Ku Sasanta Matsalar Nan da Nan!
SHIN wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta taɓa yi maka wani abin da ya ɓata maka rai har hakan ya sa kun daina zama abokai? Don ku sasanta kuma ku ci-gaba da zama abokai, kuna bukatar ku ɗau mataki nan da nan kuma ku yi hakan da dalilin da ya dace.a
Ga wani misali, ƙashin da ya karye yana bukatar jinya mai kyau don ya warke. Amma, idan ba a yi jinyar nan da nan ba, wanda ya karye ƙashin zai ci-gaba da jin zafi, fiye da hakan ma, ƙashin zai iya gaucewa kuma ba zai taɓa miƙewa kamar yadda yake a dā ba.
Kamar ƙashin da ya karye, kada mu ɓata lokaci wajen sasanta matsalar da ke tsakaninmu da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Idan ba mu sasanta nan da nan ba, abin zai iya ci-gaba da damunmu, mu riƙe mutumin a zuciya kuma a ƙarshe mu daina zama abokai. Yesu ya ce: “Ka yi sauri ka sasanta.” (Mat. 5:25) Don haka, ka sami abokinka kuma ka gaya masa yadda batun yake damun ka, amma kada ka yi hakan da fushi. Yin hakan bai da sauƙi. Me ya sa? Ga dalilai guda biyu.
Da farko, za ka iya ƙyale batun ba tare da kun sasanta ba, domin ba ka so ka yi magana game da abin da ya faru.b Alal misali, mata Kristoci guda biyu masu suna Yudiya da Sintiki sun sami matsala da juna, amma sun kasa sasanta matsalar. Mai yiwuwa ya ɗau lokaci ba su sasanta matsalar ba, har manzo Bulus da ke can nesa a Roma ya ji game da labarin. Ya gaya musu cewa su yi iya ƙoƙarinsu don su magance matsalar, kuma su sake zama abokai. (Filib. 4:2) Idan suka nuna sauƙin kai, suka tattauna da juna kuma suka gafarta wa juna, hakan zai sa su sake zama abokai.
Na biyu, mai yiwuwa ka sa rai cewa mutumin ne ya kamata ya zo ya same ka, kuma ya yarda cewa laifinsa ne. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne ku sake zama abokai, maimakon sanin wanda yake da laifi. Likitar da yake jinyar ƙashin da ya karye zai fi mai da hankali wajen sa ƙashin ya warke, maimakon ya yi ta bincika dalilan da suka sa ƙashin ya karye. Idan kuna tattaunawa, kada ka mai da hankali a kan sanin wanda yake da laifi. A maimakon haka, ka mai da hankali ga muhimmancin abokantakarku da kuma abin da za ku yi don ku sasanta.
Me zai hana ka ka je wurin wanda kuke da matsala yau don ku sasanta kuma ku sake zama abokai? “Kada ma fushinku ya daɗe ya kai har rana ta faɗi.” (Afis. 4:26) Ta wurin ɗaukan mataki nan da nan don ku sasanta, za ka taimaka wajen kāre ‘salamar da ta ɗaure mu tare.’—Afis. 4:1-3.
a Idan Kristoci sun ɗan sami matsala a tsakaninsu, zai dace su sasanta matsalar tsakaninsu kawai kuma su gafarta wa juna. (Mat. 5:23, 24) Idan matsalar babba ce, ꞌyanꞌuwan za su iya bukaci taimakon dattawa. (Mat. 18:17) Amma kafin su yi hakan, su bi abin da ke Matiyu 18:15-16 tukuna.
b Idan wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta yi mana laifin da bai ɓata mana rai sosai ba, zai dace mu haƙura kuma mu ci-gaba da abokantakarmu.—K. Mag. 26:20.