Abin da Ke Ciki
Shaidun Jehobah
SU WANE NE NE MU?
Darasi na 1-4
Akwai Shaidun Jehobah a ƙasashe 239, kuma su mutane ne da suka fito daga ƙabilu da al’adu dabam-dabam. Mene ne ya sa waɗannan mutanen da suka fito daga wurare dabam-dabam suke da haɗin kai? Su wane ne ne Shaidun Jehobah?
AYYUKANMU
Darasi na 5-14
An san mu da aikin wa’azi. Muna yin taro a Majami’un Mulki domin mu yi ibada kuma mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Yaya ake gudanar da taron, kuma su wane ne za su iya halartan taron?
ƘUNGIYARMU
Darasi na 15-28
Ƙungiyar addini ce da ke faɗin duniya, kuma ba ta cin riba ba ce, mutanen da ke bin ta suna bauta wa Allah da son rai. Yaya aka tsara ƙungiyar nan, ta yaya ake tafiyar da ita, kuma ta yaya ake samun kuɗin da ake gudanar da ayyukanta? Tana yin nufin Jehobah a yau kuwa da gaske?