Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 12/1 pp. 30-31
  • Ya Kamata Ka Bincika Wasu Addinai Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Kamata Ka Bincika Wasu Addinai Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gano Kiristanci na Gaskiya
  • Yi Hankali da Malaman Ƙarya
  • Bauta da Allah Ya Amince da Ita
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ka Guji Bautar Ƙarya!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ina Yadda Zaka Sami Addini na Gaskiya?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Game da Bauta ta Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 12/1 pp. 30-31

Ya Kamata Ka Bincika Wasu Addinai Kuwa?

“NA HALARCI taron Kirista kusan shekara ke nan, ina jin daɗin gaya wa wasu game da Mulkin Allah” in ji Miguel, wanda yanzu Mashaidi ne a Amurka ta Yamma. “Sai na fara sauraron wa’azin wasu addinai a rediyo kuma na riƙa kallon masu wa’azi na addini a telibijin. Ina tsammanin irin waɗannan abubuwa za su taimake ni in fahimci mutanen wasu addinai da kyau. Na fahimci cewa koyarwarsu ba daga Littafi Mai Tsarki ba ce, amma ina so in sani.”

A wannan ƙasar, Jorge yana da ƙwazo wajen koya wa wasu game da bautar gaskiya. Duk da haka, a wani lokaci, shi ma ya fara sauraron wa’azin addinai a rediyo da telibijin. Yakan ce, “Kana bukatar ka san abin da wasu suke tunaninsa.” Idan aka tambaye shi game da haɗari da sauraron koyarwar ƙarya za ta kawo, sai ya ce: “Babu abin da zai lalata bangaskiyar wanda ya san gaskiyar Littafi Mai Tsarki.” Waɗannan labarai sun jawo muhimmiyar tambaya, daidai ne a saurari abin da wasu suka gaskata?

Gano Kiristanci na Gaskiya

Bayan da manzanni suka mutu, bauta ta gaskiya ta fara gurɓacewa a hankali da wasu jabun Kiristanci da yawa. Fahimtar wannan zai faru, Yesu ya faɗi hanya ɗaya na bambanta wannan jabun Kiristanci daga Kiristanci na gaskiya. Da farko, ya yi kashedi: “Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.” Sai ya daɗa: “Za ku gane su ta irin aikinsu.” (Matiyu 7:15-23) Mabiyan Yesu na gaskiya suna yin abin da ya koyar, kuma babu wuya a gane su ta wajen irin aikinsu mai kyau. Kamar dai yadda Yesu kansa ya yi, suna ziyartar mutane suna yi musu bayanin Mulkin Allah daga Nassosi. Wajen yin koyi da Yesu, suna ware kansu daga siyasar duniya da kuma hargitsinta. Sun karɓi Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne kuma suna daraja shi a kan gaskiya ne. Suna sanar da sunan Allah. Kuma tun da suna ƙoƙarin su yi ƙauna da Allah ya koyar, ba sa yaƙe-yaƙe. Maimakon haka, suna bi da juna a matsayin ’yan’uwa.—Luka 4:43; 10:1-9; Yahaya 13:34, 35; 17:16, 17, 26.

Bisa Nassosi, yana yiwuwa a ga “bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da ke bauta mini da wanda ba ya bauta mini.” (Malakai 3:18) Masu bauta ta gaskiya a yau suna da haɗin kai wajen tunani da kuma ayyuka, kamar yadda Kiristoci na ƙarni na farko suke. (Afisawa 4:4-6) Da zarar ka gano wannan rukunin Kiristoci na gaskiya, me ya sa ba za ka so ka yi bincike game da imanin wasu ko kuma ka so ka sani?

Yi Hankali da Malaman Ƙarya

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa har ma bayan koyon gaskiyar Littafi Mai Tsarki, da akwai haɗarin gurɓacewa ta ruhaniya daga koyarwar ƙarya. Manzo Bulus ya yi kashedi: “Ku lura kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al’adar mutane kawai, wato bisa ga al’adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.” (Kolosiyawa 2:8) Wannan hoton kwatanci ne! Kamar dabba da yake so ya kama ka ya cinye, malaman ƙarya suna iya kawo haɗari na ƙwarai.

Hakika, Bulus ya lura da abin da wasu suka gaskata. Saboda haka ya fara taɗi da cewa: “Ya ku mutanen Atina, na dai lura, ku masoyan ibada ne ƙwarai, ta kowane fanni. Don sa’ad da nake zagawa, na duba abubuwan da kuke yi wa ibada, har ma na tarar da wani bagaden hadaya da wannan rubutu a sama da shi cewa, ‘Saboda Allahn da ba a sani ba.’ ” (Ayyukan Manzanni 17:22, 23) Amma dai, Bulus baya saurarar falsafar baki na Helenawa kullum.

Abu ɗaya ne ka sanar da kanka game da tushen da kuma imanin addinan ƙarya kuma wani abu ne dabam ka riƙa sauraronsu.a Jehovah ya naɗa “amintaccen bawan nan mai hikima” ya riƙa tanadin koyarwa bisa Kalmarsa. (Matiyu 4:4; 24:45) Bulus da kansa ya rubuta: “Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu. Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi?”—1 Korantiyawa 10:20-22.

Wasu malaman ƙarya wataƙila dā Kiristoci ne na gaskiya, amma a wani lokaci suka juya daga gaskiya zuwa kure. (Yahuza 4, 11) Wannan bai kamata ya ba mu mamaki ba. Bayan ya yi maganar “amintaccen bawan nan mai hikima” da yake wakiltar rukunin Kiristoci shafaffu, Yesu ya faɗi game da ‘mugun bawa,’ ajin waɗannan suke gunaguni, “Ubangijina ya jinkirta zuwansa,” sa’annan ya soma dukan sauran abokan bautarsa. (Matiyu 24:48, 49) Sau da yawa, waɗannan mutanen da mabiyansu ba su da koyarwar kansu; su dai bukatarsu kawai su halaka bangaskiyar wasu ne. Game da su manzo Yahaya ya rubuta: “Kowa ya zo gare ku, bai kuwa zo da wannan koyarwa ba, kada ku karɓe shi a gidanku, ko maraba ma kada ku yi masa.”—2 Yahaya 10; 2 Korantiyawa 11:3, 4, 13-15.

Mutane da suke neman addini na gaskiya da gaske sun yi ƙoƙari wajen la’akari da kyau da abin da suka ji daga addinai dabam dabam. Da shigewar lokaci, Allah zai albarkaci mutane masu zukatan kirki waɗanda suke neman gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce game da hikima ta Allah: “Ka nema da iyakar ƙoƙarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin ɓoyayyiyar dukiya. Idan ka yi za . . . ka yi nasara a kan koyon sanin Allah.” (Karin Magana 2:4, 5) Bayan ka sami wannan sanin Allah ta wajen Littafi Mai Tsarki da kuma ikilisiyar Kirista kuma bayan ka ga yadda Jehovah ya albarkaci waɗanda wannan sani ya yi musu ja-gora, Kiristoci na gaskiya ba za su ci gaba da sauraron koyarwa na addinan ƙarya ba.—2 Timoti 3:14.

[Hasiya]

a Littafin nan Mankind’s Search for God, da Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., suka buga, ya sanar game da tushen addinan duniya da kuma koyarwarsu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba