Gadōnmu Mai Tamani—Menene Yake Nufi A Gare Ka?
“Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.”—MATIYU 25:34.
1. Waɗanne irin abubuwa ake bar wa mutane gado?
DUKAN mutane suna da abubuwan da suka gāda. Wasu gadōnsu ya ƙunshi dukiya. Wasu kuma talauci suka gada. A wasu fannoni kuma, tsararraki da suka wuce, domin abin da ya faru musu ko suka ji, sun bar gadōn ƙiyayya mai tsanani na wani ƙabila. Amma, dukanmu muna da abu guda, iri ɗaya. Dukanmu mun gaji zunubi daga mutum na farko, Adamu. Wannan gadōn yana kai kowa ga mutuwa.—Mai Hadishi 9:2, 10; Romawa 5:12.
2, 3. Wane gadō ne Jehovah ya yi tun asali ga ’ya’yan Adamu da Hauwa’u, to me ya sa ba su samu ba?
2 Uba mai ƙauna, Jehovah, tun asali ya ba wa mutane gadō da ke dabam—rai madawwami cikin kamilcewa a Aljanna. Iyayenmu na farko, Adamu da Hauwa’u, sun soma rayuwa a kamilce, babu zunubi. Jehovah Allah ya yi wa mutane kyautar Duniya. (Zabura 115:16) Ya yi tanadin gonar Adnin alamar yadda dukan duniya za ta zama kuma ya ba iyayenmu na farko aiki mai girma, na ban mamaki. Za su haifi ’ya’ya, su lura da duniya da dukan shuke-shuke dabam dabam da kuma dabbobin cikinta, kuma za su faɗaɗa Aljannar ta cika duniya. (Farawa 1:28; 2:8, 9, 15) ’Ya’yansu ma za su yi wannan aiki. Wane gadō ne mai girma da ya fi wannan!
3 Amma, idan za su more dukan wannan, tilas ne Adamu da Hauwa’u da ’ya’yansu su kasance da dangantaka mai kyau da Allah. Suna da hakkin ƙaunar Jehovah da kuma yi masa biyayya, amma Adamu da Hauwa’u suka kasa nuna godiya ga abin da Allah ya ba su suka taka umarninsa. Suka yi hasarar gidansu na Aljanna da kuma dama mai ɗaukaka da Allah ya sa a gabansu. Saboda haka, ba su iya ba da wannan ga ’ya’yansu ba.—Farawa 2:16, 17; 3:1-24.
4. Ta yaya za mu iya samun gadō da Adamu ya yi banza da shi?
4 Cikin jinƙai, Jehovah ya yi tanadi domin ’ya’yan Adamu da Hauwa’u su sami zarafi na samun gadō da Adamu ya yi banza da shi. Ta yaya? A lokaci na Allah, Ɗansa, Yesu Kristi, ya ba da kamiltaccen ransa na mutum domin ’ya’yan Adamu. Ta haka ne Kristi ya fanshe su duka. Amma dai, gadōn bai zama nasu hakanan kawai ba. Suna bukatar su sami amincewa wajen Allah, wadda za su iya samu ta wurin bayyana bangaskiya cikin darajar hadayar kafarar zunubi na Yesu kuma ta wurin nuna bangaskiyar nan wajen yin biyayya. (Yahaya 3:16, 36; 1 Timoti 2:5, 6; Ibraniyawa 2:9; 5:9) Tafarkin rayuwarka yana nuna godiya ga tanadin nan kuwa?
An Ba da Gadō ta Wurin Ibrahim
5. Ta yaya Ibrahim ya nuna godiyarsa domin dangantakarsa da Jehovah?
5 Yayin da yake ci gaba da tafiyar da nufinsa game da duniya, Jehovah ya bi da Ibrahim a hanya ta musamman. Ya ce wa mutumin nan amincacce ya bar ƙasarsa ya tafi ƙasar da Allah kansa zai nuna masa. Ibrahim ya yi biyayya. Bayan da Ibrahim ya kai wajen, Jehovah ya ce ’ya’yan Ibrahim ne, ba Ibrahim kansa ba, za su gaji ƙasar. (Farawa 12:1, 2, 7) Yaya Ibrahim ya yi? A shirye yake ya bauta wa Jehovah duk inda yake so kuma ko ta yaya Allah ya umurta domin ’ya’yansa su sami gadōnsu. Ibrahim ya bauta wa Jehovah na shekara 100 a ƙasar da ba tasa ba, har mutuwarsa. (Farawa 12:4; 25:8-10) Da ka yi haka kuwa? Jehovah ya ce Ibrahim ‘abokinsa’ ne.—Ishaya 41:8.
6. (a) Menene Ibrahim ya nuna ta wurin niyyar miƙa ɗansa hadaya? (b) Wane gadō mai tamani ne Ibrahim ya bayar ga ’ya’yansa?
6 Ibrahim ya yi jira na shekaru da yawa don ya haifi ɗa, Ishaku, wanda yake ƙauna sosai. Lokacin da yaron ya yi girma ya isa mutum, Jehovah ya umarci Ibrahim ya ba da yaron hadaya. Ibrahim bai san cewa yana bakin yin abin da Allah kansa zai yi ba ne wajen bayar da Ɗansa ya zama fansa; duk da haka, ya yi biyayya, yana dab da miƙa Ishaku hadaya mala’ikan Jehovah ya hana shi. (Farawa 22:9-14) Jehovah ya riga ya faɗa cewa alkawuransa wajen Ibrahim za su cika ta wurin Ishaku. Saboda haka, Ibrahim ya nuna bangaskiyar cewa, idan bukata ta kama, Allah zai dawo da Ishaku daga matattu, ko da yake irin wannan abin bai taɓa faruwa ba. (Farawa 17:15-18; Ibraniyawa 11:17-19) Domin Ibrahim bai hana ɗansa ba, Jehovah ya ce: “Ta wurin zuriyarka kuma al’umman duniya za su sami albarka.” (Farawa 22:15-18) Wannan ya nuna cewa Ɗa da aka ambata a Farawa 3:15, Almasihu mai ceto, zai zo ne ta zuriyar Ibrahim. Lalle kuwa wannan gadō ne mai tamani da za a bayar!
7. Ta yaya Ibrahim, Ishaku, da Yakubu suka nuna godiya ga gadōnsu?
7 A lokacin Ibrahim bai san manufar abin da Jehovah yake yi ba; ko ɗansa Ishaku ko jikansa Yakubu, waɗanda suka zama “abokan tarayya ga gadōn alkawarin nan.” Amma duk sun dogara ga Jehovah. Ba su sa kansu cikin wani birnin mulki cikin ƙasar ba domin suna zuba ido ga abin da ya fi kyau—“birnin nan mai tushe, wanda mai fasarta shi, mai gina shi kuma, Allah ne.” (Ibraniyawa 11:8-10, 13-16) Duk da haka, ba dukan ’ya’yan Ibrahim ba ne suka nuna godiya ga tamanin gadōn da ya zo ta wurin Ibrahim.
Wasu da Suka Yi Banza da Gadōn
8. Ta yaya Isuwa ya nuna cewa ba shi da godiya ga tamanin gadōnsa?
8 Isuwa, babban ɗan Ishaku, ya ƙi nuna godiya ga hakkinsa na ɗan fari. Bai nuna godiya ba ga abubuwa masu tsarki. Sai wata rana Isuwa yana fama da yunwa, sai ya sayar da hakkinsa na ɗan fari ga ɗan’uwansa, Yakubu. Don me? Don a ba shi gurasa da jar miya kawai! (Farawa 25:29-34; Ibraniyawa 12:14-17) Al’ummar da alkawuran Allah wajen Ibrahim za su cika a kansu sun fito daga Yakubu ne, wanda Allah ya canja sunansa zuwa Isra’ila. Gadōn ya buɗe musu zarafin menene?
9. Saboda gadōnsu na ruhaniya, wane ceto ne aka yi wa ’ya’yan Yakubu, ko Isra’ila?
9 A lokacin wani yunwa, Yakubu da iyalinsa suka ƙaura zuwa Masar. A wajen suka riɓanɓanya suka yi yawa sosai, amma kuma sun zama bayi. Amma, Jehovah bai manta da alkawarinsa da Ibrahim ba. A lokacinsa, ya cece ’ya’yan Isra’ila daga bauta kuma ya gaya musu zai kai su cikin “kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci,” ƙasar da ya yi wa Ibrahim alkawarinta.—Fitowa 3:7, 8; Farawa 15:18-21.
10. A Dutsen Sinai, waɗanne aukuwa na ban al’ajibi ya faru game da gadōn ’ya’ya Isra’ila?
10 Yayin da ’ya’yan Isra’ila na kan hanyar zuwa Ƙasar Alkawarin, Jehovah ya tara su a Dutsen Sinai. A wajen ya ce musu: “In za ku yi biyayya da ni, ku kuma kiyaye maganata, za ku zama mutanena. Dukan duniya tawa ce, amma ku za ku zama zaɓaɓɓiyar jama’ata, za ku zama daular firistoci da al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.” (Fitowa 19:5, 6) Bayan mutanen cikin yardan rai da zuciya ɗaya suka yarda da wannan, Jehovah ya ba su Dokarsa—wani abin da bai taɓa yi wa wasu mutane ba.—Zabura 147:19, 20.
11. Menene wasu abubuwa masu tamani da ke ƙunshe cikin gadōn ’ya’yan Isra’ila?
11 Lalle sabuwar al’ummar nan ta sami gadō na ruhaniya! Suna bauta wa Allah na gaskiya shi kaɗai. An cece su daga Masar sun kuma ga aukuwa na ban al’ajabi lokacin da aka ba da Doka a Dutsen Sinai. Sun sami ƙarin darajar gadōnsu ta wurin “zantuttuka na Allah” da annabawa suka yi. (Romawa 3:1, 2) Jehovah ya zaɓe su su zama shaidunsa. (Ishaya 43:10-12) Ɗa Almasihun zai fito daga cikin al’ummarsu ne. Dokar ta yi nuni wajensa, ta sakankance shi, kuma ta taimake su su fahimci bukatarsu wajensa. (Galatiyawa 3:19, 24) Bugu da ƙari, za a ba su zarafi na yin hidima tare da Ɗa Almasihun su zama mulkin firistoci da kuma al’umma mai tsarki.—Romawa 9:4, 5.
12. Ko da sun shiga Ƙasar Alkawarin, menene Isra’ilawa ba su shiga ba? Me ya sa?
12 Gaskiya ga alkawarinsa, Jehovah ya jagabanci Isra’ilawa zuwa Ƙasar Alkawari. Amma kamar yadda manzo Bulus ya bayyana daga baya, domin rashin bangaskiyarsu, ƙasar ba ta zama musu ‘inuwa’ da gaske ba. Rukuninsu, bai shiga cikin “inuwar Allah” ba domin sun ƙi fahimi da kuma tafiya daidai da dalilin ranar nan ta hutun Allah, wanda ya fara bayan halittar Adamu da Hauwa’u.—Ibraniyawa 4:3-10.
13. Domin sun ƙi nuna godiya ga gadōnsu na ruhaniya, menene al’ummar Isra’ila ta yi hasara?
13 Da za a samu cikakken adadin waɗanda za su yi tarayya da Almasihu cikin Mulki na samaniya daga Isra’ila ta jiki su zama daular firistoci kuma al’umma mai tsarki. Amma ba su da godiya game da gadōnsu mai tamani. Isra’ilawa na jiki kalilan ne kawai suka amince da Almasihu lokacin da ya zo. Sakamakon haka, adadi kaɗan ne kawai suka sami shiga cikin mulkin firistoci da aka annabta. An ɗauke Mulkin daga hannun Isra’ila ta jiki aka ba “al’umma wadda za ta ba da amfani nagari.” (Matiyu 21:43) Wace al’umma ke nan?
Gadō Cikin Sammai
14, 15. (a) Bayan mutuwar Yesu, ta yaya al’ummai suka fara yi wa kansu albarka ta wurin ‘ɗan’ Ibrahim? (b) Menene waɗanda suke cikin ‘Isra’ila ta Allah’ suka samu gado?
14 Al’ummar da aka ba su Mulkin ‘Isra’ila ta Allah,’ Isra’ila ta ruhaniya ce, wadda adadinsu 144,000 mabiyan Yesu Kristi ne na ruhu. (Galatiyawa 6:16; Wahayin Yahaya 5:9, 10; 14:1-3) Wasu cikin waɗannan 144,000 Yahudawa ne, amma yawanci daga Al’ummai ne na duniya. Ta haka, alkawarin Jehovah ga Ibrahim cewa ta wurin ‘ɗansa’ al’ummai duka za su sami albarka ya fara cika. (Ayyukan Manzanni 3:25, 26; Galatiyawa 3:8, 9) A cikar farko, an shafe mutane na al’ummai da ruhu mai tsarki kuma Jehovah Allah ya ɗauke su su zama ’ya’yansa na ruhu, ’yan’uwan Yesu Kristi. Da haka, su ma sun zama sashe na biyu na ‘ɗan.’—Galatiyawa 3:28, 29.
15 Kafin mutuwarsa, Yesu ya gabatar da Yahudawa, waɗanda za su kasance cikin sabuwar al’ummar da jininsa da ya ba da darajar sabon alkawarin. Domin dalilin bangaskiyarsu a darajar hadayar, waɗanda suke cikin alkawarin za su zama ‘kamiltattu har abada.’ (Ibraniyawa 10:14-18) Za a iya ‘ce da su masu adalci’ kuma an gafarta musu zunubansu. (1 Korantiyawa 6:11) Da haka, suna kama da Adamu kafin ya yi zunubi. Amma dai, waɗannan ba cikin aljanna ta duniya za su zauna ba. Yesu ya ce zai shirya musu wuri a sama. (Yahaya 14:2, 3) Sun ba da damarsu ta duniya domin su sami ‘gadōn da aka ajiye musu cikin sammai.’ (1 Bitrus 1:4) Menene za su yi a wajen? Yesu ya bayyana: ‘Na yi muku alkawarin . . . mulki.’—Luka 22:29.
16. Wane aiki mai girma yake a gaban shafaffu Kirista?
16 Daga sammai, waɗanda za su yi sarauta da Kristi cikin wasu abubuwan da za su yi, shi ne za su taimaka wajen kawar da tawaye wa ikon mallaka na Jehovah. (Wahayin Yahaya 2:26, 27) Tun da yake su sashe na biyu ne na zuriyar ruhaniya ta Ibrahim, za su saka hannu wajen kawo rayuwa ta albarka kamilcacce ga mutane na dukan al’ummai. (Romawa 8:17-21) Gadō mai tamani kuwa da suke da shi!—Afisawa 1:16-18.
17. Wane fannin gadōnsu ne shafaffu Kiristoci suke morewa yayin da suke duniya?
17 Amma gadō na shafaffun mabiyan Yesu ba gaba ɗaya ne na nan gaba ba. A hanyar da babu wanda zai iya, Yesu ya taimake su su san Jehovah, shi kaɗai Allah na gaskiya. (Matiyu 11:27; Yahaya 17:3, 26) Ta wurin kalma da kuma misali, ya koya musu abin da ‘dogara ga Jehovah’ yake nufi da kuma abin da biyayya ga Jehovah ya ƙunsa. (Ibraniyawa 2:13; 5:7-9) Yesu ya ba su amanar sani na gaskiya game da nufin Allah kuma ya tabbatar musu cewa ruhu mai tsarki zai shugabance su su ƙara fahimtar shi. (Yahaya 14:24-26) Ya sahinta cikin azantai da zukatansu muhimmancin Mulkin Allah. (Matiyu 6:10, 33) Yesu kuma ya ba su amanar aikin yin wa’azi da kuma almajirantar na mutanen Urushalima, Yahudiya, Samariya, da manisantar duniya.—Matiyu 24:14; 28:19, 20; Ayyukan Manzanni 1:8.
Gadō Mai Tamani ga Babban Garke
18. A wace hanya ce alkawarin Jehovah na cewa dukan al’ummai za su albarkaci kansu ta wurin ‘ɗan’ Ibrahim yake cika a yau?
18 Hakika, an riga an zaɓi cikakken adadin Isra’ila ta ruhaniya, “ƙaramin garke” na masu tarayyar Mulki. (Luka 12:32) Shekaru da yawa yanzu, Jehovah ya mai da hankali wajen tattara babban garke na wasu tumaki daga dukan al’ummai. Da haka, alkawarin Jehovah ga Ibrahim cewa ta wurin ‘ɗansa’ dukan al’ummai za su albarkaci kansu yana cika a hanya mai girma. Abin farin ciki waɗannan su ma suna hidima tsarkaka ga Jehovah kuma sun gane cewa cetonsu ya dangana ne ga bangaskiya cikin Ɗan Ragon Allah, Yesu Kristi. (Wahayin Yahaya 7:9, 10) Ka yi na’am da gayyatar Jehovah mai kyau don ka zama tsakanin rukunin nan mai farin ciki?
19. Ga wane gadō ne al’ummai da aka albarkace su a yanzu suke zuba ido?
19 Wane gadō mai tamani ne Jehovah ya ba waɗanda ba sa cikin ƙaramin garke? A’a, ba gadō na cikin sammai ba. Gadō ne wanda da Adamu ya ba wa ’ya’yansa—damar rai madawwami cikin kamilcewa cikin aljanna da ta kewaye duniya. Za ta zama duniya ce da “ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.” (Wahayin Yahaya 21:4) A gare ku ne fa, hurarren Kalmar Allah ta ce: “Ka dogara ga Ubangiji ka aikata nagarta, ka zauna a ƙasar, ka sami lafiya. Ka nemi farin cikinka a wurin Ubangiji, zai kuwa biya maka bukatarka. A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe . . . Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar, su ji daɗin cikakkiyar salama. Adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar, su gāje ta har abada.”—Zabura 37:3, 4, 10, 11, 29.
20. Ta yaya ne “waɗansu tumaki” suke more gadō na ruhaniya na shafaffun Kiristoci?
20 “Waɗansu tumaki” na Yesu suna da gadō cikin duniya wanda yake sashe ne na Mulkin samaniya. (Yahaya 10:16a) Ko da yake ba za su zauna a sammai ba, gadō na ruhaniya da shafaffu suke da shi zai kai wajensu. Ta wurin haɗaɗɗen rukuni na shafaffu “amintaccen bawan nan mai hikima” ne, waɗansu tumaki suka sami fahimtar alkawura masu tamani waɗanda ke ƙunshe cikin Kalmar Allah. (Matiyu 24:45-47; 25:34) Tare yanzu shafaffu da waɗansu tumaki suke bauta wa Allah na gaskiya, Jehovah. (Yahaya 17:20, 21) Tare suke godiya ga darajar kafarar zunubi da hadayar Yesu ta yi. Suna bauta tare a garke guda ƙarƙashin Makiyayi ɗaya, Yesu Kristi. (Yahaya 10:16b) Dukansu suna cikin ’yan’uwanci na dukan duniya. Suna sa hannu tare cikin gata na zama Shaidun Jehovah da na Mulkinsa. I, idan kai bawan Jehovah ne da ka keɓe kai ka yi baftisma, dukan wannan yana haɗe cikin gadōnka na ruhaniya.
21, 22. Ta yaya dukanmu za mu nuna cewa muna godiya ga gadōnmu na ruhaniya?
21 Wannan gadōn da tamani yake a gare ka kuwa? Kana ɗaukansa da girma sosai don ka sa yin nufin Allah ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarka? A nuna haka, kana bin gargaɗin Kalmarsa da na ƙungiyarsa, ka kasance kullum a dukan taro na ikklisiyar Kirista? (Ibraniyawa 10:24, 25) Gadōn nan yana da daraja a gare ka da zai sa ka ci gaba da bauta wa Allah ko kana cikin wahala? Godiyarka ga wannan yana da ƙarfi sosai don ya ƙarfafa ka ka tsayayya wa jarabar bin tafarki da zai sa ka ƙi shi?
22 Bari dukanmu mu rungume gadōn nan na ruhaniya da Allah ya ba mu. Da muke kafa idanunmu sosai a kan Aljanna na nan gaba, bari mu shagala sosai cikin gata na ruhaniya da Jehovah yake ba mu a yanzu. Ta wurin gina rayuwarmu a kewaye da dangantakarmu da Jehovah, muna ba da tabbacin yadda muke ɗaukan gadō da Allah ya bayar da tamani sosai. Bari mu kasance tsakanin waɗanda suke cewa: “Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina, zan yi maka godiya har abada abadin.”—Zabura 145:1.
Yaya Za Ka Bayyana?
• Da a ce Adamu ya yi aminci ga Allah, da wane gadō zai bar mana?
• Yaya ’ya’yan Ibrahim suka ɗauki gadōn da aka ba su?
• Menene ke ƙunsa cikin gadōn shafaffu mabiyan Kristi?
• Menene gadō na babban garke, kuma ta yaya za su iya nuna cewa suna da godiya game da shi?
[Hotuna a shafi na 28]
’Ya’yan Ibrahim sun samu alkawarin gadō mai tamani
[Hotuna a shafi na 31]
Kana nuna godiya ga gadōnka na ruhaniya?