Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 82 p. 192-p. 193 par. 2
  • yesu-ya-koya-yin-addu’a

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • yesu-ya-koya-yin-addu’a
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Game da Addu’ar da Allah Yake Sauraro
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Jawowa Kurkusa da Allah Cikin Addu’a
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 82 p. 192-p. 193 par. 2
Wani Bafarisi yana addu’a a gaban jama’a kuma mutane sun tsaya suna kallon sa

DARASI NA 82

Yesu Ya Koya wa Almajiransa Yin Addu’a

Dukan abubuwan da Farisawa suke yi don su burge mutane ne. Suna yin abin kirki don a san da su. Suna addu’a a fili domin kowa ya gan su. Farisawa suna haddace addu’o’i kuma su ta maimaitawa a cikin majami’u da kuma kan titi don mutane su ji cewa suna addu’a. Saboda haka, mutane sun yi mamaki sosai sa’ad da Yesu ya ce: ‘Kada ku yi addu’a kamar Farisawa. Domin suna tunanin cewa addu’o’insu za su burge Allah. Amma ƙarya suke yi. Addu’a tsakanin ka ne da Jehobah. Ka daina maimaita kalmomi iri ɗaya. Jehobah yana so ka gaya masa abin da ke zuciyarka.

Wani yaro ya tsuguna yana addu’a

‘Ga yadda ya kamata ku riƙa yin addu’a: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka ya zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” ’ Yesu ya kuma ce su roƙi Allah ya ba su abincin da za su ci, ya kuma gafarta laifofinsu. Za su iya gaya masa wasu abubuwan da ke damunsu.

Yesu ya ce: ‘Ku riƙa yin addu’a. Ku riƙa roƙon Ubanku Jehobah don ya ba ku abubuwa masu kyau. Dukan iyaye suna so su ba yaransu abu mai kyau. Shin idan yaronka ya ce ka ba shi burodi, za ka miƙa masa dutse ne? Ko kuma idan ya ce ka ba shi kifi, za ka ba shi maciji?’

Bayan haka, sai Yesu ya faɗi darasin: ‘Idan kana ba yaranka abubuwa masu kyau, shin Ubanku Jehobah ma ba zai ba ka ruhu mai tsarki ba? Babu shakka, idan ka roƙa, zai ba ka.’ Kana bin shawarar Yesu kuwa? Waɗanne abubuwa kake roƙa sa’ad da kake addu’a?

‘Ku riƙa roƙa, za a ba ku; ku riƙa nema, za ku samu; ku riƙa ƙwanƙwasa, za a buɗe muku.’​—Matta 7:7

Tambayoyi: Mene ne Yesu ya ce sa’ad da yake koya wa almajiransa yin addu’a? Kana addu’a Allah ya ba ka abubuwan da kake so sosai?

Matta 6:​2-18; 7:​7-11; Luka 11:13

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba