Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • jt pp. 3-5
  • Su Wanene ne Su?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Su Wanene ne Su?
  • Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SUNANSU
  • Me Ya Sa Ake Kiran Mu Shaidun Jehobah?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
jt pp. 3-5

Su Wanene ne Su?

SHAIDUN Jehovah suna so ka sarƙu da su sosai. Wataƙila ka sadu da su wajen maƙwabtaka ko kuma wajen aiki ko kuma a wasu harkokin rayuwa na yau da kullum. Mai yiwuwa ka gan su a kan titi suna ba da jaridu ga waɗanda suke wucewa. Ko kuma ka yi ɗan magana da su a ƙofarka.

Hakika, Shaidun Jehovah sun damu da kai da kuma lafiyarka. Suna so su zama abokanka su gaya maka game da kansu, imaninsu, ƙungiyarsu, da yadda suke ji game da mutane da kuma duniya da dukanmu ke zama cikinta. Domin su cim ma wannan, sun shirya wannan mujalla dominka.

A hanyoyi da yawa Shaidun Jehovah suna daidai da kowane mutum. Suna da nasu matsaloli—na tattalin arziki, na jiki, da na jiye-jiye. Wasu lokatai suna kuskure, domin ajizai ne su, ba hurarru ba ne. Suna ƙoƙari su koya daga abin da ya same su kuma su yi nazarin Littafi Mai-Tsarki don su yi gyara da ake bukata. Sun keɓe kansu su yi nufin Allah, kuma sun ba da kansu su cika wannan keɓewar kan. A duk ayyukansu suna neman ja-gora daga Kalmar Allah da kuma ruhunsa mai tsarki.

Yana da muhimmanci gare su imaninsu ya zama yana da tushe cikin Littafi Mai-Tsarki ba a kan ƙage na mutane ba ko kuma ƙa’idar addinai. Suna ji kamar yadda manzo Bulus ya ji da aka hura shi ya furta: “Bari Allah ya zama mai-gaskiya, ko da kowane mutum maƙaryaci ne.” (Romawa 3:4, Litafi Mai-Tsarkia) Idan ya zo ga koyar da gaskiyar Littafi Mai-Tsarki, Shaidun sun yarda da halin Biriyawa lokacin da suka ji wa’azin manzo Bulus: “Suka karɓi magana da yardar rai sarai, suna bin cikin littattafai kowace rana, su gani ko waɗannan al’amura haka su ke.” (Ayukan Manzanni 17:11) Shaidun Jehovah sun gaskata cewa ya kamata a gwada duk koyarwan addini da hurarrun Nassosi a gani, ko su suka koyar ko kuma wani. Suna gayyatarka—suna aririta ka—ka yi haka lokacin da ka ke zance da su.

A bayane yake cewa Shaidun Jehovah sun gaskata Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne. Sun gaskata littattafansa 66 hurarru ne kuma ba su da kuskure wajen tarihi. Abin da aka saba kira Sabon Alkawari, su suna kiransa Nassosin Kirista na Helenanci, kuma suna kiran Tsohon Alkawari, Nassosin Ibrananci. Sun dangana a waɗannan, Nassosin Helenanci da Ibrananci, suna ɗaukansu a zahiri sai dai inda furci ko kuma yanayin yadda aka rubuta ya nuna cewa ta alama ce. Sun gane cewa annabce-annabce da yawa na Littafi Mai Tsarki sun cika, wasu suna kan cika, har ila wasu kuma za su cika a nan gaba.

SUNANSU

Shaidun Jehovah? Hakika, haka suke kiran kansu. Sunan kwatanci ne, da ke nuna cewa suna shaida game da Jehovah, Allahntakarsa, da kuma ƙudurinsa. “Allah,” “Ubangiji,” da “Mahalicci”—kamar “Shugaba,” “Sarki,” da “Janar”—duk laƙabi ne kuma za a iya amfani da su ga mutane dabam dabam. Amma “Jehovah” sunansa ne, yana nufin Allah Maɗaukaki da Mahaliccin sararin samaniya. An nuna wannan a cikin Litafi Mai-Tsarki a Zabura 83:18: “Domin su sani kai, wanda sunanka JEHOVAH ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.”

Sunan nan Jehovah (ko kuma Yahweh yadda Jerusalem Bible na Roman Katolik da wasu manazarta suka fi so) ya bayyana kusan sau 7,000 a Nassosin Ibrananci na asali. Yawancin Littafi Mai Tsarki ba su nuna shi haka nan ba amma sun canja da “Allah” ko “Ubangiji.” Amma, a cikin waɗannan Littafi Mai Tsarki ma, mutum da sauƙi zai san inda ayoyin Ibrananci na asali suka yi amfani da Jehovah saboda a wuraren nan da aka canja an rubuta su da manya da kuma ƙananan baƙaƙe haka: ALLAH, UBANGIJI. Da yawa a cikin fassarar zamani suna amfani da sunan nan Jehovah ko kuma Yahweh. Saboda haka, New World Translation ya ce a Ishaya 42:8, “Ni ne Jehovah. Wannan sunana ke nan.”

Nassi da Shaidun Jehovah suka ɗauko sunansu shi ne sura ta 43 na Ishaya (NW ). A wurin duniya tana kama da kotu: An gaya wa allolin al’ummai su kawo shaidu su tabbatar da da’awarsu na cewa su masu adalci ne ko kuma su ji daga wajen shaidun Jehovah kuma su san gaskiya. A wurin Jehovah ya sanar wa mutanensa: “Ku shaiduna ne, in ji Jehovah, barana kuma wanda na zaɓa; domin ku sani ku gaskata da ni kuma, ku fahimta kuma cewa ni ne shi; gabana ba a kamanta wani Allah ba, bayana kuma ba za a yi ba. Ni dai, ni ne Jehovah: kuma in banda ni babu wani mai ceto.”—Ishaya 43:10, 11, American Standard Version.

Jehovah Allah yana da shaidu a duniya shekaru dubbai kafin a haifi Yesu. Bayan Ibraniyawa sura ta 11 ta tsara wasu cikin waɗannan mutane masu aminci, Ibraniyawa 12:1 ta ce: “Domin wannan fa mu kuma, da shi ke taron shaidu mai-girma haka yana kewaye da mu, bari mu tuɓe kowane abin nauwaitawa, da zunubin da ke manne mamu, tare da haƙuri kuma mu yi tseren da an sa gabanmu.” Yesu ya ce a gaban Bilatus Babunti: “Domin wannan an haife ni. Domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya.” An kira shi “amintaccen mashaidi mai-gaskiya.” (Yohanna 18:37; Ru’ya ta Yohanna 3:14) Yesu ya gaya wa almajiransa: “Za ku karɓi iko lokacinda Ruhu Mai-tsarki ya zo bisanku; za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.”—Ayukan Manzanni 1:8.

Saboda haka, mutane 6,000,000 a yau da suke yin bisharar Mulkin Jehovah ta hannun Kristi Yesu a fiye da ƙasashe 230 sun ga daidai ne su kira kansu Shaidun Jehovah.

[Hasiya]

a Sai ko an ba da alama, dukan ayoyin Littafi Mai Tsarki da aka yi amfani da su cikin wannan mujallar daga Litafi Mai-Tsarki ne kuma an yi amfani da harufan zamani.

[Bayanin da ke shafi na 4]

Sun keɓe kansu ga Allah su yi nufinsa

[Bayanin da ke shafi na 4]

Sun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce

[Bayanin da ke shafi na 5]

Sunan kamar ana cikin kotu

[Bayanin da ke shafi na 5]

Shaidu 6,000,000 a ƙasashe fiye da 230

[Hoto a shafi na 3]

Suna son ka

[Hoto a shafi na 4]

Sunan Allah a Ibrananci na dā

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba