Sashe na 5—Ƙyautar Son Zuciya Mai-Ban Al’Ajibi
1, 2. Wane kyauta mai-ban al’ajibi ne sashen fasalin jikinmu?
DON GANE dalilin da yasa Allah ya kyale shan wahala da kuma abinda zaya yi game da shi fa, muna bukata mu san yadda ya yi mu. Ya yi abu fiye da halicce mu da jiki da ƙwalƙwalwa kawai. Ya halicce mu da ingantai na azanci da jiye-jiye na musamman.
2 Sashen fasalinmu na musamman na azanci da jiye-jiye shine son zuciya. I fa, Allah ya shuka cikin mu azancin yancin zaɓe. Ƙyauta ne fa na ban al’ajibi daga gareshi.
Yadda Aka Yi Mu
3-5. Me yasa muke godiya da samun son zuciya?
3 Bari mu yi la’akari da yadda zancen son zuciya ke kunshe cikin kyale shan wahala da Allah ya yi. Don a soma fa, ka yi tunani akan wannan: Kana jin daɗin samun yancin zaɓan abinda zaka yi da kuma faɗa, abinda zaka ci da kuma yafa, irin aiki da zaka yi, da kuma wuri da yadda zaka rayu? Ko kuwa kana son wani ya gaya maka kowane kalma da abinda zaka yi a kowane lokaci dukan rayuwarka?
4 Babu wani mutum mai-azanci da zai so a sarrafa masa kowane sashen rayuwarsa haka sarai. Don me a’a? Domin yadda Allah ya yi mu ne. Littafi Mai-tsarki ya gaya mana cewa Allah ya halicce mutum cikin ‘siffarsa da kamaninsa,’ kuma ɗaya daga cikin ingantai da Allah yake da shi shine yancin zaɓe. (Farawa 1:26; Kubawar Shari’a 7:6) Lokacinda ya halicce yan-Adam fa, ya basu ingancin nan mai ban-al’ajibi—ƙyautar son zuciya. Shi yasa mukan iske shi abin baƙinciki ne don wasu masu sarautar cin zali su wulakas da mu.
5 Saboda haka sha’awar samun yanci ba hatsari ba ne, gama Allah Allah na yanci ne. Littafi Mai-tsarki ya ce: “Inda ruhun Jehovah yake, nan akwai yanci.” (2 Korinthiyawa 3:17) Shi yasa, Allah ya ba mu azancin son zuciya kamar fasalin ranmu. Tun da shike ya san yadda azantanmu da jiye-jiyenmu zasu yi aiki, ya san da cewa zamu fi farinciki idan muna da yancin zaɓe.
6. Ta yaya Allah ya halicce ƙwalƙwalwanmu ya aika cikin jituwa da son zuciya?
6 Tare da ƙyautar son zuciyar nan fa, Allah ya bamu ingancin yin tunani, gwada al’amura, tsai da shawarwarai, kuma san abinda ke daidai da kuma mumuna. (Ibraniyawa 5:14) Domin haka, za a dangana son zuciya bisa zaɓe mai-hikima ne. Ba a yi mu kamar irin yar sā mara azancin kansu ba. Ba kuwa an halicce mu mu yi abubuwa ta wurin ilhami kamar dabbobi ba. Maimakon haka, an shirya ƙwalƙwalwanmu na ban-al’ajibi ya aika cikin jituwa da yancinmu na zaɓe.
Somawa Mafi Kyau Duka
7, 8. Wane somawa mai-kyau ne Allah ya ba iyayenmu na farko?
7 Don nuna yadda Allah yake da kulawa fa, an ba iyayenmu na fari, Adamu da Hawa’u, abinda dai mutum ke so, a haɗe da kyautar son zuciya. An sa su cikin aljanna mai-kama da gadina, mai fadi. Suna da abubuwa a yalwace. Suna da kamiltattun hankula da jikuna, saboda haka ba zasu tsufa ko yi ciwo ko kuwa mutu ba—da kuwa sun rayu har abada. Da sun haifa yara kamiltattu waɗanda su ma zasu kasance da gaba mai-farinciki, madawwamiya. Kuma da jimilla mai yawaitawar sun samu aiki mai-koshed wa wanda da sannu sannu ya juyad da dukan duniya cikin aljanna.—Farawa 1:26-30; 2:15.
8 Game da abinda aka tanadar fa, Littafi Mai-tsarki ya ce: “Allah kuma ya ga kome da ya yi, yana da kyau ƙwarai.” (Farawa 1:31) Littafi Mai-tsarki ma ya faɗi haka game da Allah: “Cikakke ayukansa suke.” (Kubawar Shari’a 32:4) I fa, Mahalicci ya ba iyalin yan-Adam cikakkiyar somawa. Babu wani abu da ya fi haka. Dubi fa Allah mai kulawa sarai!
Yanci Cikin Iyaka
9, 10. Don me tilas ne a sarrafa son zuciya daidai?
9 Amma, ashe Allah ya nufa cewa son zuciya ya kasance babu iyaka ne? Ka yi tsammanin babbar birni mara dokokin tafiya, inda kowa zai tuƙa motarsa a ko’ina kawai da gudun da ya ga dama. Ashe zaka so ka tuƙa mota a cikin yanayoyin nan? A’a, hakan lallai zai zama rashin dokar tafiya ne kuma zai jawo hatsari na ƙwarai.
10 Hakanan ma yake da kyautar Allah na son zuciya. Yanci mara iyaka zai nufa rashin yin abu daidai cikin jam’iyyar. Tilas a kasance da dokoki da zasu tsare ayukan yan-Adam. Kalmar Allah ya ce: “Ku yi tafiya kamar yantattu, kuma kada ku yi amfani da yancinku hujjar mugunta.” (1 Bitrus 2:16, JB ) Allah yana son a daidaita son zuciya ga halin kirki. Bai nufe mu da samun yanci mara-iyaka ba amma yanci mai-iyaka, wanda ke ƙalƙashin dokar sarauta.
Dokokin Wanene?
11. An shirya mu mu yi biyayya da dokokin wanene?
11 An shirya mu mu yi biyayya da dokokin wanene? Wata sashen nassi na 1 Bitrus 2:16 (JB ) ya ce: “Ku ba bayin kowa ba sai dai Allah.” Wannan ba yana nuni ga bawanci na zalunci ba ne, amma, maimakon haka, yana nufin cewa an shirya mu mu kasance da farinciki yayinda muke biyayya ga dokokin Allah. (Matta 22:35-40) Dokokinsa, fiye suke da dokoki yan-Adam da suka taɓa kafawa, yana tanadar da jagabanci mafi-kyau. “Ni ne, Jehovah, Allahnka, Wanda yake koya maka zuwa amfaninka, Wanda yana bishe ka ta hanyar da zaka bi.”—Ishaya 48:17.
12. Wane yancin zaɓe ne muke da shi cikin dokokin Allah?
12 Har ila kuma, dokokin Allah suna ba da yanci mai-girma na zaɓe cikin iyakansu. Wannan ya kawo bambance-bambance wanda ke sa iyalin yan-Adam ya zama abin marmari. Ka dai yi tunanin ire-iren abinci, tufafi, kaɗe-kaɗe, zane-zane, da gidaje dabam dabam a duk duniya. Lallai fa zamu so mu yi namu zaɓe azancen al’amura kamar waɗannan maimakon wani ya yi mana.
13. Waɗanne dokoki na sarari ne tilas mu yi biyayya da su don amfanin kanmu?
13 Saboda haka an halicce mu mu kasance da farinciki na ƙwarai yayinda muke biyayya ga dokokin Allah azancen halayen yan-Adam. Kama yake da yin biyayya ga dokokin Allah na sarari. Alal misali, idan muka yi banza da dokar maganaɗinsu kuma yi tsalle cikin iska daga wani wuri mai-nisa, zamu ji rauni ko kuwa mutu. Idan mu ka yi banza da dokoki na cikin jikinmu kuma muka denna cin abinci, shan ruwa, ko kuwa shaƙa iska, lallai zamu mutu.
14. Ina yadda muka sani cewa ba a halicce yan-Adam su zama a yance daga Allah ba?
14 Daidai yadda yake cewa an halicce mu da bukatar yin biyayya ga dokokin Allah na sarari fa, haka yake cewa an halicce mu da bukatar yin biyayya ga dokokin Allah na ɗabi’a da kuma na zaman jama’a. (Matta 4:4) Ba a halicce yan-Adam su zama a yance daga Mai-yinsu har kuma su yi nasara ba. Annabi Irmiya ya ce: “Mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyassa. Ya Jehovah, ka tsauta ni.” (Irmiya 10:23, 24) Saboda haka a kowane hali fa an halicce yan-Adam su rayu ƙalƙashin sarautar Allah ne, ba nasu ba.
15. Da dokokin Allah sun zama kaya ne ga Adamu da Hawa’u?
15 Da biyayya ga dokokin Allah baya zama wani kaya ne ga iyayenmu na fari ba. Maimakon haka, da ya amfane lafiyarsu da na dukan iyalin yan-Adam. Ashe da mutane biyu na farkon sun kasance cikin iyaka na dokokin Allah, da kowa lafiya lau yake. Hakika fa, da muna rayuwa yanzu cikin aljanna na jin daɗi mai-girma kamar haɗaɗɗen, iyalin yan-Adam masu ƙauna! Da mugunta, shan wahala, da mutuwa basu wanzu ba.
[Hoto a shafi na 11]
Mahalicci ya ba yan-Adam kamiltaccen somawa
[Hoto a shafi na 12]
Ashe zaka so ka tuka mota a inda akwai na’urorin tafiya dayawa kuma babu dokokin tafiya ko kaɗan?