Shuka Iri Na Gaskiyar Mulki
“Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka.”—MAI-WA’AZI 11:6.
1. A wace hanya ce Kiristoci suke shuka iri a yau?
NOMA babban abu ne a cikin al’ummar Ibraniyawa ta dā. Shi ya sa Yesu, wanda ya yi rayuwarsa ta mutum a cikin Ƙasar Alkawari ya yi amfani da batutuwa da kuma misalai na noma. Alal misali, ya kamanta yin wa’azin bisharar Mulkin Allah da shuka iri. (Matta 13:1-9, 18-23; Luka 8:5-15) Har wa yau, ko muna rayuwa cikin al’umma da ake noma ko babu, shuka iri na ruhaniya aiki ne mafi muhimmanci da Kiristoci suke yi.
2. Yaya muhimmancin aikinmu na wa’azi yake, kuma menene wasu abubuwa da ake yi don a cim ma wannan a yau?
2 Babbar gata ce mu sa hannu cikin shuka gaskiyar Littafi Mai-Tsarki a cikin wannan lokaci na ƙarshe. Romawa 10:14, 15 sun yi bayanin muhimmancin wannan aiki: “Ƙaƙa za su ji kuwa in ba mai-yin wa’azi ba? ƙaƙa za su yi wa’azi kuma, in ba a aike su ba? kamar yadda an rubuta, Ina misalin jamalin ƙafafu na masu-kawo bishara ta alheri!” Yanzu ne ya fi muhimmanci a yi gaba sosai da hali mai kyau a cika wannan aiki da Allah ya bayar. Saboda haka ne Shaidun Jehovah suka shagala sosai a buga Littafi Mai-Tsarki da kuma rarrabawa tareda kayan nazarin Littafi Mai-Tsarki cikin harsuna 340. Shirya waɗannan ya bukaci masu aiki da suka ba da kansu, sama da 18,000 a hedkwatar su da kuma a ofisoshin rassa a ƙasashe dabam dabam. Shaidu kusan miliyan shida ne suke sa hannu a rarraba wannan littattafai na Littafi Mai-Tsarki a duniya duka.
3. Menene ake cim ma wa ta wajen shuka gaskiyar Mulkin?
3 Mecece albarkar wannan aiki tuƙuru? Yadda yake a zamanin Kiristanci na farko, da yawa a yau suna karɓan gaskiya. (Ayukan Manzanni 2:41, 46, 47) Amma, mafi muhimmanci shi ne yawan adadin sababbi masu shelar Mulki da aka yi wa baftisma ya nuna cewa wannan shaida mai girma ta haɗa da tsarkake sunan Jehovah da kunita shi, Allah na gaskiya shi kaɗai. (Matta 6:9) Ƙari ga haka, sanin Kalmar Allah yana gyara rayukan mutane da yawa kuma yana kai wa ga cetonsu.—Ayukan Manzanni 13:47.
4. Yaya yawar damuwar da manzannin suka yi game da mutane da suke yi wa wa’azi?
4 Manzannin sun san muhimmancin ba da rai da bisharar take da shi, kuma suna juyayin waɗanda suke yi musu wa’azi. Wannan sarai yake a cikin kalmomin manzo Bulus, yayin da ya rubuta: “Domin muna marmarinku da soyayya, muka ji daɗin ba ku, ba bisharar Allah kaɗai ba, amma har da rayukanmu, gama kun zama abin ƙauna ƙwarai garemu.” (1 Tassalunikawa 2:8) A nuna irin soyayya na ƙwarai ga mutane, Bulus da wasu manzanni suna yin koyi ne da Yesu da mala’iku na sama, da sun sa hannu cikin wannan aiki na cetan rai. Bari mu sake bincika matsayi na musamman da waɗannan bayi na samaniya na Allah suke da shi a shuka gaskiyar Mulki, mu ga kuma yadda misalinsu zai ƙarfafa mu mu cika aikinmu.
Yesu—Mai Shuka Gaskiyar Mulki
5. A wane aiki ne Yesu ya shagala musamman lokacin da yake duniya?
5 Yesu, kamiltaccen mutum yana da ikon ya tanadar da abubuwa masu kyau da yawa ga mutane na zamaninsa. Alal misali, da ya warware matsalar rashin magani ko kuma da ya gabatar da wani fahimi na ’yan Adam a zancen kimiyya. Amma, tun da wuri a lokacin hidimarsa ya bayyana cewa aikinsa na yin wa’azin bishara ne. (Luka 4:17-21) Kuma a kusa da ƙarshen hidimarsa, ya yi bayani: “Domin wannan an haife ni. Domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya.” (Yohanna 18:37) Saboda haka, ya shagala sosai cikin shuka iri na gaskiyar Mulki. Koya wa waɗanda suke a lokacinsa game da Allah da Nufe-Nufensa ya fi muhimmanci da wani ilimi da Yesu zai koya musu.—Romawa 11:33-36.
6, 7. (a) Wane babban alkawari ne Yesu ya yi kafin ya haura zuwa sama, kuma yaya yake cika shi? (b) Ta yaya halin Yesu wajen aikin wa’azin ke taɓa ka?
6 Yesu ya kira kansa Mai Shuka gaskiyar Mulki. (Yohanna 4:35-38) Kowane zarafi da ya samu yana yaɗa iri na bishara. Ko lokacin mutuwarsa a kan gungume, ya yi shelar bishara game da aljanna ta duniya ta nan gaba. (Luka 23:43) Bugu da ƙari, yadda ya damu sosai a yin wa’azin bishara ba ta ƙare da mutuwarsa a kan gungume da ya sha azaba ba. Kafin ya haura zuwa sama, ya umurci manzanninsa su ci gaba da shuka iri na gaskiyar Mulkin, su almajirantar kuma. Sai kuma Yesu ya yi babban alkawari. Ya ce: “Ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.”—Matta 28:19, 20.
7 Da waɗannan kalmomin, Yesu ya yi alkawari cewa zai agaza, ya ja-goranci, kuma ya kāre aikin wa’azin bishara “kullayaumi har matuƙar zamani.” Har zuwa wannan zamanin namu, Yesu yana ci gaba da nuna marmari a aikin bisharanci. Shi ne Shugabanmu, mai kula da shuka irin gaskiyar Mulki. (Matta 23:10) Wanda shi ne Shugaban ikklisiyar Kirista, yana da hakkin wannan aiki na duniya duka a gaban Jehovah.—Afisawa 1:22, 23; Kolossiyawa 1:18.
Mala’iku Suna Shelar Bishara
8, 9. (a) Ta yaya mala’iku suka nuna marmari sosai cikin harkokin ’yan Adam? (b) A yaya za a ce mu abin kallo ne a gaban mala’iku?
8 Yayin da Jehovah ya halicci duniya, mala’iku “suka yi waƙa . . . suka yi sowa don farinciki.” (Ayuba 38:4-7) Tun daga lokacin, waɗannan halittu na sama suka nuna marmari sosai cikin harkokin ’yan Adam. Jehovah ya yi amfani da su wajen idar da saƙonninsa ga ’yan Adam. (Zabura 103:20) Wannan gaskiya ne musamman wajen yaɗa bishara a kwanakinmu. A cikin ru’uya da aka ba shi, manzo Yohanna ya ga wani “mala’ika kuma yana firiya a tsakiyar sararin sama” wanda yake da “bishara ta har abada wadda za ya yi shelarta ga mazaunan duniya, ga kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma; da babbar murya kuwa ya ce, Ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja; gama sa’ar hukuncinsa ta zo.”—Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7.
9 Littafi Mai-Tsarki ya ce mala’iku su “ruhohi masu-hidima ne, aikakku domin su yi hidima sabili da waɗanda za su gaji ceto.” (Ibraniyawa 1:14) Yayin da mala’ikun suke cika ayyuka da aka ba su, suna da zarafi su lura da mu da aikinmu. Kama yake cewa muna tsaye a kan dakalin babban ɗakin wasa a fili, muna yin aikinmu a gaban jama’a da ke a sama. (1 Korinthiyawa 4:9) Lallai wannan yana sa mu natsuwa da farin ciki cewa ba mu kaɗai ba ne ke aikin shuka gaskiyar Mulkin!
Mun Ɗokanta Mu Cika Aikinmu
10. Yaya za a iya yin amfani da shawara mai aikawa da ke a Mai-Wa’azi 11:6?
10 Me ya sa Yesu da mala’iku suke da marmari cikin aikinmu haka? Yesu ya ba da dalili ɗaya yayin da ya ce: “Ina ce maku, akwai murna a wurin mala’ikun Allah a kan mai-zunubi guda ɗaya wanda ya tuba.” (Luka 15:10) Mu ma muna nuna marmari na ƙwarai wajen mutane. Shi ya sa, muke yin iyakacin ƙoƙarinmu mu yaɗa irin gaskiyar Mulki a ko’ina. Za a iya amfani da kalmomin Mai-Wa’azi 11:6 wa aikinmu. A wajen, Littafi Mai-Tsarki ya yi mana kashedi: “Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka; gama ba ka san wanda za ya yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuwa duk za su yi kyau baki ɗaya.” Gaskiya ne, idan mutum ɗaya ya yi na’am da saƙonmu, da akwai ɗarurruwa ko dubbai da suke ƙin sa. Amma kamar mala’iku, muna yin murna yayin da “mai-zunubi” ɗaya ya karɓi saƙon ceto.
11. Yaya yin amfani da littattafai na Littafi Mai-Tsarki yake da amfani sosai?
11 Da akwai abubuwa da yawa cikin yin wa’azin bishara. Abu guda na taimako cikin wannan aiki shi ne littattafai na Littafi Mai-Tsarki da Shaidun Jehovah suke amfani da su. A wata sassa, waɗannan littattafai kama suke da iri da ake yaɗawa a ko’ina. Ba mu san inda za su yi nasara ba. Wasu lokatai, littafi yakan shiga hannun mutane dabam dabam kafin wani ya samu ya karanta. Yana yiwuwa cewa Yesu da mala’iku su sa abubuwa su faru domin masu zuciyar kirki su amfana. Ga wasu abubuwan da suka faru da ke nuna yadda Jehovah yake sa a samu sakamakon da ba a yi tsammaninsa ba wajen littattafai da aka bari a hannun mutane.
Aikin Allah na Gaskiya
12. Yaya tsohuwar jarida ta taimaki wani iyali suka zo ga sanin Jehovah?
12 A shekara ta 1953, Robert, Lila, da ’ya’yansu suka kaura daga babban birni zuwa wani tsohon gida a karkara a Pennsylvania, U.S.A. Ba da daɗewa ba bayan da suka kaura, sai Robert ya ce zai gina wajen wanka a bayan wata matakala. Bayan ya kwashe kwalaye da yawa, sai ya ga cewa a bayan, ɓeraye sun tara falle-falle da yawa, da ɓawon gyaɗa, da wasu tarkace. A wajen, cikin dukan waɗannan, ga jaridar The Golden Age. Talifin da ke zancen renon yara ne ya kwashi hankalin Robert. Bayanin Littafi Mai-Tsarki da aka yi cikin jaridar ya burge shi sosai, ya gaya wa Lila cewa za su fara bin “addinin Golden Age.” Cikin ’yan makonni kawai, Shaidun Jehovah suka zo ƙofarsu, amma Robert ya gaya musu cewa “addinin Golden Age” ne kawai iyalin suke so. Shaidun suka yi musu bayani cewa yanzu an sake sunan Golden Age zuwa Awake! Robert da Lila suka fara nazarin Littafi Mai-Tsarki babu fasawa da Shaidun, daga baya kuma suka yi baftisma. Su ma, suka shuka irin gaskiya cikin ’ya’yansu suka yi girbi mai yawa. Yau, mutane fiye da 20 cikin iyalin nan, haɗe da dukan ’ya’ya bakwai na Robert da Lila, bayin Jehovah Allah ne da suka yi baftisma.
13. Menene ya sa mata da miji a Puerto Rico su yi marmari cikin Littafi Mai-Tsarki?
13 Shekara 40 da ya shige, William da Ada, mata da miji ne daga Puerto Rico, ba su da marmari su yi nazarin Littafi Mai-Tsarki. Kowane lokaci da Shaidun Jehovah suka ƙwanƙwasa musu ƙofa, sukan yi kamar ba sa gida. Wata rana William ya je wani matattarin gwanjo don ya sayi wani abu don yin gyara a gida. Da yake barin wajen, sai ya ga wani littafi mai launi kore cikin kwandon shara. Littafin nan Religion ne, wanda Shaidun Jehovah suka buga can a shekara ta 1940. William ya kai littafin gida da farin ciki ya karanta game da bambanci tsakanin addinin ƙarya daga na gaskiya. Wani lokaci da Shaidun Jehovah suka ziyarce su, William da Ada suka saurari saƙonsu da farin ciki suka fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da su. Bayan watanni aka yi musu baftisma a Taron Dukan Ƙasashe na Nufin Allah a 1958. Tun daga lokacin, sun riga sun taimaka wa mutane 50 su zama cikin ’yan’uwanci na Kirista.
14. Yadda wani labari ya nuna, wane amfani ne littattafanmu na Littafi Mai-Tsarki ke da shi?
14 Shekaran Karl 11 ne kawai, amma fitinanne ne. Yana yawan faɗawa matsifa. Ubansa, wani mai wa’azi mabiyin Methodi na Jamus, ya koya masa cewa za a ƙona masu mugunta a jahannama bayan sun mutu. Saboda haka, Karl yana tsoron jahannama sosai. Wata rana a shekara ta 1917, Karl ya ga wani falle mai rubutu a kan titi, ya ɗauka. Da yake karantawa, nan da nan sai ya ga tambayar nan: “Menene jahannama?” Fallen gayyata ne zuwa wajen wani jawabi game da jahannama, na Ɗaliban Littafi Mai-Tsarki, da aka san su a yau da Shaidun Jehovah. Kusan shekara guda daga baya, bayan nazarin Littafi Mai-Tsarki sau da yawa, Karl ya yi baftisma, ya zama ɗaya cikin Ɗaliban Littafi Mai-Tsarki. A shekara ta 1925 aka kira shi zuwa aiki a hedkwatar Shaidun Jehovah na duniya duka—inda har yanzu yake hidima. Aiki na Kirista da ya ci shekara tamanin ya fara da falle a kan titi.
15. Menene Jehovah zai yi yadda ya ga ya dace?
15 Hakika, ya wuce iyawar mutum a san yadda mala’iku suka sa hannu dab da dab cikin waɗannan labaran. Duk da haka, kada mu yi tantamar cewa Yesu da mala’iku suna da aiki mai girma a cikin aikin wa’azin kuma cewa Jehovah zai bi da al’amura yadda ya ga ya dace. Waɗannan tare da makamancinsu suna nuna amfani mai kyau da littattafanmu suke da shi bayan mun bayar da su ga wasu.
An Ba Mu Amanar Kaya Mai Daraja
16. Menene za mu iya koya daga kalmomin 2 Korinthiyawa 4:7?
16 Manzo Bulus ya yi maganar “kaya mai-daraja cikin tukwane na ƙasa.” Kaya mai daraja ita ce aikin wa’azi da Allah ya ba mu, kuma tukwane na ƙasa su ne mutane da Jehovah ya ba su amanar wannan kaya mai darajar. Tun da shi ke mutane ajizai ne da ke da iyaka, Bulus ya ci gaba da cewa sakamakon wannan aiki ya zama “domin mafificin girman iko ya kasance na Allah, ba daga wurin mu da kanmu ba.” (2 Korinthiyawa 4:7) Hakika, za mu iya jira Jehovah ya ba da iko da muke bukata don taimaka mana mu cim ma aikin da muke da shi.
17. Menene za mu fuskanta yayin da muke shuka irin gaskiyar Mulki, kuma me ya sa ko da yaya za mu ci gaba da hali mai kyau?
17 Sau da yawa mukan yi sadaukarwa. Zai iya zama da wuya ko kuma babu zarafi a yi aiki a wasu yankuna. Da akwai wasu wurare da yawancin mutane ba su da marmari sam sam, har ba shi da sauƙi a bi da su. Mai-yiwuwa ana aiki sosai a irin waɗannan wurare babu nasara. Amma babu wani ƙoƙarin da ya wuce kima idan an gwada da abin da ke a gaba. Ka tuna cewa, iri da ka shuka zai sa mutane farin ciki yanzu kuma su sami rai na har abada a nan gaba. Kalmomin Zabura 126:6 sau da yawa sun zama gaskiya: “Ko da yana tafiya yana kuka, yana ɗauke da ƙwaryar iri; Za ya dawo kuma da guɗa, yana kawo dammunansa.”
18. Ta yaya za mu mai da hankali kullum ga hidimarmu, kuma me ya sa ya kamata za mu yi hakan?
18 Bari mu yi amfani da kowane zarafi don shuka irin gaskiyar Mulki sosai. Kada mu manta dai, ko da yake mu ne muke shuka kuma muke ba da ruwa, Jehovah ne mai sa ya yi girma. (1 Korinthiyawa 3:6, 7) Hakika, kamar yadda Yesu da mala’iku suke yin nasu sashen aikin, Jehovah yana bukatar mu cika hidimarmu sosai. (2 Timothawus 4:5) Bari mu mai da hankali kullum ga koyarwanmu, ga halinmu, da yadda muke ɗoki cikin hidima. Me ya sa? Bulus ya amsa: “Garin yin wannan za ka ceci kanka duk da masu-jinka.”—1 Timothawus 4:16.
Me Muka Koya?
• A waɗanne hanyoyi ne aikinmu na shuki ke kawo sakamako masu kyau?
• Yaya ne Yesu Kristi da mala’iku suke sa hannu cikin aikin bishara a yau?
• Me ya sa bai kamata mu sake hannu ba a shuka gaskiyar Mulki?
• Yayin da muka gamu da rashin marmari ko ƙiyayya cikin hidimarmu, me ya kamata ya motsa mu mu nace?
[Hoto a shafi na 27]
Kamar manoma a Isra’ila ta dā, Kiristoci a yau suna yaɗa irin gaskiyar Mulki sosai
[Hotuna a shafuffuka na 28, 29]
Shaidun Jehovah suna buga littattafan Littafi Mai-Tsarki dabam dabam kuma rarrabawa cikin harsuna 340