Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • kr babi na 12 pp. 118-131
  • An Tsara Su don Su Yi wa ‘Allah na Salama’ Ibada

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Tsara Su don Su Yi wa ‘Allah na Salama’ Ibada
  • Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Zan Sa Salama ta Zama Mulkinki”
  • Yadda Yesu Yake Ja-gorantar Ikilisiya
  • “Ku Zama Abin Koyi ga Garken”
  • Yadda Dattawa Suke Kula da Garken Allah a Yau
  • Ja-goranci Mai Kyau Ya Inganta Haɗin Kan Mutanen Allah
  • Makiyaya, Ku Yi Koyi da Makiyaya Mafi Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Yadda Aka Tsara Ikilisiya
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Yaya Dattawa Suke Hidima a Ikilisiya?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • “Ku Girmama Waɗanda Suke Aiki Tuƙuru A Cikinku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Mulkin Allah Yana Sarauta!
kr babi na 12 pp. 118-131

BABI NA 12

An Tsara Su don Su Yi wa ‘Allah na Salama’ Ibada

MANUFAR WANNAN BABIN

Jehobah yana ci gaba da sa mutanensa su kasance da tsari

1, 2. Wane canji aka yi wa Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona a watan Janairu 1895, kuma yaya ’yan’uwa suka ji?

SA’AD DA wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki mai kuzari mai suna John A. Bohnet ya karɓi mujallar Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona) ta watan Janairu 1895, abin da ya gani ya burge shi sosai. Mujallar tana da sabon bango da ke ɗauke da zanen hasumiya mai wuta a bakin teku mai hauka kuma wutarta tana haskaka ko’ina. Jigon sanarwar da aka yi a cikin mujallar game da sabon fasalin shi ne, “Sabon Bangonmu.”

2 Da yake abin ya burge shi, Ɗan’uwa Bohnet ya aika wa Ɗan’uwa Russell wasiƙa. Ya ce: “Na yi murnar ganin yadda aka yi wa mujallar HASUMIYAR TSARO sabon bango mai kyau.” Wani Ɗalibin Littafi Mai Tsarki mai aminci, mai suna John H. Brown, ya rubuta game da bangon: “Sabon fasalin nan yana da ban sha’awa. Hasumiyar tana tsaye a kan harsashi mai ƙwari sosai, duk da cewa ruwa da iska suna bubbuga ta.” Wannan sabon bangon shi ne canji na farko da ’yan’uwanmu suka gani a shekarar, amma hakan soma-taɓi ne. A watan Nuwamba na shekarar, sun sake samun labarin wani gagarumin canji. Wani abin ban sha’awa shi ne, canjin ya shafi wata matsala da ke kama da teku mai hauka.

3, 4. Wace matsala ce aka tattauna a Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta 15 ga Nuwamba, 1895, kuma wane babban canji ne aka sanar?

3 Wani talifi mai tsawo da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta 15 ga Nuwamba, 1895, ta bayyana matsalar: Matsaloli da ke kama da teku mai hauka suna yi wa zaman lafiya da ke tsakanin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki barazana. Gardama tana ƙara yin zafi a tsakanin ’yan’uwa game da wanda zai kasance shugaba a ikilisiya. Don a taimaka wa ’yan’uwan su ga abin da ya kamata su yi don su magance wannan matsalar, talifin ya kwatanta ƙungiyar da jirgin ruwa. Talifin ya kuma bayyana cewa waɗanda suke ja-gora sun kasa kafa ƙungiya mai kama da jirgin ruwan da zai iya jimre guguwa da ruwa. Me ya kamata a yi?

4 Talifin ya bayyana cewa ƙwararren matuƙin jirgin ruwa yana tabbatar da cewa akwai abubuwan ceton rai a cikin jirgin kuma abokan aikinsa suna shirye su sa jirgin ya ci gaba da tafiya idan aka fara ruwa da iska. Hakazalika, waɗanda suke ja-gora a ƙungiyar Jehobah suna bukatar su tabbatar da cewa dukan ikilisiyoyi suna shirye su magance duk wata matsala da za ta taso mai kama da ruwa da kuma iska. Don a cim ma hakan, talifin ya sanar da wani babban canji. Ya ba da umurni cewa nan take, “a zaɓi dattawa a kowace ikilisiya” don “‘su riƙa kula’ da garken.”—A. M. 20:28.

5. (a) Me ya sa tsari na farko da aka kafa na naɗa dattawa ya dace? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

5 Wannan shiri na naɗa dattawa mataki ne mai kyau na kafa ikilisiyoyin da za su ɗore. Shirin ya taimaka wa ’yan’uwanmu su jimre matsalolin da Yaƙin Duniya na Ɗaya ya jawo. A shekaru da yawa bayan haka, ci gaban da aka samu a ƙungiyar ya taimaka wa mutanen Allah su bauta wa Jehobah sosai. A wane nassi ne aka annabta wannan ci gaban? Waɗanne canji ne ka shaida a ƙungiyar Jehobah? Ta yaya ka amfana daga waɗannan canjin kuwa?

“Zan Sa Salama ta Zama Mulkinki”

6, 7. (a) Mene ne annabcin da ke Ishaya 60:17 yake nufi? (b) Masu ‘mulki’ da ‘mahukunta’ da aka ambata suna nuni ga mene ne?

6 Kamar yadda muka tattauna a Babi na 9, Ishaya ya annabta cewa Jehobah zai sa mutanensa su sami ƙaruwa. (Isha. 60:22) Amma, Jehobah ya yi alkawarin yin fiye da hakan. A annabcin, ya ce: “Maimakon jangaci zan kawo zinariya, maimakon baƙin ƙarfe kuma zan kawo azurfa, maimakon itace kuma jangaci, maimakon duwatsu kuma baƙin ƙarfe: zan sa salama ta zama mulkinki, adalci kuma ya zama mahukuncinki.” (Isha. 60:17) Mece ce ma’anar annabcin nan? Ta yaya ya shafe mu a yau?

Sauyin bai canja abubuwa marasa kyau da masu kyau ba, amma ya canja masu kyau ne da mafi kyau

7 Annabcin Ishaya ya ce za a yi wasu sauya za a sauya wasu abubuwa. Amma idan ka duba, za ka ga cewa sauyin bai canja abubuwa marasa kyau da masu kyau ba, amma ya canja masu kyau ne da mafi kyau. Sauya jangaci da zinariya ci gaba ne sosai, haka ma da sauran abubuwan da aka ambata a ayar. Da wannan bayanin, Jehobah ya annabta cewa zai inganta yanayin mutanensa da sannu-sannu. Amma wane irin ci gaba ne wannan annabcin yake nufi? Ta wajen ambata masu ‘mulki’ da ‘mahukunta,’ Jehobah ya nuna cewa za a samu ci gaba a hankali a yadda ake kula da kuma tsara mutanensa.

8. (a) Wane ne ya sa aka sami ci gaban da aka ambata a annabcin Ishaya? (b) Ta yaya muka amfana daga canjin da aka yi? (Ka kuma duba akwatin nan “Ya Amince da Gyara Cikin Tawali’u.”)

8 Wane ne ya kawo ci gaba ga ƙungiyar? Jehobah ya ce: ‘Zan kawo zinariya, . . . Zan kawo azurfa, . . . zan sa salama.’ Hakika, Jehobah ne da kansa ya sa aka sami ci gaba a yadda aka tsara ikilisiya, ba ƙoƙarin mutum ba. Kuma tun da aka naɗa Yesu Sarki, Jehobah ya yi amfani da Ɗansa don a sami waɗannan ci gaban. Ta yaya muka amfana daga waɗannan canjin? Wannan nassin ya ce ci gaban zai kawo “salama” da “adalci.” Yayin da muka bi ja-gorar Allah kuma muka yi gyara, salama za ta kasance a tsakaninmu. Ƙari ga haka, za mu daɗa son yin adalci, kuma hakan zai motsa mu mu bauta wa Jehobah, wanda manzo Bulus ya kira ‘Allah na salama.’—Filib. 4:9.

9. Mene ne tushen tsari da haɗin kai da ake da shi a cikin ikilisiya, kuma me ya sa?

9 Bulus ya rubuta game da Jehobah cewa: ‘Allah ba Allah na yamutsai ba ne, amma na kwanciyar rai ne.’ (1 Kor. 14:33) Ka lura cewa Bulus bai ce akasin yamutsi shi ne tsari ba, amma ya ce akasin yamutsi shi ne salama. Me ya sa? Yi la’akari da wannan: Kasancewa da tsari kawai ba ya nufin cewa za a sami salama. Alal misali, rukunin sojoji suna iya yin maci da tsari idan za su bakin dāga, amma maci da tsari da suke yi don zuwa yaƙi ne, ba don kawo salama ba. Shi ya sa a matsayinmu na Kiristoci, ya kamata mu riƙe wannan a zuciya: Duk wani tsarin da tushensa ba salama ba ne zai rushe ko bajima ko ba daɗe. Akasin haka, salama daga Allah tana kawo tsarin da zai kasance har abada. Saboda haka, muna matuƙar godiya cewa “Allah na salama” ne yake wa ƙungiyar nan ja-gora kuma shi yake kawo ci gaba! (Rom. 15:33) Salama daga wurin Allah ita ce tushen tsari mai kyau da kuma haɗin kai da muke da muke da shi a ikilisiyoyinmu a faɗin duniya.—Zab. 29:11.

10. (a) Waɗanne ci gaba ne aka samu a ƙungiyarmu a shekarun baya? (Ka duba akwatin nan “Yadda Aka Kyautata Tsarin Ja-Goranci.”) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

10 Akwatin nan “Yadda Aka Kyautata Tsarin Ja-goranci” ya nuna tsari da kuma canji masu kyau da aka samu a ƙungiyar nan a shekarun baya. Amma waɗanne canji makamantan ‘jangaci zuwa zinariya’ ne Jehobah ya yi ta wurin Sarkinmu a kwanan nan? Ta yaya gyarar da aka yi a yadda ake ja-gora ta ƙarfafa salama da haɗin kan ikilisiyoyi a faɗin duniya? Ta yaya suke taimaka maka ka bauta wa “Allah na salama”?

Yadda Yesu Yake Ja-gorantar Ikilisiya

11. (a) Wace gyara ce aka yi bayan nazarin Nassosi? (b) Sauran shafaffun sun ƙuduri yin me?

11 Daga shekara ta 1964 zuwa 1971, hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah ta kafa tsarin binciken Littafi Mai Tsarki da ya shafi batutuwa da yawa, har da tsarin ikilisiyar Kirista ta ƙarni na farko.a Nazarin ya nuna cewa a ƙarni na farko, rukunin dattawa ne ke kula da ikilisiyoyi maimakon dattijo guda. (Karanta Filibiyawa 1:1; 1 Timotawus 4:14.) Sa’ad da suka fahimci hakan, hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah ta fahimci cewa Sarki Yesu ne yake yin gyara a tsarin ƙungiyar mutanen Allah don ta sami ci gaba. Sauran shafaffu kuma sun ƙuduri niyyar bin ja-gorancin Sarkin kuma sun yi gyara nan da nan domin su bi ja-gorar da ke cikin Nassosi game da naɗin dattawa. Waɗanne canji ne aka yi a daga shekara ta 1970 zuwa 1973?

YA AMINCE DA GYARA CIKIN TAWALI’U

Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 1916, ta yaren Finnish, tana ɗauke da wata wasiƙa daga Ɗan’uwa Russell zuwa ga wasu ’yan’uwa kaɗan a Skandinabiya, har da Ɗan’uwa Kaarlo Harteva. Ɗan’uwa Russell ya rubuta musu cewa: “Muna ƙarfafa dukanku, ’yan’uwanmu cikin bangaskiya cewa ku dawo cikin gaskiya kuma ku mai da hankali ga aikin da ke gabanku.” Me ya sa Ɗan’uwa Russell ya yi wannan roƙon?

Kaarlo Harteva

Kaarlo Harteva

Ɗan’uwa Harteva, wanda aka haifa a shekara ta 1882, yana ɗaya daga cikin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki na farko a ƙasar Finland. An yi masa baftisma a watan Afrilu 1910, kuma Ɗan’uwa Russell ya umurce shi a watan Agusta ta 1912, ya wallafa Hasumiyar Tsaro a yaren Finnish. Kome yana tafiya daidai har sa’ad da Yaƙin Duniya na Farko ya ɓarke. Ɗan’uwa Harteva ya rubuta a fitowar Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba 1914 cewa: “Saboda taɓarɓarewar tattalin arziki . . . ba mu da tabbacin cewa za mu iya ci gaba da wallafa Hasumiyar Tsaro mai yawan shafuffukan da muke wallafawa ko kuma wallafa ta a kai a kai kamar yadda muke yi a wannan shekarar ba.” Amma, a shekara ta 1915, don a tara kuɗi, sai Ɗan’uwa Harteva da wasu suka kafa wata ƙungiyar gayya mai suna Ararat, wadda ta soma wallafa mujalla mai wannan sunan.

Yayin da Ɗan’uwa Harteva ya mai da hankalinsa ga sabuwar ƙungiyar da kuma sabuwar mujallar, wani ɗan’uwan ya zama editan Hasumiyar Tsaro ta yaren Finnish. Mujallar Ararat ta wallafa talifofi game da Littafi Mai Tsarki da magungunan gargajiya da kuma sabon yaren Esperanto. Kafin ka sani, wannan sabuwar mujallar ta ɗauke hankulan ’yan’uwa daga ainihin koyarwa ta gaskiya. A wannan lokacin ne Ɗan’uwa Russell ya roƙi Ɗan’uwa Harteva da sauran ’yan’uwa su “dawo cikin gaskiya, don yana so su daidaita dangantakarsu da Allah.”

Mene ne Ɗan’uwa Harteva ya yi? Ya wallafa wasiƙar Ɗan’uwa Russell a cikin mujallar Ararat, tare da amsarsa. Ɗan’uwa Harteva ya ba da haƙuri saboda abubuwan da ya yi, kuma ya ce: “Zan so in yi iya ƙoƙarina don in daidaita wannan batu.” Jim kaɗan bayan haka, a fitowar ƙarshe ta mujallar Ararat, Ɗan’uwa Harteva ya sake ba da haƙuri don yadda ya dagula hankulan ’yan’uwa kuma ya daɗa cewa: “Zan ƙoƙarta in mai da hankali sosai ga kowane sashe na gaskiyar da muke da ita yanzu.” Akasin wasu dattawan da aka zaɓa a lokacin masu girman kai, Kaarlo Harteva ya karɓi gyaran da aka yi masa cikin tawali’u.

Daga baya, an sake naɗa Ɗan’uwa Harteva a matsayin editan Hasumiyar Tsaro ta yaren Finnish kuma ya zama mai kula da ofishin reshe. Ya ci gaba da kula da waɗannan hakkokin har zuwa shekara ta 1950. Ya gama hidimarsa a duniya da aminci ga Jehobah da kuma koyarwarsa a shekara ta 1957. Hakika, waɗanda suka amince da gyarar da Sarkinsu Yesu ya yi, sun ingantu kuma Jehobah ya albarkace su.

12. (a) Wane canji ne aka yi wa hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah? (b) Ka kwatanta yadda aka tsara Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah a yau. (Ka duba akwatin nan “Yadda Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah Take Kula da Al’amuran Mulki,” a shafi na 130.)

12 Canji na farko da aka yi ya shafi hukumar da ke kula da ayyukan Shaidun Jehobah ne da kanta. Kafin wannan lokacin, wannan rukuni na ’yan’uwa shafaffu ya ƙunshi mutane bakwai ne da suka haɗu suka zama darektocin Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. Amma a shekara ta 1971, adadin hukumar ta ƙaru daga 7 zuwa 11 kuma ta ba da aikin darektocin ga wasu. Mambobin hukumar ba su ɗauki wani da muhimmanci fiye da wani a tsakaninsu ba, kuma suka fara yin karɓa-karɓa da matsayin mai kujera bisa ga harufan sunayensu a kowace shekara.

13. (a) Wane tsari ne aka yi shekaru 40 ana bi? (b) Mene ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta yi a 1972?

13 Canji na biyu ya shafi kowace ikilisiya. Ta yaya? Daga shekara ta 1932 zuwa 1972, mutum ɗaya ne kawai yake kula da ikilisiya. Har shekara ta 1936, ana kiran wannan ɗan’uwan da aka naɗa darektan hidima. Daga baya, an canja sunan zuwa bawan ikilisiya, kuma a ƙarshe aka soma kiransa mai kula da ikilisiya. Waɗannan ’yan’uwan da aka naɗa sun taimaka wa garken su ƙarfafa dangantakarsu da Allah. Mai kula da ikilisiya yakan yanke shawara a madadin ikilisiya ba tare da tuntuɓar sauran masu hidima a cikin ikilisiya ba. Amma, a shekara ta 1972, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta kawo wani babban canji. Wane canji ke nan?

14. (a) Wane sabon tsari ne aka fara bi a ranar 1 ga Oktoba, 1972? (b) Ta yaya ne mai tsara ayyukan rukunin dattawa yake amfani da shawarar da ke Filibiyawa 2:3?

14 Maimakon ɗan’uwa guda ya riƙa kula da ikilisiya, za a naɗa ’yan’uwa da suka cancanta bisa ga umurnin Littafi Mai Tsarki a matsayin dattawa. Za su zama rukunin dattawa da zai riƙa kula da ikilisiyarsu. An soma bin wannan sabon tsarin naɗa dattawa a ranar 1 ga Oktoba, 1972. A yau, mai tsara ayyukan rukunin dattawa ba ya ɗaukan kansa da muhimmanci fiye da sauran dattawan, amma yana ɗaukan kansa kamar ‘ƙanƙanin cikinsu duka.’ (Luk 9:48) Waɗannan ’yan’uwa masu sauƙin kai albarka ne ga dukan ’yan’uwa a faɗin duniya!—Filib. 2:3.

Babu shakka, da yake Sarkinmu yana da hikima, ya yi wa mabiyansa tanadin makiyaya masu taimako a kan kari

15. (a) Wane amfani ne aka samu daga tsarin rukunin dattawa da aka kafa? (b) Mene ne ya nuna cewa Sarkinmu yana da hikima?

15 Tsarin da aka kafa na raba ayyukan ikilisiya a tsakanin mambobin rukunin dattawa ci gaba ne sosai. Ka yi la’akari da hanyoyi uku da aka amfana daga wannan tsarin: Hanya ta farko ita ce, tsarin ya taimaka wa dukan dattawa su tuna cewa Yesu ne Shugaban ikilisiya kome yawan ayyukan da suke da shi a ikilisiya. (Afis. 5:23) Ta biyu, kamar yadda Misalai 11:14 ta ce: “Cikin taron masu-shawara akwai lafiya.” Yayin da dattawa suka zauna tare suka tattauna batutuwan da suka shafi ikilisiya kuma suka saurari shawarwarin juna, hakan yana taimaka musu su yanke shawarwarin da suka jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Mis. 27:17) Jehobah yana sa waɗannan shawarwarin su kasance da albarka. Ta uku, da yake ana samun ƙarin ’yan’uwa da suka cancanta, ƙungiyar tana ci gaba da tanadar da dattawa don kula da ’yan’uwa a cikin ikilisiya da yake ana samun ƙaruwa a kai a kai. (Isha. 60:3-5) Ka yi la’akari da wannan, an sami ƙarin ikilisiyoyi a faɗin duniya daga sama da 27,000 a shekara ta 1971 zuwa sama da 113,000 a shekara ta 2013! Babu shakka, da yake Sarkinmu yana da hikima, ya yi wa mabiyansa tanadin makiyaya masu taimako a kan kari.—Mi. 5:5.

YADDA AKA KYAUTATA TSARIN JA-GORANCI

  • 1881​—Ɗan’uwa Russell ya gaya wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da ke zaune a yanki ɗaya kuma suna yin taro a kai a kai cewa su sanar da ofishin Watch Tower wurin da suke yin taron domin a iya tuntuɓar su.

  • 1895​—An umurci dukan ikilisiyoyi su zaɓi ’yan’uwa maza da za su zama dattawa a tsakaninsu.

  • 1919​—Ofishin reshe ya naɗa darektan hidima a kowace ikilisiya a ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki. Ayyukansa sun ƙunshi tsara yadda za a yi wa’azi da kuma ƙarfafa ’yan’uwa su riƙa fita wa’azi. Wasu daga cikin dattawan ba su goyi bayan tsarin kafa darektan hidima ba.

  • 1932​—An daina yin zaɓen dattawa da ake yi a ikilisiyoyi a kowace shekara. A maimakon haka, ikilisiya tana zaɓan kwamitin hidima da ta ƙunshi ’yan’uwan da suke da ƙwazon fita wa’azi kuma halayensu sun jitu da sabon sunan nan Shaidun Jehobah. Ofishin reshe yana naɗa ɗaya daga cikin waɗanda ikilisiya ta zaɓa don ya zama direktan hidima.

  • 1937​—’Yan’uwan da ke cikin rukunin taro mai girma za su iya kasancewa cikin kwamitocin hidima tare da ’yan’uwa shafaffu.

  • 1938​—Ikilisiyoyi sun amince cewa a riƙa naɗa dukan dattawa a ikilisiya a ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki. Hakan ya kawo ƙarshen zaɓen dimokuraɗiyya a dukan ikilisiyoyi.

Don samun ƙarin bayani game da ci gaban da aka samu a tsarin ƙungiyarmu, ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafuffuka na 204-235.

Yadda ake zaban dattawa a ikilisiya a shekara ta 1920

“Yar’uwa Rose Swingle, daga Chicago da ke Illinois, a Amirka, ta ce: “Muna zaɓan dattawa ta wajen ɗaga hannunmu na dama, sa’an nan wani ɗan’uwa ya bi layi-layi yana ƙirga hannayen.

“Ku Zama Abin Koyi ga Garken”

16. (a) Wane hakki ne dattawa suke da shi? (b) Yaya Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ɗauki umurnin da Yesu ya bayar na ‘zama makiyayin tumakinsa’?

16 Tun zamanin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, dattawa sun riga sun fahimci cewa suna da hakkin taimaka wa ’yan’uwa su ci gaba da bauta wa Allah. (Karanta Galatiyawa 6:10.) A shekara ta 1908, wani talifin Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ya tattauna umurnin Yesu da ya ce: “Ka zama makiyayin tumakina.” (Yoh. 21:15-17) An gaya wa dattawa a cikin talifin cewa: “Ya kamata mu ɗauki umurnin da Ubangiji ya bayar game da garkensa da muhimmanci sosai, kuma mu ɗauki aikin ciyar da kuma kula da mabiyan Ubangiji a matsayin gata mai girma.” A shekara ta 1925, Hasumiyar Tsaro ta sake nanata muhimmancin hidimar makiyaya sa’ad da ta tunasar da dattawa cewa: “Allah ne yake da cocinsa, . . . kuma kowa zai ba da lissafin yadda yake amfani da gatan da aka ba shi na yi wa ’yan’uwa hidima.”

17. Ta yaya ne aka taimaka wa masu kula su zama ƙwararrun makiyaya?

17 Ta yaya ne ƙungiyar Jehobah ta taimaka wa dattawa su yi canji da ke kama da ‘baƙin ƙarfe zuwa azurfa’ a yadda suke gudanar da ziyarar ƙarfafawa? Ta hanyar horarwa. A shekara ta 1959, an gudanar da Makarantar Hidima ta Mulki ta farko domin dattawa. Wani sashe na makarantar ya tattauna batun nan, “Mai da Hankali ga Bukatun ’Yan’uwa.” An ƙarfafa dattawan su “kasance da tsari na ziyartar masu shela a gidajensu.” Wannan sashen ya nuna hanyoyi dabam-dabam da makiyayan za su iya sa ziyarar ta ƙarfafa ’yan’uwa. A shekara ta 1966, an soma wata sabuwar Makarantar Hidima ta Mulki. An tattauna batun nan, “Muhimmancin Ziyarar Ƙarfafawa,” a makarantar. Mene ne ainihin abin da aka tattauna a wannan sashen? An tattauna cewa waɗanda suke yin ja-gora “su kula da garken Allah sosai ba tare da yin watsi da tasu iyalin da kuma wa’azi ba.” A ’yan shekarun da suka wuce, an gudanar da makarantun dattawa da dama. Mene ne sakamakon wannan horarwa da ƙungiyar Jehobah take ci gaba da tanadarwa? A yau, ikilisiyar Kirista tana da dubban ƙwararrun ’yan’uwa maza da suke hidima a matsayin dattawa.

Makarantar Hidima ta Mulki a kasar Filifin a 1966

Makarantar Hidima ta Mulki a kasar Filifin a 1966

18. (a) Wane hakki mai nauyi ne aka danƙa wa dattawa? (b) Me ya sa Jehobah da Yesu suke ƙaunar dattawa?

18 Jehobah ne ya yi amfani da Sarkinmu Yesu wajen naɗa dattawa Kiristoci don su ɗauki hakki mai nauyi. Mene ne wannan hakkin? Hakkin shi ne yi wa tumakin Allah ja-gora a wannan lokaci mafi wuya a tarihin ’yan Adam. (Afis. 4:11, 12; 2 Tim. 3:1) Jehobah da Yesu suna ƙaunar dattawa sosai don yadda suke aiki tuƙuru da kuma yin biyayya ga wannan umurnin Littafi Mai Tsarki: “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku, . . . da yardan rai . . . , da karsashin zuciya . . .  kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.” (1 Bit. 5:2, 3) Za mu tattauna hanyoyi biyu daga cikin hanyoyi da dama da Kiristoci makiyaya suka zama abin koyi ga garke da kuma yadda suka ƙara sa salama da farin ciki ta kasance a cikin ikilisiya.

“MUN YI MAMAKI”

AN TURA wasu ma’aurata masu wa’azi a ƙasashen waje zuwa wata ikilisiya da aka daɗe ba a samu ƙaruwa ba a Asiya. Waɗannan ma’auratan sun lura cewa ’yan’uwan da ke ikilisiyar suna da kirki amma ba sa bin umurni daga ƙungiyar Jehobah. Bayan ma’auratan sun ƙulla abota da ’yan’uwan, ɗan’uwan da ke wa’azi a ƙasar waje ya fara taimaka wa ikilisiyar a hankali a hankali ta bi tsarin da mutanen Jehobah suke bi a faɗin duniya. Mene ne sakamakon? A cikin shekara biyu, adadin masu halartan taro ya ƙaru, sababbi suka fara fita wa’azi, kuma mutane fiye da 20 sun yi baftisma. Ma’auratan sun ce: “Mun yi mamaki. Jehobah ya albarkace mu sosai! Ganin sakamakon bin umurnin ƙungiyar Allah ya faranta ran dukan waɗanda suke cikin ikilisiyar.”

Yadda Dattawa Suke Kula da Garken Allah a Yau

19. Yaya muke ɗaukan dattawan da muke zuwa wa’azi tare?

19 Na ɗaya, dattawa suna fita wa’azi tare da waɗanda suke cikin ikilisiya. Ga abin da Luka marubucin Linjila ya ce game da Yesu: ‘Ya zagaye birni da ƙauye yana wa’azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi.’ (Luk 8:1, Littafi Mai Tsarki) Kamar yadda Yesu ya fita wa’azi tare da manzanninsa, hakazalika a yau dattawa masu kafa misali mai kyau suna aiki tare da ’yan’uwansu masu bi in sun fita wa’azi. Sun fahimci cewa ta wajen yin hakan, suna inganta hali mai kyau da ikilisiyar take da shi. Yaya waɗanda suke cikin ikilisiya suke ɗaukan irin waɗannan dattawan? Jeannine, wata ’yar’uwa ’yar wajen shekara 90 ta ce: “Fita wa’azi tare da dattijo yana ba ni damar tattaunawa da shi da kuma ƙara saninsa.” Wani ɗan’uwa ɗan wajen shekara 35 mai suna Steven, ya ce: “Idan na fita wa’azi tare da dattijo, na san cewa zai taimaka mini sosai, kuma irin wannan taimakon yana faranta mini rai.”

Wani makiyayi ya sami tunkiyarsa da ta bace

Kamar yadda makiyayi yake neman tunkiyar da ta ɓace, su ma dattawa suna yin iya ƙoƙarinsu su nemi waɗanda suka bar ikilisiya

20, 21. Ta yaya dattawa za su iya yin koyi da makiyayin da ke cikin almarar da Yesu ya bayar? Ka ba da misali. (Ka duba kuma akwatin nan “Ziyarar Mako-mako Mai Amfani Sosai.”)

20 Na biyu, ƙungiyar Jehobah ta koyar da dattawa su riƙa nuna cewa sun damu da waɗanda suka bar ikilisiya. (Ibran. 12:12) Me ya sa ya kamata dattawa su taimaka wa waɗanda dangantakarsu da Jehobah ta yi sanyi, kuma ta yaya za su yi hakan? Amsar tana cikin almarar da Yesu ya bayar na makiyayi da tunkiyar da ta ɓace. (Karanta Luka 15:4-7.) Sa’ad da makiyayin da aka ambata a cikin almarar ya lura cewa tunkiyarsa ta ɓace, ya nemi tunkiyar kamar ita ce kaɗai tunkiyarsa. Ta yaya dattawa a yau suke yin koyi da wannan makiyayin? Kamar yadda tunkiyar da ta ɓace take da tamani a idanun makiyayin, haka su ma waɗanda suka bar ikilisiya suke da tamani a gaban dattawa. Suna ɗaukan mutumin da dangantakarsa da Jehobah ta yi sanyi kamar tunkiyar da ta ɓace, ba kamar mutumin da ya yi nisan da ba zai ji kira ba. Bugu da ƙari, kamar yadda makiyayin ya “je neman abin da ya ɓace har ya samu,” dattawa ma suna neman waɗanda dangantakarsu da Jehobah ta yi sanyi kuma suna taimaka musu.

21 Mene ne makiyayin da ke cikin almarar ya yi sa’ad da ya ga tunkiyar da ta ɓace? Ya ɗauke ta a hankali, ya saɓe ta a “kafaɗunsa,” kuma ya mayar da ita cikin garken. Hakazalika, idan dattijo ya nuna cewa ya damu da mutumin da dangantakarsa da Jehobah ta yi sanyi, hakan zai iya ƙarfafa shi kuma ya mai da shi cikin ikilisiya. Abin da ya faru da Victor ke nan, wani ɗan’uwa a Afirka wanda ya daina tarayya da ikilisiya. Ya ce: “A shekaru takwas da na yi ba na zuwa taro da kuma wa’azi, dattawa sun ci gaba da nema na don su taimaka mini.” Mene ne ya fi ratsa zuciyarsa? Ya ce: “Wata rana, wani dattijo mai suna John, wanda muka halarci Makarantar Hidima ta Majagaba tare ya ziyarce ni kuma ya nuna mini wasu hotunan da muka ɗauka a makarantar. Hotunan sun tuna mini abubuwa da dama masu ban sha’awa har na soma ɗokin sake farin ciki kamar yadda nake yi a dā, sa’ad da nake bauta wa Jehobah.” Ba da daɗewa ba bayan ziyarar John, Victor ya koma yin tarayya da ikilisiya. A yau, yana hidimar majagaba kamar dā. Hakika, dattawa Kiristoci da ke nuna sun damu da ’yan’uwansu suna sa mu farin ciki sosai.—2 Kor. 1:24.b

Wasu ’yan’uwa biyu sun ziyarci wani dan’uwa da ya yi sanyi a ibada

ZIYARAR MAKO-MAKO MAI AMFANI SOSAI

DOMIN suna so su taimaka wa tumakin da suka ɓace, dattawan wata ikilisiya a Amirka sun tattauna abin da ya kamata su yi don su cim ma wannan maƙasudin. Sun lura cewa mutane wajen 30 da suka daina bauta wa Jehobah shekaru da daɗewa suna zaune a yankin ikilisiyarsu har ila. Yawancinsu kuma sun tsufa.

Ɗaya daga cikin dattawan mai suna Alfredo ya nemi sunayen mutanen kuma ya soma ziyartar su. Ya ce: “Kowace ranar Jumma’a da safe, ina zuwa in ƙwanƙwasa ƙofar wani wanda ya daina zuwa wa’azi da taro.” Sa’ad da mutumin ya buɗe ƙofarsa, sai Alfredo ya soma tattaunawa da mutumin cikin natsuwa kuma ya gaya masa yadda yake ƙaunarsa. Yakan gaya wa ’yar’uwa ko ɗan’uwan da ya daina halartan taro da kuma fita wa’azi cewa ikilisiya ba ta manta da ayyuka masu kyau da ya yi domin Mulkin Jehobah ba. Alfredo ya ci gaba da cewa: “Sa’ad da na gaya wa wani ɗan’uwa tsoho da ya daina halartan taro da fita wa’azi yawan awoyi da kuma adadin mujallun da ya bayar a rahotonsa na ƙarshe a shekara ta 1976, sai idanun ɗan’uwan suka cika da hawaye.” Alfredo yana kuma karanta ma waɗanda ya ziyarta Luka 15:4-7, 10, kuma yakan yi musu wannan tambayar: “Mene ne ke faruwa sa’ad da tunkiyar da ta ɓace ta dawo ikilisiya? Jehobah da Yesu da kuma mala’iku suna yin farin ciki. Ka yi tunanin hakan!”

A cikin shekaru biyu yanzu, Alfredo yana zuwa wurin waɗanda suka daina zuwa taro da wa’azi don ya taimaka musu. Mene ne sakamakon ƙoƙari da kuma haƙurin da ya yi? Yana farin ciki domin ya taimaka wa ’yan’uwa biyu su koma tarayya da ikilisiya. A yanzu suna zuwa taro a kai a kai a ranar Lahadi. Yana murmushi kuma ya ce: “Na yi hawaye sa’ad da suka shiga Majami’ar Mulki. Ko da yake ’yan’uwan nan sun soma halartan taro, ina ziyartar su kowace ranar Jumma’a domin sun gaya mini cewa suna jin daɗin wannan ziyarar mako-mako sosai. Ni ma ina jin daɗin haka!”

Ja-goranci Mai Kyau Ya Inganta Haɗin Kan Mutanen Allah

22. Ta yaya adalci da salama suke kawo haɗin kai a cikin ƙungiyar Jehobah? (Ka kuma duba akwatin nan “Mun Yi Mamaki.”)

22 Kamar yadda aka faɗa a baya, Jehobah ya annabta cewa adalci da salama za su ci gaba da ƙaruwa a tsakanin mutanen Allah. (Isha. 60:17) Waɗannan halayen sun sa ’yan’uwa a ikilisiyoyi sun kasance da haɗin kai sosai. Ta yaya? A batun adalci, ‘Ubangiji Allahnmu Ubangiji ɗaya ne.’ (K. Sha 6:4) Babu bambanci a mizaninsa na adalci a ikilisiyoyin wannan ƙasar da kuma ikilisiyoyin da ke wata ƙasa. Mizanansa na abin da ya dace da wanda bai dace ba ɗaya ne, kuma haka suke a “cikin dukan ikilisiyai na tsarkaka.” (1 Kor. 14:33) Saboda haka, ikilisiya za ta samu ci gaba ne kawai idan aka bi mizanan Allah. A batun salama, Sarkinmu yana so mu more salama a cikin ikilisiya kuma mu zama “masu-sada zumunta.” (Mat. 5:9) Shi ya sa muke himma wajen “yin abubuwan da ke kawo salama.” Muna ɗaukan mataki don mu magance matsalolin da za su iya tasowa a tsakaninmu. (Rom. 14:19, LMT) Ta haka, muna sa ikilisiyarmu ta kasance da salama da kuma haɗin kai.—Isha. 60:18.

23. A matsayinmu na Shaidun Jehobah, mene ne muke morewa a yau?

23 A watan Nuwamba ta 1895, sa’ad da Hasumiyar Tsaro ta sanar da tsari na farko da aka kafa na naɗa dattawa, ’yan’uwan da ke ja-gora sun furta muradinsu. Mene ne muraɗin? Sun yi fata da addu’a cewa wannan sabon shirin da ƙungiyar ta yi zai taimaka wa mutanen Allah su ‘haɗa kai nan da nan a bangaskiya.’ Muna godiya sosai saboda yadda Jehobah ya yi amfani da Sarkinmu wajen kyautata yadda ake ja-goranci a shekarun nan da dama, kuma hakan ya sa mun kasance da haɗin kai sosai a ibadarmu. (Zab. 99:4) A sakamakon haka, dukan mutanen Jehobah a yau suna murna domin suna bin “ruhu ɗaya,” da “sawu ɗaya,” kuma suna bauta wa ‘Allah na salama’ “da zuciya ɗaya.”—2 Kor. 12:18; karanta Zafaniya 3:9.

a An wallafa sakamakon wannan bincike mai zurfi a cikin wani littafin bincike mai suna Aid to Bible Understanding.

b Ka duba talifin nan “Dattawa Kirista Suna Aiki Don Mu Yi ‘Farin Ciki,’” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2013, shafuffuka na 27-31.

Ka Gaskata da Mulkin Kuwa?

  • Waɗanne ci gaba ne Mulkin ya kawo a ƙungiyar Jehobah?

  • Ta yaya gyaran da aka yi a yadda ake yin ja-goranci a cikin ikilisiya ya taimaka maka ka yi wa ‘Allah na salama’ ibada?

  • Waɗanne kalamai da kuma halaye na dattijo ne suka daɗa sa ka farin ciki?

  • Me za ka iya yi don a ci gaba da kasancewa da salama da haɗin kai a cikin ikilisiya?

Yadda Hukuma da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suke taro

YADDA HUKUMAR DA KE KULA DA AYYUKAN SHAIDUN JEHOBAH TAKE KULA DA AL’AMURAN MULKI

HUKUMAR da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta ƙunshi bayin Jehobah shafaffu. A matsayin rukuni, su ne “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Su ne suke da hakkin tanadar da abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah da kuma ba da umurni da ƙarfafawa a kan wa’azin Mulki a faɗin duniya.—Mat. 24:14, 45-47.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana yin taro kowane mako, a yawancin lokaci a ranar Laraba. Hakan yana sa ’yan’uwan nan su yi aiki cikin haɗin kai. (Zab. 133:1) An rarraba mambobin wannan hukumar zuwa kwamitoci dabam-dabam. Kowane kwamiti yana kula da sashe guda don a faɗaɗa al’amuran Mulki. Ga ayyukansu a taƙaice.

  • ’Yan’uwa maza suna hada hannu don su kula da garken Allah

    Kwamitin Masu Tsara Ayyuka

    ’Yan’uwan da ke cikin wannan kwamitin suna kula da batutuwan da suka shafi shari’a da kuma yin amfani da kafofin yaɗa labarai don sanar da ainihin imaninmu idan hakan ya wajaba. Suna taimakawa a lokacin bala’i da tsanantawa da kuma sa’ad da bukata ta gaggawa ta taso wa ’yan’uwanmu a faɗin duniya.

  • ’Yan Bethel suna yin aiki iri-iri

    Kwamiti Mai Kula da Ma’aikata

    Wannan kwamitin ne yake da hakkin kula da bukatun iyalin Bethel a faɗin duniya da kuma yi musu tanadin abubuwan da za su ƙarfafa dagantakarsu da Jehobah. Yana kula da zaɓa da kuma gayyatar sababbin ’yan’uwa zuwa Bethel kuma shi ne yake amsa tambayoyin da ake yi game da hidimarsu a Bethel.

  • Wani mai hidima a Bethel yana taimaka wa wajen buga da aika littattafanmu

    Kwamitin Buga Littattafai

    Waɗanda suke wannan kwamitin suna kula da buga littattafai da kuma aika su a faɗin duniya. Su ne ke kula da wuraren buga littattafai, ofisoshin reshe da Majami’un Taro da gine-gine makamantansu waɗanda ƙungiyar Jehobah take amfani da su a faɗin duniya, tare da aikin gine-gine da ya haɗa da gina Majami’un Mulki. Su ne suke tsara yadda za a yi amfani da gudummawar da aka bayar don aikin Mulki da kyau.

  • Wani dan’uwa yana shirya da yin bincike

    Kwamitin Hidima

    ’Yan’uwan da ke wannan kwamitin suna kula da dukan fannonin wa’azi da batutuwan da suka shafi ikilisiyoyi, masu shela, majagaba, dattawa, masu kula masu ziyara, da masu yin wa’azi a ƙasashen waje. Ƙari ga haka, suna kula da ayyukan Kwamitocin Yin Hulɗa da Asibitoci da kuma wallafa Hidimarmu ta Mulki.

  • Wani dan’uwa yana jawabi a bagadi

    Kwamitin Koyarwa

    Wannan kwamitin ne ke kula da jawaban da ake bayarwa a manyan taro da kuma taron ikilisiya. Shi ne ke kula da Makarantar Gilead da Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki da Makarantar Hidima ta Majagaba da Makarantar Hidima ta Allah, da makamantansu. Ƙari ga haka, wannan kwamitin yana kula da shirye-shiryen koyarwa da ake tanadarwa ta sauti da bidiyo.

  • Fasalolin littattafanmu dabam-dabam har da dandalin jw.org

    Kwamitin Rubuce-rubuce

    ’Yan’uwan da ke wannan kwamitin ne suke kula da kuma shirya abubuwan da ke ƙarfafa dangantaka da Allah. Kwamitin yana yin hakan ta littattafai ko ta kwamfuta don ’yan’uwa masu bi da kuma jama’a baki ɗaya. Yana kuma kula da dandalin Yanar Gizon ƙungiyarmu kuma shi ne yake kula da aikin fassara da ake yi a faɗin duniya. Ƙari ga hakan, wannan kwamitin yana amsa tambayoyin da aka yi game da ma’anar wasu nassosi da kuma abubuwan da aka faɗa a littattafanmu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba