Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ll kashi 5 pp. 12-13
  • Babbar Rigyawa—Su Wane Ne Suka Yi Biyayya? Su Wane Ne Ba Su Yi Ba?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Babbar Rigyawa—Su Wane Ne Suka Yi Biyayya? Su Wane Ne Ba Su Yi Ba?
  • Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Makamantan Littattafai
  • Jirgin Nuhu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Sashe na 5
    Ka Saurari Allah
  • Nuhu Ya Gina Jirgi
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ya Yi “Tafiya Tare da Allah”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
Dubi Ƙari
Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
ll kashi 5 pp. 12-13

SASHE NA 5

Babbar Rigyawa—Su Wane Ne Suka Yi Biyayya? Su Wane Ne Ba Su Yi Ba?

Yawancin mutane a zamanin Nuhu sun yi abin da bai da kyau. Farawa 6:5

Wasu mugayen malai’iku da suka canja kamaninsu zuwa na mutane suna sha’ani da mata

Adamu da Hauwa’u sun haifi ’ya’ya, kuma mutane sun yi yawa a duniya. Bayan wani lokaci, wasu mala’iku suka yi tawaye kamar Shaiɗan.

Sun zo duniya kuma suka zama mutane domin su auri mata. Matan sun haifi ’ya’ya maza ƙatta masu mugun fushi da ƙarfi.

Wata mata tana rike da jariri kuma wani yaro yana mata naushi; kattai, yaran mugayen malai’iku suna aikata mugunta

Duniyar ta cika da mutanen da ke aikata abubuwa marar kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce “muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowacce shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kaɗai kullayaumi.”

Nuhu ya saurari Allah kuma ya gina jirgin. Farawa 6:13, 14, 18, 19, 22

Nuhu ya saurari Allah

Nuhu mutumi ne mai aminci. Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa, zai halaka mugayen mutane da babbar rigyawa.

Nuhu da iyalinsa sun gina jirgi

Allah ya kuma gaya wa Nuhu cewa ya gina jirgin ruwa mai girma, kuma ya shigar da iyalinsa da kowace irin dabba a cikinsa.

Nuhu ya gargade mutane kafin a fara Rigyawa, amma mutanen yi masa dariya

Nuhu ya gargaɗi mutane game da Rigyawar da ke tafe, amma ba su saurare shi ba. Wasu sun yi ma Nuhu dariya; wasu kuma sun tsane shi.

Nuhu da iyalinsa suna shigar da dabbobi cikin jirgin

Sa’ad da aka gama gina jirgin, Nuhu ya shigar da dabbobi cikin jirgin.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba