Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • kp pp. 22-23
  • “Ba Su Lura ba”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ba Su Lura ba”
  • Ka Zauna A Faɗake!
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yaya Kake Ji Game da Gargaɗi da ke Fitowa Daga Wurin Allah?
  • Ku Tuna da Matar Lutu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Matar Lutu Ta Dubi Baya
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • “Ku Zauna A Faɗake”—Lokacin Hukunci Ya Yi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Ka Zauna A Faɗake!
kp pp. 22-23

“Ba Su Lura ba”

YIN banza da gargaɗi yana iya jawo bala’i.

Mutanen Darwin, a Australia, suna cikin shiri sosai na ranakun hutu a shekara ta 1974 sa’ad da suka ji jiniya tana faɗakar da jama’a cewa ƙila za a yi guguwa mai tsanani. Amma ya kai shekara 30 da guguwa mai tsanani ta auku a Darwin. Sai yanzu? Yawancin mazauna ba su ɗauki gargaɗin da muhimmanci ba har sai da iska ta fara ɓarke jinka da bangon gidaje da mutane suke maƙewa ciki. Kafin washegari, birnin ya zama kango.

Wani dutse ya yi aman wuta a Colombia a Nuwamba 1985. Ya narke dusar ƙanƙara kuma ya baza ƙanƙara mai taɓo da ya binne mazauna fiye da 20,000 a garin Armero. Ba a ba da gargaɗi ba ne? Cikin watanni duwatsun sun yi ta girgizawa. Amma, domin sun saba da zama kusa da duwatsu da ke gobara, yawancin mutanen Armero ba su damu ba. An gaya wa gwamnati cewa ba da daɗewa ba za a yi bala’i, amma ba su sanar wa jama’a ba. An yi sanarwa a rediyo don a tabbatar wa jama’a kada su damu. An yi amfani da bututun ɗaukan kuwwa don a gaya wa jama’a kada su firgita. A maraicen an shaida fashewar nakiya biyu. Da ka yi watsi da mallakarka kuma ka gudu? Ko mutane kalilan ma ba su yi motsi ba har sai da suka makara.

Sau da yawa masana halittar ƙasa sukan faɗi lokacin da za a yi girgizan ƙasa ya zama daidai. Amma ba sa iya faɗan daidai sa’ar da za ta auku. A shekara ta 1999, girgizar ƙasa ta lashe rayuka 20,000 a duk duniya. Mutane da yawa da suka mutu sun yi tsammanin ba zai taɓa faru musu ba.

Yaya Kake Ji Game da Gargaɗi da ke Fitowa Daga Wurin Allah?

Littafi Mai Tsarki ya kwatanta da daɗewa game da aukuwa da suke alamar kwanaki na ƙarshe. Game da wannan, ya aririce mu mu yi la’akari da “zamanin Nuhu.” “Kamar a kwanakin nan ne gabannin Ruwan Tsufana,” mutane sun taƙure da harkokin rayuwa, ko da yake sun damu da yawan mugunta da ke a lokacin. Game da gargaɗin da Allah ya bayar ta wurin bawansa Nuhu, “ba su lura ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su.” (Matiyu 24:37-39, NW ) Da ka saurari gargaɗin ne? Kana yin haka a yanzu?

Da kana zama a Saduma, kusa da Tekun Gishiri fa, a zamanin mutumin nan Lutu, ɗan wan Ibrahim? Yankin kamar aljanna take. Birnin mai ni’ima ce. Mutanen masu almubazzaranci ne. A zamanin Lutu, “ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine.” Suna cikin jama’a marasa ɗabi’a. Da ka saurari gargaɗin sa’ad da Lutu ya faɗakar game da munanan ayyuka? Da ka saurare shi sa’ad da ya gaya maka cewa Allah ya ƙudura ya halaka birnin Saduma? Ko kuma da ka ɗauka wasa ne yadda surukan Lutu suka yi? Ƙila za ka soma gudun amma sai ka juya baya, yadda matar Lutu ta yi? Ko da yake wasu ba su ɗauki gargaɗin da muhimmanci ba, ranar da Lutu ya bar Saduma, “aka zubo wuta da duwatsun wuta daga sama, aka halaka su duka.”—Luka 17:28, 29.

Yawancin mutanen zamaninmu ba sa lura. Amma an rubuta waɗannan misalai cikin Kalmar Allah domin gargaɗi gare mu, ya ƙarfafa mu MU ZAUNA A FAƊAKE!

[Akwati/Hoto a shafi na 22]

An Yi Rigyawa a Dukan Duniya da Gaske?

’Yan soke da yawa sun ce ba a yi ba. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce an yi.

Yesu Kristi ma ya yi zancensa, kuma yana da rai sa’ad da ya auku, yana kallo daga sama.

[Akwati/Hoto a shafi na 23]

An Halaka Saduma da Gwamrata da Gaske Kuwa?

’Yan tona ƙasa sun tabbatar da wannan aukuwar.

Tarihin duniya ya ambata wannan.

Yesu Kristi ya tabbatar da wannan aukuwa, kuma an ambata abin da ya faru cikin littattafai 14 na Littafi Mai Tsarki.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba