Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • gf darasi na 14 pp. 22-23
  • Aminan Allah Suna guje Ma Abin Da Ba Shi Da Kyau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Aminan Allah Suna guje Ma Abin Da Ba Shi Da Kyau
  • Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
  • Makamantan Littattafai
  • Ayukan da Allah Baya So
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Mene Ne Muke Bukatar Mu Yi Don Mu Faranta wa Allah Rai?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Sashe na 13
    Ka Saurari Allah
  • Mene Ne ra’ayinka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
Dubi Ƙari
Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
gf darasi na 14 pp. 22-23

DARASI NA 14

Aminan Allah Suna guje Ma Abin Da Ba Shi Da Kyau

Shaiɗan yana jarabtar mutane su yi abubuwan da ba su da kyau. Mutumin da yake son ya zama aminin Allah yana bukatar ya tsane abin da Jehobah ya tsana. (Zabura 97:10) Ga wasu abubuwa da aminan Allah suka tsana:

Abubuwan da Jehobah ya tsana, kamar lalata da maye da giya da zubar da ciki da sata da karya da fada, da kuma caca

Lalata da zina. “Ba za ka yi zina ba.” (Fitowa 20:14) Ƙari ga haka, yin jima’i kafin aure zunubi ne.—1 Korintiyawa 6:18.

Yin maye. “Masu-maye . . . ba za su gāji mulkin Allah ba.”—1 Korintiyawa 6:10.

Kisan kai, zubar da ciki. “Ba za ka yi kisan kai ba.”—Fitowa 20:13.

Sata. “Ba za ka yi sata ba.”—Fitowa 20:15.

Ƙarya. Jehobah ba ya son “harshe mai-ƙarya.”—Misalai 6:17.

Yawan fushi da kuma mugunta. “Mai-mugunta da mai-son zalunci ransa [Jehobah] yana ƙinsu.” (Zabura 11:5) “Ayyukan jiki [sun haɗa da] . . . hasala.”—Galatiyawa 5:19, 20.

Caca. ‘Kada ku yi tarayya da mutum . . . mai-kwaɗayi.’—1 Korintiyawa 5:11.

Ƙiyayya saboda launin fata ko ƙabila. “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta maku, ku yi masu addu’a.”—Matta 5:43, 44.

Abubuwan da Allah ya gaya mana don amfanin kanmu ne. Ba kowane lokaci ba ne yake da sauƙi mu ƙi abubuwan da ba su da kyau. Da taimakon Jehobah da kuma na Shaidunsa, za mu iya ƙin abubuwan da suke ɓata wa Allah rai.—Ishaya 48:17; Filibiyawa 4:13; Ibraniyawa 10:24, 25.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba