allah na samaniya a hannun Kristi zai zama sabon iko da ke sarauta, gwamnati ɗaya tak da take bisa dukan duniya.—Wahayin Yahaya 11:15.

6. Wane irin sarauta za mu zata daga Sarki na Mulkin?

6 Kalmar Allah ta ce game da sabon Masarauci na duniya: “Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, domin dukan jama’a, da al’ummai, da harsuna su bauta masa.” (Daniyel 7:14) Domin Yesu zai yi koyi da ƙaunar Allah, salama da farin ciki za su kasance ƙwarai a lokacin sarautarsa. (Matiyu 5:5; Yahaya 3:16; 1 Yahaya 4:7-10) “Game da ƙaruwa na gwamnatinsa da salama za su kasance ko yaushe, . . . za a ɗaukaka ta da yin gaskiya da kuma adalci.” (Ishaya 9:7, Revised Standard Version) Za ta zama albarka ce a sami Sarki da zai yi sarauta da ƙauna, gaskiya, da kuma adalci! Da haka, 2 Bitrus 3:13 ya annabta: “Amma bisa ga alkawarinsa muna jiran sababbin sammai [Mulkin Allah na samaniya] da sabuwar ƙasa [sabuwar jam’iyyar duniya], inda adalci zai yi zamansa.”

7. Ta yaya Matiyu 24:14 ke cika a yau?

7 Babu shakka Mulkin Allah shi ne labari mafi daɗi ga dukan waɗanda suke ƙaunar abin da ke daidai. Shi ya sa, da yake ba da alama cewa yanzu muna cikin “zamanin ƙarshe” na wannan mugun tsari, Yesu ya annabta: “Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.” (2 Timoti 3:1-5; Matiyu 24:14) Wannan annabci yana cika yanzu, Shaidun Jehovah wajen miliyan shida a ƙasashe 234 suna ba da sa’o’i fiye da biliyan a shekara a gaya wa wasu game da Mulkin Allah. Daidai kuwa, kowanne wajen bautarsu a ikilisiyoyi 90,000 na dukan duniya ana kiransa Majami’ar Mulki. A wurin, mutane suna zuwa su koya game da sabuwar gwamnati mai zuwa.

Abokan Sarauta

8, 9. (a) Daga ina ne abokan sarautar Kristi suka fito? (b) Wane gaba gaɗi za mu kasance da shi a sarautar Sarkin da abokan sarautarsa?

8 Za a samu abokan sarauta da Kristi Yesu a Mulkin Allah na samaniya. Wahayin Yahaya 14:1-4 ya annabta cewa mutane 144,000 za a “fanso daga cikin mutane” kuma a tashe su zuwa rayuwa a sama. Waɗannan sun haɗa da maza da mata waɗanda maimako a yi musu hidima, cikin tawali’u suna wa Allah da ’yan’uwa mutane hidima. “Za su zama firistocin Allah da na Almasihu, su kuma yi mulki tare da shi har shekara dubu.” (Wahayin Yahaya 20:6) Adadinsu ya yi kaɗan da “ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al’umma, da kabila, da jama’a, da harshe” waɗanda za su tsira a ƙarshen wannan tsarin. Waɗannan ma suna bauta wa Allah “dare da rana,” amma ba za su je sama ba. (Wahayin Yahaya 7:9, 15) Sun zama cibiyar sabuwar duniya, su ne Mulkin Allah na samaniya zai yi sarauta a kansu.—Zabura 37:29; Yahaya 10:16.

9 A zaɓan waɗanda za su yi sarauta da Kristi a sama, Jehovah ya zaɓi mutane masu aminci waɗanda suka fuskanci matsaloli a rayuwa. Babu abin da mutane suka fuskanta da waɗannan sarakuna da firistoci ba su fuskanta ba. Saboda haka rayuwarsu a duniya za ta ƙara inganta sarautarsu bisa mutane. Yesu ma kansa “ya koyi biyayya ta wuyar da ya sha.” (Ibraniyawa 5:8) Manzo Bulus ya faɗi haka game da shi: “Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a’a, shi ne wanda aka jarabe shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.” (Ibraniyawa 4:15) Lalle yana ta’azantarwa a san cewa a sabuwar duniya ta Allah mai adalci, sarakuna da firistoci masu ƙauna da tausayi za su yi sarautar mutane!

Nufin Allah ne a Yi Mulkin?

10. Me ya sa Mulki na sama ba ya cikin nufin Allah na asali?

10 Mulki na samaniya yana cikin nufin Allah na asali ne lokacin da ya halicce Adamu da Hauwa’u? A labarin halitta da ke cikin Farawa, ba a ambata wani Mulki da zai yi sarautar mutane ba. Jehovah kansa ne Sarkinsu, muddin suna masa biyayya, ba a bukatar wata sarauta. Farawa sura 1 ya nuna cewa, wataƙila ta wajen Ɗansa ɗan fari na samaniya, Jehovah ya yi sha’ani da Adamu da Hauwa’u. Labarin ya yi amfani da furcin nan ‘Allah ya ce musu’ da kuma “Allah kuwa ya ce” musu.—Farawa 1:28, 29; Yahaya 1:1.

11. Ta yaya mutane suka kasance da somi mai kyau?

11 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai.” (Farawa 1:31) Kome da yake cikin gonar Adnin yana da gwanin kyau. Adamu da Hauwa’u suna da zama cikin aljanna. Azantansu da jikunansu cikakku ne. Sukan yi magana da Mahaliccinsu shi kuma ya yi da su. Ta kasancewa da aminci, za su haife yara kamiltattu. Da ba a bukaci sabuwar gwamnati na samaniya ba.

12, 13. Yayin da mutane kamiltattu suke ƙaruwa, da ta yaya Allah zai iya sadawa da su?

12 Yayin da iyalin ’yan Adam suke ƙaruwa, yaya Allah zai riƙa magana da su? Ka yi la’akari da taurari na sama. An haɗa su a sararin samaniya da ake kira rukunin taurari. Wasu rukunan suna ɗauke da taurari biliyan. Wasu kuma suna ɗauke da biliyoyi. Masana kimiyya sun kimanta cewa akwai taurari wajen 100 biliyan a sararin sama da ake gani! Duk da haka, Mahaliccin ya ce: “Ka dubi sararin sama a bisa! Wanene ya halicci taurarin da ka ke gani? Shi wanda yake musu ja-gora kamar sojoji, ya sani ko su guda nawa ne, yana kiran dukansu, kowanne da sunansa! Ikonsa da girma yake, ba a taɓa rasa ko ɗayansu ba.”—Ishaya 40:26.

13 Tun da yake Allah ya san duka waɗannan halittu na sama, babu shakka ba zai masa da wuya ya san adadi kaɗan na mutane ba. A yanzu ma, bayinsa miliyoyi suna addu’a kullum a gare shi. Waɗannan addu’o’i suna kai wurin Allah nan da nan. Saboda haka yin magana da dukan mutane kamiltattu da ba zai zama masa matsala ba. Da ba zai bukaci Mulki na samaniya ba don ya yi musu ja-gora. Lalle wannan shiri ne mai girma—Jehovah ya zama Masarauci, a yi magana da shi kai tsaye, da tsammanin ba za a taɓa mutuwa ba, a zauna har abada a cikin aljanna ta duniya!

