Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ol sashe na 1 pp. 4-5
  • Dukan Addinai ne Suke Koyar da Gaskiya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dukan Addinai ne Suke Koyar da Gaskiya?
  • Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Addininmu Dole ne Ya Kasance Bisa Gaskiya
  • Yadda Addinan Karya Suke Bata Sunan Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Mene Ne Zai Faru da Addini?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Allah Ya Yarda da Dukan Addinai Ne?
    Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
Dubi Ƙari
Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
ol sashe na 1 pp. 4-5

SASHE NA 1

Dukan Addinai ne Suke Koyar da Gaskiya?

1. Waɗanne addinai ne ake yi a Afirka?

KUSAN kowa a Afirka ya yarda cewa yana da muhimmanci matuƙa a bauta wa Allah. Amma, ba a jitu ba game da yadda za a bauta masa. Wasu suna bauta a masallaci, wasu kuma suna zuwa ɗakunan bauta ta al’ada. Har ila wasu suna zuwa coci. Amma ba daidai ba ne a yi tunanin cewa addinai uku ne kawai ake da su a Afirka. A tsakanin Musulmai da akwai bambancin dokoki da kuma imani. Addinan al’ada sun bambanta ƙwarai daga wuri zuwa wuri. Tsakanin Kiristoci masu zuwa coci kuma da akwai rashin jituwa ƙwarai da gaske. Ban da manyan coci coci, da akwai wasu dubbai masu zaman kansu a cikin dukan nahiyar Afirka.

Wata mata ta durkusa a gaban gunki; wani mutum ya durkusa a inda ake tsafi

Addininmu Dole ne Ya Kasance Bisa Gaskiya

2. (a) Menene ainihi yake ƙaddara addinin mutum? (b) Menene ba ya tabbatar da cewa addininmu yana faranta wa Allah rai?

2 Me ya sa mutane suke bauta yadda suke yi? Mutane da yawa suna bin addinan iyayensu ne. Abubuwa da suka faru can dā ma suna rinjayar addinan da mutane suke yi a yau. Littafin nan The Africans​—A Triple Heritage ya ce: “Musullunci ya yaɗu a arewacin Hamada ta wajen yaƙi, . . . Kiristanci ya yaɗu a kudancin Hamada ta wajen abu ɗaya. Idan a arewacin Hamada Musulunci ya yaɗu ta wajen takobi, a kudancin Hamada Kiristanci ya yaɗu ta wajen bindiga.” Duk da haka, yawancinmu mun gaskata cewa addininmu yana faranta wa Allah rai. Amma addini ba zai zama daidai ba domin kawai iyayenmu suna yin sa ko kuma domin wasu al’ummai masu ƙarfi sun tilasta wa kakanninmu.

3-5. Wane misali ne ya taimake mu ganin cewa ba dukan addinai ba ne suke koyar da gaskiya?

3 Ko da yake, dukan addinai suna da’awar cewa suna ba da ja-gora mai kyau game da bauta wa Allah, ra’ayoyinsu sun bambanta. Suna koyar da abubuwa dabam dabam game da Allah da kuma abin da yake bukata a gare mu. Ka yi tunani game da wannan: A ce, ka samu aiki a wata babbar masana’anta. A ranarka ta farko a wajen aiki, aka ce maka maigidanka ya je hutu. Sai ka tambayi ma’aikata uku abin da za ka yi. Na farkon ya ce maigidan yana so ka yi shara. Na biyun ya ce ka yi fentin gini. Na uku ya ce ka rarraba wasiƙu.

4 Daga baya, ka tambayi ma’aikatan game da maigidan. Na farkon ya ce maigidan saurayi ne, dogo, mai zafin rai. Na biyun ya ce tsoho ne, gajere, mai fara’a. Na ukun ya gaya maka cewa mai gidan ba namiji ba ne ma sam sam​—tamace ce. Wataƙila, za ka ce waɗannan ma’aikata uku ba gaskiya suke gaya maka ba. Idan kana so ka ci gaba da aikinka, wataƙila za ka yi wasu bincike ka san waye ne ainihi maigidan, da kuma abin da yake so ko take so ka yi.

5 Haka yake da addini. Domin da akwai ra’ayoyi da yawa game da Allah da kuma abin da yake bukata a gare mu, muna bukatar mu tabbata cewa hanyar bautarmu ta jitu da gaskiya. Amma ta yaya za mu koyi gaskiya game da Allah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba