WAƘA TA 49
Mu Riƙa Faranta Ran Jehobah
Hoto
(Misalai 27:11)
1. Uba, mun yi alkawari,
Alkawarin bauta maka.
Muna so mu yi biyayya
Domin mu faranta ranka.
2. Wakilinka a duniya
Yana yin shelar girmanka,
Yana ciyar da mu sosai
Don mu riƙa yin nufinka.
3. Ka ba mu ruhunka, Allah,
Domin mu riƙe aminci.
Hakan zai sa mu yabe ka
Kuma mu faranta ranka.
(Ka kuma duba Mat. 24:45-47; Luk. 11:13; 22:42.)