‘Ba a Hannun Mutum ne Yake Ba’

14. Me ya sa mutane za su bukaci sarautar Jehovah har abada?

14 Amma, mutane—har ma kamiltattu—za su bukaci sarautar Jehovah har abada. Me ya sa? Domin Jehovah bai halicce su su yi sarautar kansu ba ban da taimakonsa. Wannan mizani ne ga ’yan Adam, yadda annabi Irmiya ya nuna: “Ya Ubangiji, na sani al’amuran mutum ba a hannunsa suke ba, ba mutum ne ke kiyaye takawarsa ba. Ka tsauta mini, ya Ubangiji.” (Irmiya 10:23, 24) Wauta ce ’yan Adam su yi tunani cewa za su yi ja-gorar mutane ba tare da Jehovah ya yi sarautarsu ba. Zai saɓa da yadda ya yi su. ’Yanci daga sarautar Jehovah babu shakka zai kawo, son kai, ƙiyayya, zalunci, mugunta, yaƙe-yaƙe, da mutuwa. ‘Mutane za su sha wuya a ƙarƙashin waɗanda suke mulki.’—Mai Hadishi 8:9.

15. Wane sakamako ne ya fito daga mummunar zaɓe da iyayenmu na farko suka yi?

15 Abin baƙin ciki, iyayenmu na farko suka shawarta cewa ba sa son Allah ya zama Masaraucinsu, sun zaɓi su ware kansu daga wurinsa. Sakamakon haka, Allah bai kiyaye su ba cikin kamilci. Yanzu suna kama ne da abin da yake aiki da lantarki da aka yanke daga tushe da yake samun wutar. Da kaɗan kaɗan za su rage yadda suke aiki har su tsaya—lokacin da suka mutu. Sun zama kamar samfur mai aibi, kuma wannan yanayin ne kawai suka ba ’ya’yansu. (Romawa 5:12) “Shi [Jehovah] Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne, gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne. . . . Sun aikata mugunta a gabansa, su ba ’ya’yansa ba ne saboda lalacewarsu.” (Maimaitawar Shari’a 32:4, 5) Gaskiya, halittar ruhu da ya yi tawaye wanda ya zama Shaiɗan ne ya zuga Adamu da Hauwa’u, amma suna da kamiltaccen azanci, da za su iya ƙin shawarwarinsa marar kyau.—Farawa 3:1-19; Yakubu 4:7.

16. Ta yaya tarihi ya nuna sakamakon ’yanci daga Allah?

16 Tarihi ya nuna sakamako mai yawa da ya fito daga ’yancin kai wurin Allah. Shekaru dubbai yanzu, mutane sun gwada kowace irin gwamnati ta ’yan Adam, kowane irin tsarin tattalin arziki da na zaman jama’a. Duk da haka, mugunta “ƙara muni za su riƙa yi.” (2 Timoti 3:13) Ƙarni na 20 ya tabbatar da wannan. Ya cika da ƙiyayya da kuma mugunta da ta fi muni, yaƙi, yunwa, talauci, da wahala da ta fi kowacce cikin tarihi. Kuma kowane irin hanyoyin jinya da aka yi, nan gaba ba da jimawa ba kowa zai mutu. (Mai Hadishi 9:5, 10) Ta wurin ƙoƙari su kiyaye takawarsu, mutane sun ba da kansu ga Shaiɗan da aljanunsa sosai har Littafi Mai Tsarki ya kira Shaiɗan “sarkin zamanin nan.”—2 Korantiyawa 4:4.

Kyautar ’Yancin Zaɓe

17. Ta yaya za a yi amfani da kyautar Allah na ’yancin zaɓe?

17 Me ya sa Jehovah ya ƙyale mutane su yi nasu zaɓe? Domin ya halicce su ya ba su kyauta mai girma na son rai, ikon ’yancin zaɓe. “Inda Ruhun Ubangiji yake kuma, a nan ’yanci yake,” in ji manzo Bulus. (2 Korantiyawa 3:17) Ba wanda yake so ya zama na’ura da sai wani ya gaya mata abin da za ta faɗa da abin da za ta yi kowace daƙiƙa na rana. Amma Jehovah ya bukaci mutane su yi amfani da wannan ’yancin zaɓe da kyau, su ga hikimar yin nufinsa kuma su ci gaba da yin biyayya gare shi. (Galatiyawa 5:13) Saboda haka ’yanci ba zai kasance cikakke ba, saboda wannan zai kawo yamutsi. Za a sarrafa shi cikin iyakar dokokin Allah na alheri.

18. Menene Allah ya nuna ta barin ’yan Adam su yi zaɓe da kansu?

18 Ta barin iyalin ’yan Adam su bi nasu hanyar, Allah sau ɗaya ɗungum, ya nuna cewa muna bukatar sarautarsa. Yadda yake sarauta, ikon mallakarsa, hanya ce kawai da ke daidai. Tana kawo farin ciki, gamsuwa, da ni’ima mafi girma. Wannan haka ne domin zukatanmu da jikunanmu Jehovah ya shirya su su yi aiki sosai yayin da suke tafiya daidai da dokokinsa. “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi.” (Ishaya 48:17) ’Yancin zaɓe ba tare da ƙetare dokokin Allah ba ba zai yi nauyi ba amma zai sa a yi abinci, gidaje, zane-zane, da kaɗe-kaɗe dabam dabam masu kyau. Idan an yi amfani mai kyau da shi, ’yancin yin abu da zai kawo rayuwa mai armashi, da ban marmari ne a cikin aljanna ta duniya.

19. Ta yaya Allah zai sulhunta kansa da ’yan Adam?

19 Amma saboda zaɓensu marar kyau, mutane suka ware kansu daga Jehovah, suka zama ajizai, suna suƙuƙucewa, suna kuma mutuwa. Saboda haka zai bukaci a fanshe su daga wannan yanayi na baƙin ciki a kuma mai da su zuwa dangantaka mai kyau da Allah na ’ya’yansa maza da mata. Ta Mulkinsa da ya zaɓa ne Allah zai cim ma wannan, Mai Fansar Yesu Kristi ne. (Yahaya 3:16) Ta wannan tsari, waɗanda suka tuba da gaske—kamar ɗa mubazzari a kwatancin Yesu—za su sulhunta da Allah, kuma zai karɓe su su zama ’ya’yansa.—Luka 15:11-24; Romawa 8:21; 2 Korantiyawa 6:18.

20. Ta yaya Mulkin zai cika nufin Allah?

20 Babu fasawa, nufin Jehovah zai cika a duniya. (Ishaya 14:24, 27; 55:11) Ta wajen Mulkinsa a hannun Kristi, Allah zai kunita (daidaita ko nuna) ikonsa sosai, na mai Mallakarmu. Mulkin zai kawo ƙarshen sarautar mutane da na aljanu bisa duniya, kuma shi kaɗai zai yi sarauta daga sama na shekara dubu. (Romawa 16:20; Wahayin Yahaya 20:1-6) Amma a lokacin, yaya za a nuna mafificiyar hanyar sarauta ta Jehovah? Bayan shekara dubun, wane hakki ne Mulkin zai kasance da shi? Talifi na biye zai bincika waɗannan tambayoyi.

Darussa don Maimaitawa

• Menene jigon Littafi Mai Tsarki?

• Su wa sabuwar sarauta ta duniya ta ƙunsa?

• Me ya sa sarautar ’yan Adam ba da taimakon Allah ba ba za ta yi nasara ba?

• Dole yaya za a yi amfani da ’yancin yin abu?

[Hoto a shafi na 8]

Koyarwar Yesu ta nanata sarautar Allah ta wajen Mulkin

[Hotuna a shafi na 10]

A kowacce ƙasa Shaidun Jehovah suna sa Mulkin ya zama koyarwarsu na musamman

[Hotuna a shafi na 12]

Tarihi ya nuna mummunar sakamako na ’yanci daga Allah

[Inda aka Dauko]

Sojojin WWI: U.S. National Archives photo; sansanin: Oświęcim Museum; yaro: UN PHOTO 186156/J. Isaac

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba