Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Yau

Lahadi, 19 ga Afrilu

Idan kana da hikima a zuciyarka, ni ma zuciyata za ta ji daɗi.—K. Mag. 23:15.

A lokacin da Yohanna ya rubuta wasiƙar, wasu a cikin ikilisiya suna yaɗa koyarwar ƙarya, kuma suna raba kan ꞌyanꞌuwa. Duk da haka, wasu sun ci-gaba da ‘bin gaskiya.’ Sun “bi umarnan Allah.” (2 Yoh. 4, 6) Yadda suka riƙe amincinsu ya faranta ran Yohanna da kuma Jehobah. (K. Mag. 27:11) Wannan ya koya mana cewa riƙe aminci yana kawo farin ciki. (1 Yoh. 5:3) Alal misali, za mu yi farin ciki don mun san cewa muna faranta ma Jehobah rai. Jehobah yana farin ciki sosai idan ya ga mun ƙi yin abin da bai dace ba, kuma muka bi maganarsa. Malaꞌiku ma sukan yi farin ciki. (Luk. 15:10) ꞌYanꞌuwanmu ma sukan yi farin ciki idan suka ga mun riƙe amincinmu. (2 Tas. 1:4) A-kwana-a-tashi, za a halaka wannan duniyar Shaiɗan. Saꞌad da hakan ya faru, za mu yi farin ciki sosai cewa mun riƙe amincinmu ga Jehobah har ƙarshe. w24.11 12 sakin layi na 17-18

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2026

Litinin, 20 ga Afrilu

Kada ka yi wa kanka kaɗai abu mai kyau, amma ka yi wa ɗanꞌuwanka kuma.—1 Kor. 10:24.

Yaya tsawon lokaci da ya kamata ka ɗauka kana lura da halinta? Idan ka yi saurin gaya ma wata cewa kana son ta, za ta iya ɗauka cewa kai mai yin abu cikin garaje ne. (K. Mag. 29:20) Amma kuma idan ka daɗe kana lura da halinta, za ta iya ɗauka cewa ba ka san abin da kake so ba musamman idan ta riga ta ɗago cewa kana son ta. (M. Wa. 11:4) Ka tuna cewa ba sai ka tabbatar wa kanka cewa za ka aure ta ne za ka gaya mata yadda kake ji ba. Amma ka tabbata cewa ka yi shirin yin aure kuma cewa za ku iya dacewa da juna. Me za ka yi idan ka lura cewa wata tana ƙaunar ka? Idan ba ka da niyyar neman ta, ka yi abubuwa da za su sa ta gane hakan. Ba zai dace ka yi kamar kana so ku yi soyayya da ita, alhali kuma ba niyyarka ke nan ba.—Afis. 4:25. w24.05 22-23 sakin layi na 9-10

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2026

Talata, 21 ga Afrilu

Zan dawo in kai ku wurina.—Yoh. 14:3.

Sai shafaffu na gaske kuma masu amince ne Yesu zai marabce su a Mulkin sama. Lokacin da Yesu zai zo ya tattara “waɗanda aka zaɓa,” ba zai ɗauki duk wani shafaffe da bai zauna da shiri ba. (Mat. 24:31) Ya kamata duka bayin Allah su ɗauki gargaɗin Yesu da muhimmanci, wato su zauna da shiri kuma su riƙe aminci. Ko da suna sa ran yin rayuwa a sama ne ko a duniya. Muna da tabbaci cewa duk abin da Jehobah ya yi daidai ne. Don haka, ko da Jehobah ya zaɓi wasu Kiristoci su zama shafaffu a zamaninmu, ba za mu damu ba. Mun san abin da Yesu ya faɗa game da maꞌaikatan da aka kira su su yi aiki a gonar inabi wajen ƙarfe biyar na yamma. (Mat. 20:​1-16) Akwai wasu da suka soma aiki a gonar tun da safe, wasu kuma da rana, amma abin da aka biya su ɗaya ne da waɗanda suka zo da yamma. Don haka, ko da wane lokaci ne aka zaɓi mutum ya zama shafaffe, idan ya kasance da aminci har ƙarshe, zai sami ladan shiga Mulkin sama. w24.09 24 sakin layi na 15-17

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2026
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba