Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • nwt 3 Yohanna 1-13
  • 2 Yohanna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 2 Yohanna
  • Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
2 Yohanna

WASIƘAR YOHANNA TA BIYU

1 Daga tsohon* nan, zuwa ga macen da Allah ya zaɓa, da kuma ꞌyaꞌyanta waɗanda nake ƙauna sosai, kuma ba ni kaɗai ba, amma har da dukan waɗanda suka zo ga sanin gaskiya, 2 saboda gaskiyar da take cikinmu kuma za ta kasance tare da mu har abada. 3 Za mu sami alheri, da jinƙai, da salama daga Allah Uba da kuma Yesu Kristi Ɗan Uban, za su ƙaunace mu kuma su koya mana gaskiya.

4 Na yi farin ciki sosai, domin na gano cewa wasu daga cikin ꞌyaꞌyanki suna yin rayuwa cikin gaskiya, kamar yadda muka sami umurni daga wurin Uban. 5 Yanzu, macen da Allah ya zaɓa, ina roƙon ki cewa mu ƙaunaci juna. (Ba sabon doka ne nake rubuta miki ba, amma doka ce da muke da shi tun daga farko.) 6 Kuma ga abin da ƙauna take nufi, wato mu ci-gaba da yin rayuwa bisa ga dokokinsa. Wannan ne dokar kamar yadda kuka ji tun daga farko, cewa ku ci-gaba da yin rayuwa cikin ƙauna. 7 Gama mutane da yawa masu yaudara sun fito a duniya, waɗanda ba su yarda cewa Yesu Kristi ya zo a cikin jiki ba. Wannan ne mai yaudaran da kuma maƙiyin Kristi.

8 Ku mai da hankali ga kanku, don kar ku rasa sakamakon aiki da muka yi, amma don ku samu cikakken lada. 9 Duk wanda bai tsaya a kan koyarwar Kristi ba amma yana yin ƙari a kanta, ba shi da haɗin kai da Allah. Amma wanda ya ci-gaba da bin wannan koyarwar, shi ne yake da haɗin kai da Uban da kuma Ɗan. 10 Idan wani ya zo wurinku amma bai zo da wannan koyarwar ba, kada ku karɓe shi cikin gidanku, ko kuma ku gaishe shi. 11 Domin wanda ya gaishe shi yana goyon bayan mugayen abubuwan da yake yi.

12 Ko da yake ina da abubuwa da yawa da zan rubuta muku, amma ba na so in rubuta muku da takarda da kuma abin rubutu,* amma ina sa ran zuwa wurinku, kuma in yi muku magana yayin da muke ganin juna fuska da fuska, domin farin cikinku ya zama cikakke.

13 ꞌYaꞌyan ꞌyarꞌuwarki wadda aka zaɓa, suna aika miki gaisuwarsu.

Ko kuma “dattijon.”

Ko kuma “alƙalami; tawada.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba