WAƘA TA 50
Alkawarin Bauta wa Jehobah
Hoto
1. Na ba Allah zucina
Don ta so dokokinsa.
Na ba Allah muryata
Don ta rera mai yabo.
2. Ya Jehobah Allahna,
Na ba ka rayuwata
Da kuma wadatata,
Don in bi umurninka.
3. Allah ka taimaka min
Domin in yi nufinka.
Bari duk ayyukana
Su faranta maka rai.
(Ka kuma duba Zab. 40:8; Yoh. 8:29; 2 Kor. 10:5.)