Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • bm sashe na 10 p. 13
  • Sulemanu Sarki Ne Mai Hikima

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sulemanu Sarki Ne Mai Hikima
  • Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Makamantan Littattafai
  • Shi Misali Mai Kyau Ne A Gare Ka Ko Kuma Kashedi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Haikalin Jehobah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Sulemanu Sarki Mai Hikima
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ka Daraja Yesu, Wanda Ya Fi Dauda Da Sulemanu Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
bm sashe na 10 p. 13

Sashe 10

Sulemanu Sarki Ne Mai Hikima

Jehobah ya ba Sarki Sulemanu zuciya mai hikima; a lokacin sarautar Sulemanu, Isra’ilawa sun shaida salama da kuma arziki marar iyaka

YAYA rayuwa za ta kasance idan al’umma gabaki ɗaya da kuma sarkinta suka bi Jehobah a matsayin Mamallakinsu kuma suka yi biyayya ga dokokinsa? An kwatanta amsar a lokacin sarauta ta shekara 40 na Sarki Sulemanu.

Kafin Dauda ya mutu, ya naɗa ɗansa Sulemanu a matsayin wanda zai gaje shi. A cikin mafarki, Allah ya gaya wa Sulemanu ya roƙi abin da yake so. Sulemanu ya roƙi hikima da fahimi don ya yi wa mutanen ja-gora yadda ya dace kuma cikin hikima. Jehobah ya yi farin ciki kuma ya ba Sulemanu zuciya mai hikima da fahimi. Kuma Jehobah ya yi masa alkawarin arziki, ɗaukaka, da tsawon rai idan iya ci gaba da yi masa biyayya.

Sulemanu ya zama sananne don hukuncinsa na hikima. Akwai lokacin da wasu mata biyu suke gardama a kan yaro jariri, kowannensu na da’awar cewa ita ce uwar. Sulemanu ya ba da umurni cewa a raba jaririn biyu kuma a ba kowace mata rabi. Mace ta farko ta yarda, amma nan da nan ainihin uwar ta yi roƙo cewa a ba da jaririn ga ɗayan matar. A nan Sulemanu ya gane cewa matar nan mai tausayi ita ce uwar kuma ya ba ta jaririnta. Nan da nan dukan Isra’ila ta ji wannan hukuncin da ya yanke, kuma dukan mutanen suka gane cewa hikimar Allah tana tare da Sulemanu.

Ɗaya daga cikin abubuwa mafi girma da Sulemanu ya cim ma shi ne gina haikalin Jehobah, gini ne mai girma a Urushalima da zai kasance cibiyar bauta a Isra’ila. Sa’ad da ake keɓe haikalin, Sulemanu ya yi addu’a: “Ga shi, sammai da samman sammai ba su da iko su karɓe ka: balle fa wannan gida da na gina!”—1 Sarakuna 8:27.

Sunan Sulemanu ya yaɗu zuwa ƙasashe, har ƙasar Sheba da ke Arabiya. Sarauniyar Sheba ta yi tafiya don ta ga ɗaukakar Sulemanu da arzikinsa kuma ta gwada zurfin hikimarsa. Hikimar Sulemanu da arzikin ƙasar Isra’ila sun burge sarauniyar har ta yaba wa Jehobah da ya naɗa irin wannan sarki mai hikima. Hakika, domin albarkar Jehobah, sarautar Sulemanu ta kasancewa mafi ɗaukaka tare da salama a tarihin Isra’ila ta dā.

Abin baƙin ciki, Sulemanu ya daina yin abubuwan da suka jitu da hikimar Jehobah. Ta wajen yin watsi da dokar Allah, ya auri ɗarurruwan mata, kuma yawancinsu suna bauta wa allolin ƙarya. Da sannu-sannu matansa suka rinjayi zuciyarsa daga bin Jehobah kuma ya soma bauta wa gumaka. Jehobah ya gaya wa Sulemanu cewa za a ƙwace sashen mulkinsa daga hannunsa. Sashe ɗaya ne kawai zai rage a iyalinsa, in ji Allah, domin Dauda mahaifin Sulemanu. Duk da kaucewar da Sulemanu ya yi, Jehobah ya kasance da aminci ga alkawarin Mulki da ya yi wa Dauda.

—An ɗauko daga 1 Sarakuna, surori 1 zuwa 11; 2 Labarbaru, surori 1 zuwa 9; Kubawar Shari’a 17:17.

◼ Menene Allah ya yi a kan roƙon da Sulemanu ya yi?

◼ Ta yaya ne Sulemanu ya nuna hikimarsa?

◼ Ta yaya ne Sulemanu ya kauce daga hanyoyin Jehobah, kuma menene sakamakon?

[Taswira a shafi na 13]

Farawa

Fitowa

Levitikus

Littafin Lissafi

Kubawar Shari’a

Joshua

Alƙalawa

Ruth

1 Sama’ila

2 Sama’ila

1 Sarakuna ●

2 Sarakuna

1 Labarbaru

2 Labarbaru ●

Ezra

Nehemiya

Esther

Ayuba

Zabura

Misalai

Mai-Wa’azi

Waƙar Waƙoƙi

Ishaya

Irmiya

Makoki

Ezekiel

Daniyel

Hosiya

Joel

Amos

Obadiya

Yunana

Mikah

Nahum

Habakkuk

Zafaniya

Haggai

Zakariya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba