Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • dg kashi 11 pp. 28-32
  • Sashe na 11—Ana Kafa Tushin Sabuwar Dunyia Yanzu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sashe na 11—Ana Kafa Tushin Sabuwar Dunyia Yanzu
  • Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yan’uwantaka na Dukan Ƙasashe na Gaske
  • Sakankance Mutanen Allah
  • Wani Fasalin Sakankancewa
  • Amsa Muhawwara Mai-girma na Biyu
  • Minene Zaɓenka?
  • Su Waye Suke Yin Addini na Gaskiya?
    Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
dg kashi 11 pp. 28-32

Sashe na 11—Ana Kafa Tushin Sabuwar Dunyia Yanzu

1, 2. A cikin cikawar annabcin Littafi Mai-tsarki fa, minene yake faruwa a idanunmu?

ABIN ban al’ajibi kuma shine lazun cewa ana kafa tushin sabuwar duniyan Allah yanzu, ko da tsofuwar duniyar Shaitan tana rugugujjewa. A idanunmu, Allah yana tattara mutane daga dukan al’ummai kuma yana shirya su cikin tushin sabuwar jam’iyya na duniya wanda bada daɗewa ba zai dauki matsayin ruɓaɓɓiyar duniyar nan. A cikin Littafi Mai-tsarki, a 2 Bitrus 3:​13, an kira sabuwar jam’iyyar nan “sabuwar duniya.”

2 Annabcin Littafi Mai-tsarki ma ya ce: “Zaya zama a cikin kwanaki na ƙarshe [lokaci da muke ciki yanzu] . . . , Dangogi dayawa kuwa zasu tafi su ce, Ko zo, mu hau zuwa dutsen Jehovah [sujadarsa na gaskiya], . . . shi ma zaya koya mana tafarkinsa, mu kuma mu kama tafiya cikin hanyoyinsa.”​—⁠Ishaya 2:​2, 3.

3. (a) A tsakanin su waɗannene annabcin Ishaya ke cikawa? (b) Ina yadda littafin Littafi Mai-tsarki na ƙarshe ya yi zance game da wannan?

3 Ana cika annabcin nan yanzu a tsakanin waɗanda suke bada kansu ga ‘hanyoyin Allah kuma suna tafiya cikin tafarkunsa.’ Littafi na ƙarshe na Littafi Mai-tsarki ya yi zance game da jam’iyya na dukan duniya mai-ƙaunar salamar nan kamar “babban garke . . . daga dukan kabilai da al’ummai da harsuna,” yan’uwantakan dukan duniya na gaskiya da ke bauta wa Allah a haɗe. Littafi Mai-tsarki kuma ya ce: “Sune waɗanda suka fito daga cikin babban tsananin.” Watau wai, sun tsira ma ƙarshen wannan miyagun shirin abubuwa.​—⁠Ru’ya ta Yohanna 7:​9, 14; Matta 24:⁠3.

Yan’uwantaka na Dukan Ƙasashe na Gaske

4, 5. Me yasa yan’uwantakan Shaidun Jehovah na dukan duniya ke yiwuwa?

4 Miliyoyin Shaidun Jehovah da gaskiya suna ƙoƙarin rayuwa cikin jituwa da koyaswan Allah da hanyoyinsa. Begensu na madawwamiyar rai a kafe yake cikin sabuwar duniyar Allah. Ta wurin rayuwarsu na kullayaumi cikin biyayya da dokokin Allah fa, suna nuna shiryawarsu su yi biyayya da hanyar sarautarsa yanzu da kuma cikin sabuwar duniyan. A ko’ina, ko da minene al’ummarsu ko kuwa fata dai, suna biyayya ga mizanai ɗaya da​—⁠Allah ya jera cikin Kalmarsa. Shi yasa su yan’uwantaka na ƙasashe ne na gaskiya, sabuwar jam’iyyar duniya yin Allah.​—⁠Ishaya 54:13; Matta 22:​37, 38; Yohanna 15:​9, 14.

5 Shaidun Jehovah basu ba kansu darajar kasancewarsu na yan’uwantaka na dukan duniya wanda dabam yake ba. Sun sani cewa wannan sakamakon ikon ruhu mai-tsarki na Allah ne da ke aika bisa mutane da suke biyayya da dokokinsa. (Ayukan Manzanni 5:29, 32; Galatiyawa 5:22, 23) Abinda Allah ya yi ne. Kamar yadda Yesu ya fada, “abinda ba shi yiwuwa ga mutum ya yiwu ga Allah.” (Luka 18:27) Saboda haka Allah wanda ya kafa sararin halitta mai-jurewa shine ma wanda yasa sabuwar jam’iyya na duniya mai-jurewa ta yiwu.

6. Me yasa za a iya ƙiran yan’uwantaka na Shaidun Jehovah mu’ujiza na zamani?

6 Saboda haka, ana iya ganin hanyar sarautar Jehovah na sabuwar duniyar yanzu cikin abinda yake haifad cikin tushin sabuwar duniyar da ake shiryawa yanzu. Kuma abinda ya yi ko da Shaidunsa, a wata azanci fa, mu’ujiza ne na zamani. Don me? Domin ya shirya Shaidun Jehovah cikin yan’uwantaka na gaskiya a dukan duniya, wanda tsatsaguwar al’ummai, na fata, ko kuwa na addini ba zai rushe shi ba. Yayinda Shaidun sun kai miliyoyi kuma suna cikin ƙasashe sama da 200, a haɗe suke kamar ɗaya a cikin dangantaka mara karyawa. Wannan yan’uwantaka na dukan duniya, wanda dabam yake a duk tarihi, mu’ujiza ne ƙwarai na zamani​—⁠yin Allah.​—⁠Ishaya 43:10, 11, 21; Ayukan Manzanni 10:34, 35; Galatiyawa 3:⁠28.

Sakankance Mutanen Allah

7. Ina yadda Yesu ya ce za a sakankance mabiyansa na gaskiya?

7 Ina yadda za a ƙara rabe mutanen da Allah yake amfani da su don kafa tushin sabuwar duniyarsa? To dai, waɗannene suke cika kalmomin Yesu a Yohanna 13:​34, 35? Ya furta: “Sabuwar doka nike ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka zasu fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” Shaidun Jehovah sun gaskata da kalmomin Yesu kuma suna aika bisa hakan. Kamar yadda Kalmar Allah ya koyas fa, suna da “ƙauna mai-huruwa zuwa ga juna.” (1 Bitrus 4:⁠8) Sun “yafa [ma kansu] ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kolossiyaawa 3:14) Saboda haka fa ƙauna na yan’uwa ita ce “magami” da ke riƙe su tare a duk duniya.

8. Ina yadda 1 Yohanna 3:​10-⁠12 ya sakankance mutanen Allah kuma?

8 1 Yohanna 3:​10-12 ma, ya ce: “Inda ’ya’yan Allah sun bayanu ke nan, da ’ya’yan Shaitan: dukan wanda ba shi aika adilci ba, ba na Allah ba ne, da wannan kuma wanda baya yi ƙaunar dan’uwansa ba. Gama jawabi ke nan da ku ka ji tun daga farko, mu yi ƙaunar junanmu; ba kamar Kayinu wanda shi ke na Shaitan, ya kashe dan’uwansa.” Saboda haka, mutanen Allah mara aika laifi ne, yan’uwantaka na duk duniya ne.

Wani Fasalin Sakankancewa

9, 10. (a) Ta wurin wane aiki ne za a sakankance bayin Allah a cikin kwanaki na ƙarshe? (b) Ina yadda Shaidun Jehovah sun cika Matta 24:⁠14 ko?

9 Akwai wata hanya kuma na sakankance bayin Allah. A cikin annabcinsa game da ƙarshen duniya, Yesu ya ambata abubuwa dayawa da zasu alamce lokaci na kwanaki na ƙarshe. (Duba Sashe na 9.) Sashe na musamman na wannan annabcin an ambata shi a cikin kalmominsa a Matta 24:14: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuka zata zo.”

10 Ashe annabcin nan yana cikawa kuwa? I. Gama tun kwanaki na ƙarshe da suka soma a 1914, Shaidun Jehovah sun yi wa’azin bisharar Mulkin Allah ko a dukan duniya a fasalin da Yesu ya umurta, watau, a gidajen mutane. (Matta 10:​7, 12; Ayukan Manzanni 20:20) Miliyoyin Shaidu suna ziyarar mutane cikin kowane al’umma don su yi masu zance game da sabuwar duniya. Wannan shi ya kai ga samun mujallar nan kai kanka, da shike aikin Shaidun Jehovah yana haɗe da bugu da kuma rarraba biliyoyin littattafai game da Mulkin Allah. Ka san da wani kuma wanda yake wa’azin Mulkin Allah daga gida zuwa gida a dukan duniya? Markus 13:10 ya nuna cewa wannan aikin wa’azi da koyaswa dole ya zama abu na “fari,” da za a yi kafin ƙarshen zata zo.

Amsa Muhawwara Mai-girma na Biyu

11. Minene Shaidun Jehovah suke kamalawa ta wurin yin biyayya da sarautar Allah?

11 Ta wurin yin biyayya da dokoki da ka’idodin Allah fa, Shaidun Jehovah sun cimma wani abu dabam. Sun nuna cewa Shaitan maƙaryaci ne da da’awar cewa yan-Adam ba zasu kasance da aminci ga Allah ƙalƙashin gwadawa ba, da haka suna amsa muhawwara mai-girma na biyu, da ya shafe riƙe kāmalar yan-Adam. (Ayuba 2:​1-5) Kamar jam’iyya na miliyoyin mutane daga dukan al’ummai fa, Shaidun sun nuna, imani ga sarautar Allah, kamar jiki ɗaya. Ko da shike su yan-Adam marasa cikawa ne, sun ɗaukaka ra’ayin Allah na muhawwara na ikon sarautar dukan sararin halitta duk da tsananin shaitan.

12. Ta wurin bangaskiyarsu, wanene Shaidun suke kofa?

12 Ayau fa, waɗannan miliyoyin Shaidun Jehovah sun daɗa shaidarsu ga wasu shaidu dayawa na lokuttan dā waɗanda suka nuna imani ga Allah. Wasun su sūne Habila, Nuhu, Ayuba, Ibrahim, Saratu, Ishaƙu, Yakubu, Deborah, Ruth, Dawuda, da Daniel, kalila ke nan kaɗai fa. (Ibraniyawa, sura 11) Su daidai ne, kamar yadda Littafi Mai-tsarki ya ce, ‘taron amintattun shaidu mai-girma.’ (Ibraniyawa 12:⁠1) Waɗannan, da wasu haɗe da almajiran Yesu sun riƙe kāmalarsu ga Allah. Yesu kuma ya tanadar da misali mai-girma duka na riƙe cikakken kāmala.

13. Minene Yesu ya gaya ma shugabannen addinai game da Shaitan da ya tabbata gaskiya?

13 Wannan ya tabbatas da cewa abinda Yesu ya faɗi ga shugabannen addinai game da Shaitan gaskiya ne: “Amma yanzu ku na nema ku kashe ni, ni wanda na fada maku gaskiya, wadda na ji daga wurin Allah. . . . Ku na ubanku Shaitan ne, ƙyashe ƙyashe na ubanku kuma kuna da nufi ku yi. Shi mai-kisan kai ne tun daga farko, baya tsaya a kan gaskiya ba, domin babu gaskiya a cikinsa. Sa’anda yake yin ƙarya, don kasan yake yi; gama maƙaryaci ne shi, da uban ƙarya kuma.”​—⁠Yohanna 8:​40, 44.

Minene Zaɓenka?

14. Minene ke faruwa ga tushin sabuwar duniyar?

14 Tushin sabuwar duniya da Allah yake shiryawa yanzu cikin jam’iyya na ƙasashe na Shaidun Jehovah yana ƙara ƙarfi. Kowace shekara dubban darurrukan mutane suna amfani da son zuciyarsu, mai-tushe bisa tacaccen sani, su kuma amshi sarautar Allah. Sun zama sashen sabuwar jam’iyya na duniya, suna ɗaukaka ra’ayin Allah na muhawwarar ikon sarautar dukan sarari, kuma tabbatas da Shaitan maƙaryaci.

15. Wane aikin rarrabawa ne Yesu ke tafiyadda shi cikin kwananmu?

15 Don sun zaɓa sarautar Allah fa, sun inganta a sanya su a “hannun dama” na Kristi kamar yadda yake ware “tumakin” daga “awaki.” A cikin annabcinsa game da kwanaki na ƙarshe fa, Yesu ya ce: “A gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai; shi kuwa zaya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi ya kan rarraba tumaki da awaki; kuma zaya sanya tumaki ga hannun damansa, amma awaki ga hagu.” Tumakin sūne mutane masu tawali’u waɗanda suke tarayya da kuma goye bayan yan’uwan Kristi, waɗanda suke biyayya da sarautar Allah. Awakin sūne mutane masu-taurin kai wadanda suka ƙi da yan’uwan Kristi kuma basu yin wani abu don goyon bayan sarautar Allah ba. Da kuma wane sakamako? Yesu ya ce: “Waɗannan [awakin] kuwa zasu tafi cikin hukunci na har abada; amma masu-adilci [tumakin] cikin rai na har abada.”​—⁠Matta 25:​31-⁠46.

16. Minene tilas ne ka yi idan kana son ka rayu cikin Aljanna mai-zuwan?

16 Lallai fa, Allah yana kula da mu! Bada jimawa ba zaya tanadar da duniya ta aljanna mai-dadi. Kana son ka rayu cikin Aljannan nan? Idan haka ne, ka nuna godiyarka ga tanadodin Jehovah ta wurin koyawa game da shi da kuma aikawa bisa abinda ka koya. “Ku nemi Jehovah tun yana samuwa; ku yi kiransa tun yana kusa; mai-mugunta shi saki hanyatasa, mara-adilci kuma shi bar tunaninsa; shi komo wurin Jehovah, shi kuwa zaya jikansa.”​—⁠Ishaya 55:​6, 7.

17. Me yasa babu karin lokaci da za a batas a zaban wanda za a bauta masa?

17 Babu ɓata lokaci kuma. Ƙarshen wannan tsofuwar shirin ta yi kusa. Kalmar Allah ya galgadas: “Kada ku yi ƙaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya. Idan kowa ya yi ƙaunar duniya, kaunar Uba ba ta cikinsa ba . . . Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”​—⁠1 Yohanan 2:​15-⁠17.

18. Wane mataki ne zai taimake ka ka kasance da begen rayuwa cikin sabuwar duniyar Allah mai-ban al’ajibi da gabagaɗi?

18 Ana koyas da mutanen Allah yanzu don rai na har abada cikin sabuwar duniya. Suna koya ingantai na ruhaniya da wasu da ake bukata don gina aljannan. Muna zuga ka ka zabi Allah kamar Mai-sarauta kuma ka goye bayan aikin cetas da rai da yake yi ayau a dukan duniya. Ka nazarta Littafi Mai-tsarki da Shaidun Jehovah, kuma ka zo ga sanin cewa Allah wanda yake kulawa da kai da gaske da kuma wanda zai kawo ƙarshe ga shan wahala. Ta haka fa kai ma zaka zama tushin sabuwar duniyan. Da haka fa zaka kasance da begen samun jinkan Allah da kuma rayuwa har abada cikin sabuwar duniyar nan mai-ban al’ajibi da gabagadi.

[Hoto a shafi na 31]

Shaidun Jehovah suna da yan’uwantaka na ƙasashe na gaskiya

[Hoto a shafi na 32]

Ana shirya tushin sabuwar duniyar yanzu haka

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba