Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 3/1 pp. 8-13
  • “Alkawarin Aljanna a Duniya Ya Canja Rayuwata”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Alkawarin Aljanna a Duniya Ya Canja Rayuwata”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Na Soma ‘Tuna Mahaliccina’ Shekaru Casa’in Da Suka Shige
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Dā Ni Mugu Ne da Kuma Mai Son Yin Fada
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 3/1 pp. 8-13

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR

Mutane Alkawarin Aljanna a Duniya Ya Canja Rayuwata!

Ivars Vigulis ne ya ba da labarin

  • SHEKARAR HAIHUWA: 1974

  • ƘASAR HAIHUWA: LATVIA

  • TARIHI: YA YI GASAR TUƘIN BABUR DA YA ƘUNSHI ƊAUKAN KASADA

RAYUWATA A DĀ:

An haife ni a Riga, babban birnin ƙasar Latvia. Mahaifiyarmu ce ta yi renon ni da yayata. Duk da cewa mahaifiyarmu ’yar Katolika ce, muna zuwa coci a ranar da ake bukukuwan addini a cocinmu ne kawai. Tun ina yaro, na gaskata cewa akwai wani mai iko sosai da ya wanzu, amma wasu abubuwa dabam da nake sha’awa sun sha kaina.

Sa’ad da nake girma, mahaifiyata ta lura cewa na gwanance wajen wargaje abubuwa da kuma harhaɗa su. Saboda haka, ba ta son bari na a gida ni kaɗai domin ta san cewa akwai abubuwa da yawa masu sauƙin wargajewa. Domin wannan, ta ba ni wani akwati mai ɗauke da abubuwan da zan iya harhaɗa motocin wasa da su da dai makamantansu. Nakan harhaɗa su sa’an nan in wargaje su kuma. Ƙari ga wannan, na yi sha’awar tsere da babur. Mahaifiyata ta sa ni a gasar babura da ake kira The Golden Moped. Na soma gasar da ƙananan babura da ba sa guduwa sosai, amma daga baya na soma yi da manyan babura.

Ina kama abubuwa da wuri idan aka yi mini koyo, saboda haka ba da daɗewa ba, na zama gwani a wannan wasa mai kasada. Na ci wasan zakaru masu tsere da babura a Latvia sau uku, kuma sau biyu na ci gasar Baltic States Superbike Championship.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

A lokacin da na shahara sosai a wannan wasan, budurwata mai suna Evija (wadda daga baya na aure ta) ta sami littattafan Shaidun Jehobah da ke ɗauke da fom a wani shafi, wanda mutum yana iya cikawa idan yana so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ta cika fom ɗin kuma ta aika. Ba da daɗewa ba, Shaidun Jehobah guda biyu sun ziyarce ta kuma suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Hakan bai ɓata mini rai ba, amma a lokacin, ban damu da addini ba.

Wata rana da Shaidun suka zo yin nazari da matata, sun gaya mini in zauna don in saurara. Na yarda kuma na ji daɗin bayaninsu. Abin da ya fi ratsa zuciyata shi ne alkawarin Allah da ke cikin Littafi Mai Tsarki cewa duniya za ta zama aljanna. Alal misali, sun nuna mini littafin Zabura 37:10, 11, inda ya ce: “In an jima kaɗan, sa’an nan mai mugunta ba shi: Hakika, da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba. Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan [duniya, New World Translation]; Za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” Na ji daɗin wannan alkawarin sosai.

Na ci gaba da yin sha’awar koyarwar Allah. Na fahimci cewa addinai da yawa suna koyar da ƙarya. Akasin haka, koyarwar Littafi Mai Tsarki sun burge ni domin a fili suke kuma ba su da wuyar fahimta.

Yayin da na ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki, na fahimci cewa Jehobah yana ɗaukan rai da muhimmanci sosai. (Zabura 36:9) Hakan ya sa ban so in ci gaba da tseren kuma ba, domin ba na so in yi kasada da raina. Maimakon haka, na so in yi amfani da rayuwata wajen ɗaukaka Jehobah. Hakan ya sa na daina sha’awar suna da kuma ɗaukaka da ke tattare da gasar babura.

Na fahimci cewa Mahaliccinmu ya damu da yadda nake rayuwa

A shekara ta 1996, na halarci taron Shaidun Jehobah na ƙasashen duniya da aka yi a Tallinn, wato babban birnin Estoniya. Wurin taron bai yi nisa da filin wasan motoci da na saba gasa a dā ba. A wurin taron, na ga yadda mutane daga ƙasashe da yawa suke zaman lafiya da juna kuma suke yin abubuwa cikin haɗin kai. Alal misali, sa’ad da wata Mashaidiya ta ɓatar da ƙaramar jakarta, na ɗauka cewa ba za ta sake ganin jakar ba. Amma ba da daɗewa ba bayan hakan, wata Mashaidiya ta ga jakar kuma ta mayar mata, ko kobo bai ɓace a ciki ba. Hakan ya ba ni mamaki sosai kuma na fahimci cewa Shaidun suna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da zuciya ɗaya. Ni da Evija mun sami ci gaba a nazarinmu, kuma a shekara ta 1997 muka yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah.

YADDA NA AMFANA:

Wasu abokaina sun rasa rayukansu domin yawan gudu a kan babura da kuma irin rayuwa ta ko-in-kula da suka yi. Nazarin Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in fahimci cewa Jehobah Mahaliccinmu ya damu da yadda nake rayuwa. Wataƙila sanin hakan ne ya ceci raina.

Ni da matata Evija mun yi shekaru huɗu muna hidima ta cikakken lokaci a ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke Riga. Yanzu muna rainon ’yarmu Alise kuma muna taimaka mata ta ƙaunaci Jehobah. Ƙari ga haka, nakan je ofishin fassara sau ɗaya a mako don in taimaka wajen gyara motoci da dai wasu abubuwa da suka lalace, kuma hakan gata ne a gare ni. Ina farin cikin yin amfani da abin da na koya sa’ad da nake yaro. Hakika, har ila ina wargaje abubuwa da kuma harhaɗa su.

Abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa ni da iyalina mu yi wa mutane wa’azi game da Jehobah, Allah na gaskiya. Hakan babban gata ne a gare ni. Tabbas, alkawarin aljanna a duniya ya canja rayuwata!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba