Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 6/15 pp. 29-31
  • Dattawa, Ku Ƙarfafa Masu Baƙin Ciki!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dattawa, Ku Ƙarfafa Masu Baƙin Ciki!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI TUNANIN YANAYIN ’YAN’UWANKA
  • KA SA ’YAN’UWANKA SU SAKI JIKI
  • KA ƘARFAFA SU DA KALMAR ALLAH
  • KA CI GABA DA TAIMAKA MUSU
  • Dattawa Kirista—​Suna Aiki Don Mu Yi ‘Farin Ciki’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Gargadin da Kake Bayarwa Yana Karfafa Mutane?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ka Koma don Ka “Karfafa ’Yan’uwanka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Mu Riƙa Kula da Kuma Ƙarfafa Juna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 6/15 pp. 29-31

Dattawa, Ku Ƙarfafa Masu Baƙin Ciki!

Angela,a wata ’yar’uwa ce da ba ta yi aure ba kuma ’yar shekara talatin da wani abu ce. Dattawa suna son su kai ziyara gidanta, kuma tana ɗan fargaba. Tana tunani, ‘Mene ne dattawan nan suke son su gaya mini? Na san cewa akwai wasu ranaku da ban je taro ba, amma na gaji ne bayan na taso daga wajen aikin da nake yi na kula da tsofaffi.’ Ban da waɗannan matsalolin, ta kuma damu da lafiyar mahaifiyarta.

Da a ce kai ne kake son ka ziyarce Angela, da mene ne za ka ce don ka ƙarfafa ta? (Irm. 31:25) Waɗanne shirye-shirye ne ya kamata ka fara yi kafin ka yi ziyara mai ƙarfafawa sosai?

KA YI TUNANIN YANAYIN ’YAN’UWANKA

Akwai wasu lokatai da dukanmu muke gajiya don ayyukanmu ko kuma hakokkinmu a cikin ikilisiya. Alal misali, annabi Daniyel ya “suma” sa’ad da aka sauƙar masa da wahayin da bai fahimta ba. (Dan. 8:27) Amma, Allah ya aiko da mala’ika Jibrailu ya yi wa Daniyel bayani kuma ya gaya masa cewa Jehobah ya amsa addu’o’insa. Mala’ikan ya ce shi “ƙaunatace ne ƙwarai” a gaban Jehobah. (Dan. 9:21-23) Daga baya, wani mala’ika ya kuma bayyana ga Daniyel kuma ya ƙarfafa shi.—Dan. 10:19.

Hakazalika, kafin ka ziyarci wani da ke baƙin ciki ko sanyin gwiwa, ka yi la’akari sosai da yanayinsa. Ka tambayi kanka, ‘Waɗanne matsaloli ne yake fuskanta? Ta yaya waɗannan matsalolin za su iya sa shi sanyin gwiwa? Waɗanne halaye masu kyau ne yake da su?’ Wani ɗan’uwa mai suna Richard wanda dattijo ne fiye da shekara ashirin ya ce, ya fi mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwa kafin ya ziyarce su. Yana kuma yin la’akari sosai da yanayinsu. Hakan yana sa ya ƙarfafa su yadda ya kamata. Idan kai da wani dattijo kuna son ku ziyarci wani ɗan’uwa, zai yi kyau ku tattauna yanayinsa kafin ku ziyarce shi.

KA SA ’YAN’UWANKA SU SAKI JIKI

Ba shi da sauƙi mutum ya gaya wa dattijo yadda yake ji. Amma, ta yaya za ka iya taimaka wa ɗan’uwanka ya saki jiki? Zai dace ka yi murmushi kuma ka furta kalmomi masu daɗi sosai sa’ad da ka fara tattaunawa da shi. Ga abin da Michael, wanda dattijo ne fiye da shekara arba’in yake fara cewa sa’ad da ya kai ziyara: “Ka san cewa wani gata mafi kyau na dattawa shi ne su ziyarci ’yan’uwa a gidajensu kuma su san su sosai. Kuma na daɗe ina ɗokin ziyartar ka.”

Za ku iya yin addu’a tare kafin ku soma tattaunawa. Za ka iya ambata halaye masu kyau na ɗan’uwan, kamar imani da ƙauna da kuma jimiri. Abin da manzo Bulus yake yi ke nan sa’ad da yake addu’a a madadin ’yan’uwansa. (1 Tas. 1:2, 3) Yin hakan zai kwantar da hankalin ɗan’uwan kuma zai sa ziyarar ta yi daɗi. A sakamako, kalmominka za su ƙarfafa shi. Wani dattijo da ya manyanta sosai mai suna Ray ya ce muna yawan mancewa da ayyuka masu kyau da muke yi a hidimar Allah, amma idan wani ya tuna mana su, hakan yana wartsake mu.

KA ƘARFAFA SU DA KALMAR ALLAH

Hanya ɗaya da za ka iya ƙarfafa ɗan’uwanka ita ce ta wajen yin amfani da Littafi Mai Tsarki, ko da aya guda tak ka karanta. (Rom. 1:11) Alal misali, wani ɗan’uwa da ke sanyin gwiwa zai iya ji shi sakarai ne. Me za ka iya yi don ka ƙarfafa shi? Za ka iya karanta masa labarin wani marubucin zabura wanda ya ji ya zama “goran ruwa cikin hayaƙi” wanda ya yamutse. Amma duk da haka, ya ce: “Ba na manta da dokokinka ba.” (Zab. 119:83, 176) Bayan ka ɗan bayyana masa nassin, za ka iya gaya masa ka san cewa shi ma bai “manta” da dokokin Allah ba.

Hakazalika, za ka iya yin amfani da kwatancin macen da ta ɓatar da azurfarta don taimaka wa ’yar’uwar da ta soma bijirewa daga ikilisiya ko ta soma sanyi-sanyi. (Luk 15:8-10) Wataƙila azurfar tana cikin sarka mai ɗauke da tsabar azurfa da yawa. Yayin da kake tattauna wannan kwatancin da ’yar’uwar, za ka iya taimaka mata ta san cewa ita ma tana da daraja a cikin ikilisiyar Kirista. Za ka kuma iya taimaka mata ta san cewa ita ’yar tunkiya ce a wajen Jehobah, kuma yana kula da ita sosai.

’Yan’uwanmu suna yawan son tattauna nassin da suka taɓa karantawa. Saboda haka, kada ka mamaye tattaunawar. Bayan kun karance wata aya tare, za ka iya sa ya yi kalami a kan wani furuci a cikin ayar. Alal misali, bayan ka karanta 2 Korintiyawa 4:16 za ka iya ce, “Za ka iya ambata hanyoyin da Jehobah ya ‘sabonta’ ka, ko kuma ya ba ka ƙarfi?” Irin wannan tambayar za ta iya sa tattaunawarku ta kasance mai ƙarfafawa sosai.—Rom. 1:12.

Za ka kuma iya ƙarfafa ’yan’uwanka ta wajen tattauna labarin wani a cikin Littafi Mai Tsarki wanda ya fuskanci irin yanayinsu. Labarin Hannatu ko Abafroditus zai iya taimaka wa ɗan’uwan da ke baƙin ciki, kuma zai sa ya san cewa yana da tamani a wajen Allah. (1 Sam. 1:9-11, 20; Filib. 2:25-30) Akwai misalai masu ɗimbin yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da za ka iya tattaunawa.

KA CI GABA DA TAIMAKA MUSU

Bayan ka ziyarce su, ka ci gaba da nuna musu cewa ka damu da su. (A. M. 15:36) Alal misali, bayan ziyarar, za ka iya yin shiri don ku fita wa’azi tare. Sa’ad da wani dattijo wanda ya manyanta mai suna Bernard ya haɗu da wani ɗan’uwa ko ’yar’uwar da ya ziyarta, yana tambaya cikin basira, “Shin shawarar ta taimaka kuwa?” Ta yin hakan, za ka iya sani ko yana bukatar ƙarin taimako ko a’a.

Yana da muhimmanci sosai yanzu ’yan’uwa su san cewa kana kula da su, ka fahimce su, kuma kana ƙaunar su. (1 Tas. 5:11) Saboda haka, kafin ka ziyarci ’yan’uwanka, ka yi la’akari da yanayinsu. Ka yi addu’a game da batun. Ka nemi nasossin da za ka karanta. Idan ka yi hakan, za ka samu kalmomi masu daɗi da za ka ƙarfafa masu baƙin ciki da su.

a An canja sunayen.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba