Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • bhs babi na 18 pp. 185-196
  • Alkawarin Yin Nufin Allah da Kuma Baftisma

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Alkawarin Yin Nufin Allah da Kuma Baftisma
  • Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Karanta a Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • NAZARI DA BANGASKIYA
  • KA KOYA WA WASU GASKIYAR DA KE LITTAFI MAI TSARKI
  • KA TUBA KUMA KA JUYO
  • KA YI ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH
  • KADA KA JI TSORON CEWA BA ZA KA IYA RIƘE ALKAWARINKA BA
  • NUNA WA KOWA CEWA KANA SO KA YI NUFIN JEHOBAH
  • ABIN DA BAFTISMAR DA KA YI TAKE WAKILTA
  • Ka Shirya Yin Baftisma Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Me Ya Sa Ya Kamata Ka Yi Baftisma?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Me Ya Sa Za Ka Yi Alkawarin Bauta wa Allah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Na Shirya Yin Baftisma Kuwa?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
bhs babi na 18 pp. 185-196

BABI NA SHA TAKWAS

Alkawarin Yin Nufin Allah Da Kuma Baftisma

1. Wane tunani za ka iya yi bayan ka yi nazarin wannan littafin sosai?

BABU SHAKKA, ka koyi abubuwa da yawa a cikin wannan littafin kamar su alkawarin da aka yi mana na rai na har abada da yanayin matattu da kuma tashin matattu. (Mai-Wa’azi 9:5; Luka 23:43; Yohanna 5:28, 29; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Wataƙila ka soma zuwa taron Shaidun Jehobah kuma ka fahimci cewa su ne suke bin Allah da gaske. (Yohanna 13:35) Ƙari ga haka, mai yiwuwa ka soma ƙulla dangantaka da Jehobah kuma ka tsai da shawarar bauta masa. Saboda haka, za ka iya tunani, ‘Me ya kamata in yi yanzu don in bauta wa Allah?’

Filibus da Bahabashe ma’aikacin kotu

2. Me ya sa wani Bahabashe ya so a yi masa baftisma?

2 Abin da wani Bahabashe da ya yi rayuwa a zamanin Yesu ya yi tunani a kai ke nan. Ba da daɗewa ba bayan da aka ta da Yesu daga mutuwa, almajirinsa Filibus ya yi wa mutumin wa’azi. Filibus ya tabbatar masa da cewa Yesu shi ne Almasihu. Bahabashen ya ji daɗin abin da ya koya sosai sai nan da nan ya ce: “Ga ruwa; me za ya hana a yi mini baftisma?”—Ayyukan Manzanni 8:26-36.

3. (a) Wace doka ce Yesu ya ba wa mabiyansa? (b) Yaya ya kamata a yi wa mutum baftisma?

3 Littafi Mai Tsarki ya koyar dalla-dalla cewa ya kamata duk wanda yake son ya bauta wa Jehobah ya yi baftisma. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: ‘Ku almajirtar da dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma.’ (Matta 28:19) Yesu da kansa ya yi baftisma don ya kafa mana misali mai kyau. An nitsar da shi gaba ɗaya cikin ruwa, ba yayyafa ruwa a kansa aka yi ba. (Matta 3:16) Haka ma a yau, idan za a yi wa wani baftisma, wajibi ne a nitsar da shi cikin ruwa.

4. Mene ne yin baftisma yake nunawa?

4 Yin baftisma yana nuna wa mutane cewa kana son ka zama aminin Allah kuma ka bauta masa. (Zabura 40:7, 8) Za ka iya yin tunani, ‘Me nake bukatar yi don in yi baftisma?’

NAZARI DA BANGASKIYA

5. (a) Me ya kamata ka yi kafin ka yi baftisma? (b) Me ya sa taron Shaidun Jehobah suke da muhimmanci?

5 Kafin ka yi baftisma, wajibi ne ka san Jehobah da kuma Yesu. Nazarin Littafi Mai Tsarki da kake yi yanzu ya nuna cewa ka soma yin hakan. (Karanta Yohanna 17:3.) Amma yin hakan ba shi ne kawai abin da ake bukata ba. Littafi Mai Tsarki ya ce dole mu ‘cika da sanin nufin’ Jehobah. (Kolosiyawa 1:9) Taron da Shaidun Jehobah suke yi za su taimaka maka wajen sa dangantakarka da Jehobah ta yi ƙarfi. Wannan dalili ɗaya ne da ya sa zuwa taronsu babu fashi yake da muhimmanci.—Ibraniyawa 10:24, 25.

Shaidun Jehobah guda biyu suna nazarin Littafi Mai Tsarki da wani mutum

Wajibi ne ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kafin ka yi baftisma

6. Ya kamata ka san kome da ke Littafi Mai Tsarki ne kafin ka yi baftisma?

6 Hakika, Jehobah ba ya bukata ka san kome-da-kome da ke cikin Littafi Mai Tsarki kafin ka yi baftisma. Bai ce sai Bahabashen ya san kome-da-kome kafin a yi masa baftisma ba. (Ayyukan Manzanni 8:30, 31) Me ya sa? Don koyo game da Allah bai da iyaka. (Mai-Wa’azi 3:11) Amma kafin ka yi baftisma, kana bukata ka koya da kuma amince da muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki.—Ibraniyawa 5:12.

7. Ta yaya nazarin Littafi Mai Tsarki da ka yi ta taimaka maka?

7 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba ya kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da bangaskiya.” (Ibraniyawa 11:6) Saboda haka, kana bukata ka kasance da bangaskiya kafin ka yi baftisma. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa, sa’ad da wasu mutane a birnin Koranti suka ji wa’azin almajiran Yesu, sai “suka ba da gaskiya, aka yi musu baftisma.” (Ayyukan Manzanni 18:8) Hakazalika, nazarin da kuke yi daga Littafi Mai Tsarki ya taimaka maka ka kasance da bangaskiya a kan alkawuran Allah da kuma ikon da hadayar Yesu take da ita wajen kawar da zunubi da kuma mutuwa.—Joshua 23:14; Ayyukan Manzanni 4:12; 2 Timotawus 3:16, 17.

KA KOYA WA WASU GASKIYAR DA KE LITTAFI MAI TSARKI

8. Mene ne zai motsa ka ka gaya wa wasu abin da kake koya?

8 Idan ka ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ka ga yadda yake taimaka maka, bangaskiyarka za ta yi ƙarfi sosai. Kuma za ka so ka gaya wa mutane abin da kake koya. (Irmiya 20:9; 2 Korintiyawa 4:13) Amma su wane ne za ka iya ma wa’azi?

Wani dalibi yana ma wani wa’azi kuma malaminsa yana kallo

Bangaskiya za ta sa ka gaya wa mutane abin da ka gaskata

9, 10. (a) Su waye ne za ka iya soma gaya wa abin da kake koya? (b) Me za ka yi idan kana so ka soma yin wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiya?

9 Wataƙila, za ka so ka gaya wa iyalinka da abokanka da maƙwabtanka da kuma abokan aikinka abin da kake koya. Hakan yana da kyau, amma ka riƙa yin hakan da haƙuri da kuma ƙauna. Yin hakan zai taimaka maka ka soma yin wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiyarku. Idan ka shirya yin hakan, za ka iya gaya wa wanda yake nazari da kai cewa za ka so ka soma zuwa wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiyarku. Idan wanda yake nazari da kai ya ga cewa ka cancanci zuwa wa’azi kuma kana bin abin da kake koya daga Littafi Mai Tsarki, dattawa biyu a ikilisiyarku za su tattauna wasu batutuwa da ku.

10 Mene ne za ku tattauna? Dattawan za su tattauna da kai don su ga ko ka gaskata da muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma kana yin rayuwar da ta jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Ƙari ga haka, za su ga ko kana a shirye ka zama Mashaidin Jehobah. Kada ka manta cewa dattawa suna kula da kowane mutum da ke ikilisiyar har da kai, don haka, kada ka ji tsoron gaya musu ra’ayinka. (Ayyukan Manzanni 20:28; 1 Bitrus 5:2, 3) Bayan tattaunawar, za su gaya maka ko za ka iya soma yin wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiya.

11. Me ya sa yake da muhimmanci ka yi canje-canje kafin ka soma wa’azi tare da ikilisiyar?

11 Dattawa za su iya gaya maka cewa kana bukatar ka ƙara yin wasu canje-canje kafin ka soma zuwa wa’azi da ikilisiyar. Me ya sa waɗannan canje-canjen suke da muhimmanci? Domin muna wakiltar Jehobah sa’ad da muke gaya wa mutane game da shi kuma wajibi ne rayuwarmu ta girmama shi.—1 Korintiyawa 6:9, 10; Galatiyawa 5:19-21.

KA TUBA KUMA KA JUYO

12. Me ya sa kowa yake bukatar tuba?

12 Akwai wani abu kuma da ya kamata ka yi kafin ka yi baftisma. Manzo Bitrus ya ce: ‘Ku tuba fa, ku juyo, domin a shafe zunubanku.’ (Ayyukan Manzanni 3:19) Mene ne yin tuba yake nufi? Yana nufin yin da-na-sani don wani kuskuren da muka yi. Alal misali, idan kana yin lalata, to, za ka bukaci yin tuba. Kuma ko da kana ƙoƙarin yin abin da ya dace a dukan rayuwarka, har ila kana bukatar yin tuba. Me ya sa? Domin dukanmu muna yin zunubi kuma muna bukatar neman gafara daga wurin Allah.—Romawa 3:23; 5:12.

13. Mene ne furucin nan ‘ka juya’ yake nufi?

13 Shin yin da-na-sani ne kawai kake bukata don ka nuna cewa ka tuba? A’a. Manzo Bitrus ya ce kana bukatar ‘ka juyo.’ Wannan yana nufin barin halin da bai dace ba kuma ka soma yin abin da ya dace. Alal misali, a ce kana so ka je wani gari da ba ka taɓa zuwa ba. Da ka soma tafiyar, sai ka gane cewa ka ɓata hanya. Mene ne ya kamata ka yi? Babu shakka, za ka ja birki, ka tsaya kuma ka juya don ka bi hanyar da ta dace. Hakazalika, yayin da kake nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka lura cewa akwai wasu halayenka ko wasu abubuwan da kake bukata ka canja. Zai dace ‘ka juya,’ wato ka daina yin abubuwan da ba su dace ba kuma ka soma yin waɗanda suka dace.

KA YI ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH

Wani dalibi yana yin alkawarin bauta wa Jehobah ta yin addu’a

Shin ka yi alkawarin bauta wa Jehobah?

14. Ta yaya za ka yi alkawarin bauta wa Allah?

14 Wani babban matakin da kake bukata ka ɗauka kafin ka yi baftisma shi ne yin alkawari cewa za ka yi nufin Jehobah. Alkawarin da za ka yi addu’a ce da za ka gaya wa Jehobah cewa shi kaɗai ne za ka bauta wa, kuma nufinsa ne zai fi muhimmanci a rayuwarka.—Kubawar Shari’a 6:15.

15, 16. Me yake motsa mutum ya yi alkawarin bauta wa Allah?

15 Yin alkawarin bauta wa Jehobah shi kaɗai, yana kamar yin alkawarin kasancewa da wani da kake so har mutuwa. Alal misali, a ce saurayi da budurwa suna fita zance. Idan saurayin ya gane cewa budurwar tana da halin kirki, zai so ta sosai kuma ya yi alkawari cewa zai aure ta. Ko da yake tsai da wannan shawarar bai da sauƙi, amma saurayin ya ɗau wannan alkawarin ne don yana son ta sosai.

16 Yayin da ka ci gaba da koyo game da Jehobah, za ka ƙaunace shi kuma ka yi iya ƙoƙarin bauta masa. Hakan zai sa ka yi addu’a kuma ka yi alkawarin bauta masa. Littafi Mai Tsarki ya ce duk wanda yake so ya bi Yesu zai “yi musun kansa.” (Markus 8:34) Mene ne ma’anar wannan furucin? Yana nufin sa yin nufin Jehobah farko a rayuwarka. Yin nufin Jehobah ya fi ra’ayinka da maƙasudanka muhimmanci.—Karanta 1 Bitrus 4:2.

KADA KA JI TSORON CEWA BA ZA KA IYA RIƘE ALKAWARINKA BA

17. Me ya sa wasu mutane suke ƙin ɗaukan alkawarin bauta wa Jehobah?

17 Wasu mutane sun ƙi yin alkawarin bauta wa Jehobah don suna tsoron cewa ba za su iya riƙe alkawarin ba. Ba sa son su ɓata ma Jehobah rai ko kuma suna gani kamar idan ba su yi wannan alkawarin ba, za su iya yin abin da suka ga dama kuma Jehobah ba zai ga laifinsu ba.

18. Me zai taimaka maka ka daina tsoron cewa ba za ka iya riƙe alkawarin da ka yi wa Jehobah ba?

18 Ƙaunarka ga Jehobah za ta taimaka maka ka daina jin tsoron ƙarya alkawarin da ka yi. Da yake kana ƙaunarsa, za ka yi iya ƙoƙarinka ka riƙe wannan alkawarin da ka yi. (Mai-Wa’azi 5:4; Kolosiyawa 1:10) Ba za ka ga cewa yin nufin Jehobah yana da wuya sosai ba. Manzo Yohanna ya ce: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo.”—1 Yohanna 5:3.

19. Me ya sa bai kamata mu ji tsoron yin alkawarin bauta wa Jehobah ba?

19 Ba sai ka zama kamili ba ne za ka iya yin alkawarin bauta wa Jehobah ba. Jehobah ba ya son mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. (Zabura 103:14) Zai taimaka maka ka yi abin da ya dace. (Ishaya 41:10) Idan ka dogara ga Jehobah da dukan zuciyarka, zai “daidaita hanyoyinka.”—Misalai 3:5, 6.

NUNA WA KOWA CEWA KANA SO KA YI NUFIN JEHOBAH

20. Bayan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, wane mataki kuma kake bukatar ka ɗauka?

20 Shin kana gani ka shirya ka yi alkawarin yin nufin Jehobah? Bayan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, kana bukatar ka ɗauki wani mataki kuma. Wane mataki ke nan? Kana bukatar yin baftisma.

21, 22. Ta yaya za ka “shaida” bangaskiyarka?

21 Ka gaya wa mai tsara ayyukan rukunin dattawan ikilisiyarku cewa ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma kana son ka yi baftisma. Zai tura wasu dattawa su yi biyar muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki da kai. Idan sun yarda cewa ka cancanta, za su gaya maka cewa za a iya yi maka baftisma a babban taron Shaidun Jehobah mai zuwa. Za a yi jawabin da zai bayyana abin da yin baftisma ya ƙunsa a taron. Mai jawabin zai tambayi waɗanda suke son su yi baftisma wasu tambayoyi biyu masu sauƙi. Idan ka ba da amsa ga waɗannan tambayoyin, za ka “shaida” bangaskiyarka ga kowa.—Romawa 10:10.

22 Bayan haka, sai a yi maka baftisma. Za a nitsar da kai gaba ɗaya cikin ruwa. Baftismar za ta nuna wa kowa cewa ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma yanzu ka zama Mashaidin Jehobah.

ABIN DA BAFTISMAR DA KA YI TAKE WAKILTA

23. Mene ne yin baftisma ‘cikin sunan Uba da na Ɗa da na ruhu mai-tsarki’ yake nufi?

23 Yesu ya ce za a yi wa almajiransa baftisma ‘cikin sunan Uba da na Ɗa da na ruhu mai-tsarki.’ (Karanta Matta 28:19.) Mene ne ma’anar wannan furucin? Yana nufin cewa ka fahimci ikon Jehobah, ka san matsayin Yesu wajen cika nufin Allah kuma ka san cewa Allah yana amfani da ruhunsa mai-tsarki don ya cim ma nufinsa.—Zabura 83:18; Matta 28:18; Galatiyawa 5:22, 23; 2 Bitrus 1:21.

Wani yana nuna cewa ya tsai da shawarar bauta wa Jehobah ta yin baftisma

Yin baftisma tana nuna cewa kana son ka yi nufin Allah

24, 25. (a) Mece ce baftisma take wakilta? (b) Mene ne za mu tattauna a babi na gaba?

24 Baftisma tana wakiltar abu mai muhimmanci sosai. Nitsar da kai cikin ruwa yana nufin cewa ka bar halayen banza da kake yi a dā. Fito da kai kuma yana nufin cewa za ka soma yin nufin Allah a rayuwarka. Ƙari ga haka, yana nuna cewa daga yanzu, za ka riƙa yin nufin Jehobah har abada. Ya kamata ka nuna cewa ba mutum ko wata ƙungiya ko kuwa aiki ka yi alkawarin bauta wa ba. A maimakon haka, Jehobah ne ka yi alkawarin bauta wa.

25 Alkawarin da ka yi zai taimaka maka ka ƙulla dangantaka da Jehobah. (Zabura 25:14) Yin baftisma ba ya nufin cewa lallai mutum zai sami ceto. Manzo Bulus ya ce: “Ku yi aikin cetonku da tsoro da rawan jiki.” (Filibiyawa 2:12) Yin baftisma mafari ne. Amma ta yaya za ka ci gaba da kasancewa kusa da Jehobah? Babi na ƙarshe na wannan littafin zai amsa wannan tambayar.

TAƘAITAWA

GASKIYA TA 1: SHIN YA DACE IN YI BAFTISMA?

“Ga ruwa; me za ya hana a yi mini baftisma?” —Ayyukan Manzanni 8:36

Me ya sa ya kamata ka yi baftisma kuma yaya za ka yi hakan?

Baftisma tana nuna cewa mutum ya bar rayuwar banza da yake yi a dā kuma yanzu ya soma rayuwar da ta jitu da nufin Allah.

  • Matta 28:19, 20

    Kana bukatar yin baftisma don ka bauta wa Jehobah yadda ya dace.

  • Zabura 40:8

    Baftisma tana nuna wa mutane cewa ka tsai da shawarar bauta wa Allah.

  • Matta 3:16

    Wajibi ne a nitsar da kai cikin ruwa kamar yadda aka yi wa Yesu.

GASKIYA TA 2: JEHOBAH BA YA CE MU YI ABIN DA YA FI ƘARFINMU

“Gama ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.”—1 Yohanna 5:3

Me ya sa bai kamata ka ji tsoron yin alkawarin bauta wa Jehobah ba?

  • Zabura 103:14; Ishaya 41:10

    Ba sai ka zama kamiltacce ba ne kafin ka iya tsai da shawarar bauta wa Jehobah. Jehobah zai taimaka maka ka yi abin da ya dace.

  • Kolosiyawa 1:10

    Ƙaunarka ga Jehobah za ta taimaka maka ka shawo kan jin tsoro cewa ba za ka iya riƙe alkawarinka ba.

GASKIYA TA 3: MATAKAN DA MUTUM ZAI ƊAUKA KAFIN YA YI BAFTISMA

“Murna nake yi in yi nufinka, ya Allahna, Hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.”—Zabura 40:8

Me kake bukata ka yi don ka iya tsai da shawarar bauta wa Jehobah?

  • Yohanna 17:3

    KA YI NAZARIN KALMAR ALLAH

    Ka san Jehobah da kuma Yesu Kristi. Idan ka ci gaba da koyo game da su, za ka ƙaunace su sosai.

  • Ibraniyawa 11:6

    KA KASANCE DA BANGASKIYA

    Ka gaskata da alkawuran Allah da kuma ikon da hadayar Yesu take da ita na sa mu sami ceto daga zunubi da kuma mutuwa.

  • Ayyukan Manzanni 3:19

    KA TUBA

    Yin hakan yana nufin yin da-na-sani don abubuwan da muka yi a dā.

    KA JUYA

    Wannan yana nufin daina wasu abubuwan da muke yi da ba su da kyau.

  • 1 Bitrus 4:2

    KA YI ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH

    Za ka tsai da shawarar bauta wa Jehobah sa’ad da ka yi addu’a, ka gaya masa cewa kana son ka bauta masa kuma ka sa nufinsa farko a rayuwarka.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba